← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau satinsu biyu da zuwa kuma ahalin yanzu tana jin jikinta normal babu wani ciwo,toilet ta shiga tayi wanka da sabulu mai kamshi ta fito, bayan tagama kwalliya ne tana tsaka da fesa turare jawad ya shigo, ta bayanta yaje ya rungumeta,ya fara shafata,
"Jawad ya haka?" Ta fada a sabule,
"Queen gwaji zanyi, so nake naga ko kin samu lfy" kokarin kwacewa ta fara amma ta kasa, cak ya dauketa bai direta ako ina ba sai akan gadonsu.

Ranar dai pherty tasha wuya a hannun jawad saboda ji tayi kamar wannan ne karon farko harma yaso yafi karon farkon, shi kuwa jawad kasa banbance waccan ranar da wannan yayi domin queen dinsa dai ta juye ta zama cikakkiyar budurwa tun anan ya gane shi dinne dai yanzun ma dama kuma baya zargin gwanar tasa.

Sai da komai ya lafa sannan ya shiga rarrashinta yana yi mata wasu kalamai wanda nidai ummi A'isha bana jin ko me yake fada, ajikinsa ya dorata ya kwantar da ita nan ta fara baccin gajiya.

Sai da tayi baccinta ta more sannan ta tashi duk jikinta ciwo yake mata amma mararta lfy lau ko alamun ciwo babu, lokacin data farka jawad baya cikin dakin dan haka ta lallaba ta shiga toilet tayi wanka da zazzafan ruwa ta fito, mai kawai ta shafa tasa turare ta zira wata yar guntuwar riga iya gwiwa tayi kwanciyarta, jawad ya shigo hannunsa dauke da wata babbar leda mai kyalkyali,
"My queen kin tashi?" Tana ganinsa ta fashe da kukan shagwaba, da sauri ya karaso inda take ya dauketa ya goyata yayi falo da ita yana jijjigata tareda yi mata albishir din kayan sawar da ya siyo mata harda sarkar gold da awarwaro da zobuna, a bayansa tayi bacci sai da ya daina jin motsinta sannan yaje ya kwantar ta.

Koda ta tashi wani rikicin ta sa masa nan ya shirya itama ta shirya cikin bakar doguwar riga ta nade kanta da jan gyale suka fita yawon zaga gari, ko ina jama'a ce anata hada hadar kasuwanci kai ba zaka ce dare yayi ba, sai wurin karfe 2 nadare sannan suka koma masaukinsu.

Hakika sunyi rayuwa mai dadi acikin wannan kasa sunsha soyayya sosai sannan sun jiyar da junansu farin ciki, satinsu biyar acan suka fara shirin dawowa Nigeria.

Ummi Shatu
[5/29, 1:56 PM] Ummi A'isha🏻: [5/27, 9:32 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
81
~~~ Satinsu biyar a kasa mai tsarki sannan suka fara shirye shiryen dawowa kasar mu Nigeria bayan sun jibgo tsaraba mai tarin yawa.

Ranar talata suka baro kasar saudiya suka nufo Nigeria, kwanciya pherty tayi ajikin jawad ta rungumeshi acikin jirgi tana tuna daddadar rayuwar da suka yi ita dashi akasar saudiyya amma samun lafiyarta yafi mata komai dadi.

Karfe 4 na yamma suka sauka acikin garin gombe yaya aadil ne yaje dauko su sai faman fara'a da murmushi yake hakan yasa pherty tsarguwa gashi ko hada ido dashi ta kasa domin a halin yanzu kunyarsa take ji.

Gidansu ya kaisu ya ajiyesu sannan yayi musu sallama ya tafi, gidan tsaf tsaf an gyara musu ko ina kamar suna nan, wanka suka yi sukai salla suka ci abinci jawad ya fita ya tafi gidan Ummi ita kuma pherty ta kwanta domin hutawa.

Kwanansu biyu da dawowa suka je gidan ummi suka wuni acan da daddare suka biya ta gidan yaya aadil suka kai musu tsarabarsu kasa kasa pherty take kallon aadil da salima wadda cikinta ya dan fito yayi das ajikinta, hannunta salima ta kama zuwa cikin bedroom dinta suka zauna, ta debo mata kayayyaki na amare ta bata ita dai pherty duk kunya ta rufeta, sun dan jima sosai sannan jawad yace ta fito su tafi.

Tun a hanya yake damunta da tambayoyi wai me ta samo, kanta ta dauke taki bashi amsa,
"Queen tambayar ki fa nake, menene wannan?"
"Maganin ciwon cikine anty salima ta bani"
Juyowa yayi ya kalleta "kamar kuwa kin san nima cikina ciwo yake ,muje gida sai ki sammin nasha"
Shiru tayi bata bashi amsa ba har suka je gida, dakinta ta wuce ta zuba kayan acikin drawer din mirror dinta ta wuce bathroom tayi wanka, lokacin da ta fito ta iske jawad zaune kan dan stool din mirror da jarkar tsumin da anty salima ta bata dazu, da sauri taje ta zata kwace saboda har yasha rabi,
"Haba jawad danme zaka dauka min kasan ko meye?"
Idanuwansa ya lumshe ya budesu a hankali, "menene?

Naji da zaki kuma da kamshi"
"Kai kasani wayasa ka shamin?"
Gaban mudubin ta karasa ta karbe robar ta rufe ta ajiye ta tsaya ta fara kokarin shiryawa, hannunta ya riko,
"Ni ki bari haka ba sai kinyi kwalliya ba haka kinfi kyau natural beauty" harararsa tayi ba tare da tayi magana ba, tashi yayi ya rungumeta ta baya, ta cikin mudubi ta kalleshi idonshi yayi dan ja kamar me jin bacci,
"Yau nashiga uku,da ya muka kare ma balle yanzu kasha wani abu" kokarin kunce towel din jikinta ya fara tayi saurin dakatar dashi,
"Meye haka" malam nifa agajiye nake ka rabuda ni in huta ka gane?"
Idanuwansa a lumshe ya sake matseta ajikinsa,
"Kiyi hakuri pherty na, kinga fa nayi hakuri sosai tunda a saudiyya ma sau daya kika barni"
Abubuwan da ya fara yi matane suka hanata magana dolenta ta rabuda shi ta bada kai bori ya hau.

Washe gari suka shirya domin zuwa kumo wannan shine karon farko da pherty zataje gida tun bayan bikinta wurin wata hudu kenan, duk zumudi da doki ya cika mata rai saboda har ta kasa boyewa ko jawad sai da ya gane murnar da take ciki.

"Bafa kwana zakiyi ba" ya fada da niyyar zolayarta,
"Wlhi kwana biyu zanyi dan har kayana ma na debo"
"Ba kun koma sch ba?"
"Mun koma amma ni bazan koma ba sai upper week,yaushe rabona dasu mama ai dole ma na kwana"
Murmushi yayi ba tare da yace komai ba, suna shiga cikin garin kumo kasuwa jawad ya wuce dasu, a sabuwar plaza dinnan tasu ya tsaya wadda yanzu an budeta shaguna shake da kaya babu abinda ba a sayarwa,fita yayi ya barta cikin motar yaje ya debo kaya Wanda ita dai bata san ko na menene ba kawai dai taji an bude but ana zuba kayan, bayan an gama loda kayanne ya koma cikin motar suka nufi cikin gari.

Lokacin da suka shiga unguwar su pherty pherty ji take kamar tayi tsalle ta fada gidan ai kuwa yana tsayawa ta bude kofa tayi cikin gida, tana shiga ta fara kwallawa mamanta kira,
"Mama, mama, mama kina ina?"
Da sauri maman ta fito daga cikin daki tana cewa, "wa nake ji haka?

Yan tafiya har an iso mana?"
Tsalle pherty tayi ta dane jikin mamanta tana dariya daidai lokacin jawad ya shigo ya harareta, itama harararsa tayi ta saki mama ta wuce ciki.

Har cikin falo mama ta shigar jawad tayi masa shimfida ya zauna ita kuwa pherty ana can cikin daki sai bincike take yiwa mama,
"Mama ina abba na?" Tafada tana daga can cikin daki,
"Yafita kasuwa sai anjima zaki ganshi ya dawo" mama ta fada lokacin da take ajiyewa jawad ruwa da lemo a kusa dashi, cikin hausarsa dai wacce bata gama isarshi ba ya samu suka gaisa da mama.

Ya dan jima agidan kafin ya yiwa mama sallama ya fita,
"Sai ki fito ki rakashi ai ja'ira kawai" mama ta fada lokacin da ta shiga dakin da pherty take ciki tana bincike,
"To mama bari naje" mayafinta ta dauka tayi hanyar kofar gida ita kuma mama tana ta fadan binciken da pherty take yi.

Lokacin data fita ya samu yara sun fara debo kayan suna kokarin shigar dasu cikin gidan, tsayawa tayi tana kallonsa kamar yadda shima ya tsaya jikin motarsa ya zuba mata manyan fararen idanuwansa, sai da yaran suka gama shigar da kayan ya sallamesu suka tafi sannan ya dubeta ta wani rike kugu tana kallonsa,
"Zaki cinyeni ne ko yaya?" Ya fada da zummar tsokanarta,
"Babu mamaki" ta fada tana dubansa,Murmushi yayi ya nufota, ciki da koma ta buya a bayan kofar zauren gidan yana shiga ya ganta, binta jikin bango yayi ya matseta yasa dan yatsansa a saman idonta,
"Yau bazan iya bacci ba, yau zan kasa bacci queen"
Bata yi magana ba taji lips dinsa kan nata, ahankali ya fara tsotar bakinta har na tsawon wani lokaci,ita kanta tasan zata yi missing din shi, hannunta yaja zuwa inda motarsa take,
Kashe mata ido yayi, sunkuyar da kanta tayi saboda duk ya saukar mata da kasala, murmushi yayi yace,
"To ni kinga tafiyata yau da daddare sai ki nemi abokin bacci" motarsa ya bude ya shiga ya fara daga mata hannu ya tafi, murmushi tayi ta koma cikin gida tana tunanin hali irin na jawad komai nashi simple ne.

Tunda ta koma ta saka mama agaba sunata hira sai wurin la'asar sannan ta samu ta leka gidansu hawy cikin sa'a kuwa ta samu tana nan itama tazo weekend, kallonta hawy tayi cikeda tsokana,
"Kawata cikin naki wata nawa ne?"
"Ke zaki fada tunda ke kika san ina dashi" dariya hawy tayi "kema kin san kina dashi kawai fada min ne ba zaki yiba" hirarsu suka sha har lokacin sallar magrib tayi sannan suka rankaya suka koma gidansu pherty.

Suna zuwa pherty ta cicciro mata tsarabar da ta iyo mata ta takalmi da yar jaka sai atamfa mai dan karen kyau, har dare suna tare da hawy, sai lokacin da fita rakata ne sannan jawad ya kirata a waya, wata kunya taji saboda sam ta manta bata kirashi taji yaya ya sauka ba.
Chapter 24 · 0% Book details