← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 27

Sashe 22

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda safiya tayi makara suka yi basu tashi ba sai wurin 6 harda yan mintuna, pherty ce tafara bude idonta ta kalli jawad wanda ke kanannade da ita kamar za a kwace masa ita, bakinshi akan tsakiyar gashin kanta ya makalkaleta sosai, murmushi tayi, tayi kissing din kirjinsa sannan ta fara kokarin tashinsa, bayansa ta shafo ta kirashi a hankali,
"Jawad, jawad tashi"
Ahankali ya bude idonsa ya sauke su akan kyakkyawar fuskarta wadda kamar ba daga bacci ta tashi ba, murmushi ya sakar mata ta mayar masa da martani, tashi yayi ba tare da yayi magana ba, ya shiga toilet kafin ya fito har ta gudu dakinta, bayan ta idar da salla ta sake kwanciya har sai wurin 9 sannan ta tashi tayi wanka taci gayunta cikin bakar t shirt da jan wando, kitchen ta shiga lokacin har masu aiki sun gama kimtsa ko ina, dankali ta dauka ta fara ferewa tareda kunna karatun alqur'ani kira'ar sudais acikin wayarta tana aikinta tana bin karatun, shigowar jawad cikin kitchen dinne ya sata kashe karatun ta jiyo ta kalleshi da alama ya warke domin yayi kyau sosai ya sha riga ja da blue din wando sai kamshin turare mai dadi yake gashi ya gyara sajensa da sumarsa sun kara fito da kyawunsa.

"Morning my queen, Xarah, my wife, my luvly one and only" ya fada yana murmushi,
"Morning" ta fada ta cigaba da aikinta,gas ta kunna ta dora mai ta zuba dankalin, lekawa jawad yaje yayi tsall mai ya fantsalo masa a hannu cikin sauri ya matsa yana yarfe hannunsa, matsowa tayi kusa dashi "mu gani, ka kone?"
"Na kone mana, queen kalli kigani" hannun nashi ta kamo tana dubawa shi kuma yana duban rigarta wadda ta dameta kamar zata yage, kirjinta ya shafa da sauri ta matsa,
"Koma falo ka jirani"
"Queen tayaki fa zanyi kike korata"
"Nidai nace ka koma falo" juyawa yayi ya fita ya koma falon ya zauna yana jiranta, murmushi tayi taci gaba da aikinta har ta kammala ta harhado ta kawo falo ta shiryasu akan table.

Bayan sun kammala break dinne yace ta shirya su tafi gidan yaya aadil, tashi tayi taje ta shiryo cikin wani leshi maroon ta yafo bakin mayafi da bakin takalmi ta dauki bakar jaka, tana tunanin ta yadda zata iya hada ido da yaya aadil yau,Allah sarki gashi duk kayan da take sawa kayan lefen da ya hada mata ne ashe da rabon ba shine zai ga kwalliyar ba.

A mota ta samu jawad suka tafi, yana ta yi mata hira a hanya har suka isa gidan aadil kamar wata marar gaskiya haka ta zama, jawad yana gaba tana biye dashi a baya, a babban falo suka tarar dasu Salima na zaune kusa dashi suna karanta magazine,yayi kyau yayi kiba abinsa gashi ya sake haske, caraf suka hada ido lokacin da ya dago domin amsa sallamar su, saurin sunkuyar da kanta tayi har suka karasa cikin falon kanta yana kasa, a kasan kujera ta zauna shikuma jawad ya hau kujera ya zauna,sannu da zuwa anty Salima ta fara yi musu wacce kallo daya zaka yi mata ka fahimci tana dauke da juna biyu domin alamu duk sun gama bayyana, a kunyace ta gaishe su amma bata bari sun hada ido da yaya aadil ba, sam ta kasa sakewa wata irin kunya taji tana ji.

Basu fi minti 20 ba jawad yace ta tashi su tafi dan ya fahimci ta kasa sakewa nan suka yi musu sallama suka tafi gidan Ummi, nanma taga karamci domin ummi ta karbeta hannu bibbiyu anan ne suka dade dan har jawad ficewa yayi ya barta sai la'asar lis sannan ya dawo ya dauketa suka koma gida.

Suna shiga falo ta fada jikin jawad,
"Nagaji yimin tausa, amma bari na cire kayan nan nasha iska" riga da skirt din ta cire ta zauna daga ita sai underwear da bra, jikinta ya fara mammatsa mata tana lumshe idanu can taji ya canja salo dan haka tayi saurin rike hannunsa,
"Pls queen" ya fada idonsa a lumshe, zuruf ta tashi ta kwasa a guje tayi dakinta binta yayi tana kokarin rufo kofar ya hanata ya shiga, bathroom ta sake kwasa zata shige yayi saurin damkota ya dorata kan bed anan aka fara dambatawa har dai ta fahimci yau jawad da gaske yake dan haka ta kyaleshi ya shiga nuna mata zallar soyayya amma kuma acan kasan ranta tunani take ko zata iya bashi abinda yake so?

Tunanin ta ne ya tsaya daidai lokacin da taji mararta ta yi wani irin murdawa, nan ta fara jin ciwo kamar zata mutu, kankame jawad tayi ta rirrikeshi tana numfarfashi,
"Wayyo zan mutu, wayyo Allah, jawad marata, wayyo marata" haka ta yi ta fada a gigice,
Da sauri ya katse abinda yake yi ya tallafota ya rungumeta
"Xarah menene?" Ya fada a rude,
"Marata jawad" ta fada tana cije lebenta, wata kara tasa sakamakon wani irin azababben ciwo da taji sai kuma ta fara bleeding jini guda guda ya fara fita daga jikinta, cikin tsoro gamida rudu jawad ya sake rungumeta,
"Pherty wannan jinin fa?

Jinin meye wannan?" Bata iya bashi amsa ba sai hawaye data fara zubarwa, nan jawad ya sake rudewa yama rasa me zaiyi saboda har yanzu jinin ne yake fita bai daina ba, kwantarta yayi ya saka kayansa, yaje falo ya dauki wayarsa ya kira dr ansar, da sauri ya dawo wurinta ya dauko kayanta ya fara saka mata, ita kuwa pherty in banda kuka babu abinda take amma ba kukan ciwo take ba kukan kaddarar da take tare da ita take saboda tasan dole jawad ya sake aure nan gaba tunda ita ba zata iya biya mishi bukatarsa ba,yama za ace zai iya zama da ita a haka?

Sai dai kawai ya kalleta amma babu wani abu da zai samu daga gareta.

Nan hankalin jawad ya sake tashi kololuwa, mintuna kadan sai ga dr ya iso nan jawad ya shiga yi masa bayanin abinda ya faru,
"To shi wannan jinin na mensuration ne ko me?" Dr ansar ya fada cikeda al'ajabi,
"No ba period bane dama ta taba samun problem ne ta bugu a mararta" jawad ya fada kamar me shirin yin kuka, nan dr ya fara kokarin bata taimakon gaggawa, bayan ya rurrubuta mata magunguna ya bawa jawad shawarar lallai suje asibiti suga likitan mata domin shi ba likitan mata bane, ita dai pherty tana kwance tana jinsu.

Bayan dr ya tafi ne jawad ya tashi da niyyar zuwa ya siyo mata magungunan, hannunsa ta riko,
"Ina zakaje?

Ka zauna kar katafi" kai ya gyada mata,
"To bari na bawa mai gadi ya siyo miki maganin" hannunsa ta saki yaje ya dawo ya kwanta akusa da ita ya rungumeta shi kansa tunani yake wannan wacce irin kaddara ce?

Ga mace har mace amma ace ba zata iya rayuwar aure ba, hakika wannan wata jarrabawa ce acikin rayuwar aurensu shida pherty.

Jin ana kwankwasa kofar falon ya sashi sakinta yaje ya bude maigadin ne ya kawo maganin da aka aike shi ya siyo, karbowa yayi ya dawo ciki ya dauko mata ruwa ya tayar da ita zaune ya bata tasha maganin ya sake kwantar da ita, gumi ta fara hadawa duk da sanyin ac din dake ratsa dakin, babu shiri ya cire mata kayan dake jikinta ya barta haka, babu bata lokaci ta fara aikin bacci.

Ummi Shatu🏻
[5/23, 7:57 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
79-80
~~~Ta jima tana baccin wahala kafin ta iya bude idonta lokacin har gefen marar tata ya kumbura kadan, juyi tayi ta kalli jawad wanda ke kwance a gefenta fuskarsa cikeda tausayinta gami da alhinin halin da suka tsinci kansu.

"Sannu queen, ya jikin naki" ya tambayeta cikin rada
"Da sauki, hada min ruwan zafi zanyi wanka" ta fada tana kwalla, girgiza mata kai yayi,
"Don't cry my queen,karki sawa kanki damuwa pls insha Allahu zaki samu lafiya"
Hawayen fuskarta ta goge ta fara kokarin tashi zaune, jawad dinne ya taimaka mata ta zauna ya jawo mata towel ta daura ya shiga toilet ya hada mata ruwan zafi ya fito, dakyar ta iya tashi ta shiga toilet din saboda zugin ciwon da gefen marar ta yake yi mata.

Acikin toilet dinma ta dade tana kuka kafin tayi wankan, jin shiru shiru bata fito ba yasa jawad binta cikin toilet din nan ya sameta zaune sai faman kuka take, agabanta ya durkusa ya kamo hannuwanta ya rike ya fara yi mata magana a hankali,
"My dear menene abin kuka?

Kowacce cuta tana da maganinta kar ki sawa ranki damuwa har wani ciwon ya kama min ke kinji?

Oya tashi nayi miki wankan" mikar da ita yayi, shine yayi mata wankan yana yi yana yimata wasu yan wasanni da haka har yayi nasarar mantar da ita bacin ran da take ciki.
Chapter 22 · 0% Book details