← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da misalin karfe 3 yaje wurin pherty bayan sunsha hirane yake sanar mata da batun bikinsu nan taji jikinta yayi sanyi amma ta nuna masa farin cikinta a fili, koda ya tafi ta shiga hostel nan ta fadawa su Sadiya da A'isha sai kuma ta fara kuka, nan suka shiga tsokanarta wai kukan farin ciki take.
***
Jawad yana zaune a falo daga shi sai three quarter da yar body hug yana tv game ajikin computer kamar wani yaro, Ummi tana zaune tana waya kamar daga sama ya jiyo ta tana cewa "bikin Aadil ne ya taso nan da 4 months zai auri wata yarinya phertyma shine nake son ki hado min kayan lefe....!"
Zunbur ya mike kamar an tsikareshi, da sauri ya wuce side dinshi ya dauko key din motarsa ya nufi gidan yayan nasa Aadil, lokacin da ya shiga gidan iya Aadil ne zaune a falo yana kallo yayinda Salima take kitchen tana aiki,
A can ciki yayi sallama,shi dinma Aadil din a dakile ya amsa domin ba don ta zama wajibi ba ma to da bazai amsa ba,
Kallonsa jawad yayi idonsa kamar gauta dan ja, "nazo ne nayi maka kashedi, pherty ba taka bace tawace, ta sanadiyyata ka ganta har ka kamu da sonta saboda tsabar abin kunya"
Kallonsa Aadil yayi "Kai wanne irin shasha ne?

Kana tsammanin pherty zata aureka ne?

To idan mafarki kake gara ka farka, bayan ka gama rusa mata MARTABAR TA shine yanzu zaka dawo kace wai kana sonta?

To babu abinda pherty zata yi dakai gara ma ka daina batawa kanka lokaci"
"Ba batawa kaina lokaci nake ba kuma kai kanka zaka tabbatar da haka domin indai ina rayuwa to nine mijin pherty, kuma nine zan dawo mata da MARTABAR TA"
"Ahakan?

You are very stupid, idiot"
Har ya juya zai tafi ya sake dawowa, "kar ka kuskura ka sake zagina dan zan iya daukar mataki"
"An zageka din, idiot ko zaka rama ne?"
Idonsa jawur ya kalleshi "kai kanka kasan a doke ba iya duka na zakayi ba dan ko fafatawa muka yi ba zakayi nasara ba akaina so be very careful" ya nunashi da yatsa sannan ya juya ya fice daga falon yabar Aadil a tsaye.

Ummi A'isha🏻
[5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [4/28, 8:49 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
26-30
~~~ Jawad yana fita Aadil ya dunkule hannunsa ya naushi iska "oh!

My God", ya fada da karfi tareda fadawa kan kujera dabas ya zauna daidai lokacin Salima ta fito daga cikin kitchen ta zauna kusa dashi,
"Sahibi meke faruwa ne?"
Cikin kunar rai yace
"Babu komai"
"Da kuma sai naji kamar muryar jawad"
Shiru yayi bai bata amsa ba sakamakon tafarfasar da zuciyarsa keyi, aransa fadi yake "yaron nan jawad na fuskanci ya gama rainani amma zanyi maganinsa dan ni ba sa'ansa bane, a haifi yaron akan idona amma yazo yana kawo min raini?"
Dafashi Salima tayi tareda fara rarrashinsa tamkar karamin yaro duk kuwa da cewar bata da masaniyar abunda ya faru amma dai taga ransa a bace don haka ta fara kokarin mantar dashi bacin ran dake tare dashi.
******
Lokacin da jawad yabar gidan Aadil gudu kawai yake shekawa ya nufi sch din su Xarah wato state university gombe, yana zuwa babu jira ya shiga cikin makarantar a gaban auditorium yayi parking yana daga cikin motarsa a zaune, wani irin zugi yaji zuciyarsa nayi masa tabbas ko shakka babu yasan yana daf da kamuwa da ciwon zuciya.

Yana nan zaune cikin motar tasa kamar daga sama ya hangosu itada Sadiya sun fito karatu, da sauri ya bude motar ya fita ya nufesu, sai da gaban pherty yayi mummunar faduwa lokacin data ganshi, cikin dashewar murya yace da ita
"Zo ina son magana dake"
Yana gama fadin haka ya juya ya yi gaba, kamar wacce take tsoronsa ta kalli Sadiya tace "ina zuwa, bari nadawo"
Binsa tayi har wurin motarsa ta tsaya ta waje tana kallonsa cikeda alamun tsoro karara akan fuskarta,
"Gani" ta fada tana kallon wani wuri,
"Pherty"
Yakira sunanta cikin damuwa,
"Kina son ki hadani da dan uwana ko?

Kina son hada yaki acikin familynmu ko?

Aadil is my brother and i love him more than how you are think, so kar ki jawo abun da zaisa na tsani dan uwana, kar kisa nafara gaba dashi, tabbas idan kika auri Aadil kin gama da rayuwa ta kuma babu abinda yayi saura acikin rayuwata"
Kallonsa ta danyi ta gefen ido ga mamakinta sai taga yar kwalla acan lungun idonsa,idanuwansa sun kada sunyi jajur,
"Sai dai kayi hakuri jawad amma a gaskiya ni ahalin yanzu banida miji in ba yaya Aadil ba...!"
Cikin sauri ya balle murfin motar ya fito wata damka ya kai mata "ke me kike takama dashine?

Am asking you dame kike ji?

You are not serious pherty, ke kin isa ki auri wani namijin da ba niba?

Kinyi kadan wallahi ni zaki aura"
Yana kaiwa nan ya sassauta rikon da yayi mata "pherty kar kiyiwa rayuwata haka, bai kamata ki rama abinda nayi miki ba ta hanyar auren dan uwana, haba pherty so kike ki kasheni ne?

Wallahi indai baki aureni ba mutuwa zanyi i will die if you didn't marry me, pls save my life, pls pherty,pls, pls" kansa ya kifa akan kafadarta kwalla tana kokarin zubowa daga idonsa, ita kanta phertyn hawaye ne yake kwaranya daga idonta domin tasan tana son jawad so nagaskiya to amma bazata taba iya aurensa ba, dole ta auri aadil saboda wani dalili mai karfi,
Yakai mintuna biyu ajikinta yana shakar kamshin jikinta sannan ya dago kansa yana kallonta, "idan har na mutu ko kuma na fada cikin wani hali to ki zargi kanki"
Yana kaiwa nan ya matsa daga kusa da ita ya shiga motarsa yaja ya fita yana driving yana hawaye Wanda shi kansa bai san ko na menene ba, yana isa gidansu part dinsa ya shiga ya kwanta akan tangamemen gadonsa ya fara tunani "hakika pherty nasan na cutar dake, amma ki yafe min ki bani dama domin gyara kuskurena,pls and pls pherty" haka ya fada a hankali,
Juyi kawai yake ga wani irin ciwo da yaji kansa yana yi masa gashi yayi nauyi kamar an dora masa katoton dutse akan nasa, daren wannan rana yayishi ne cikin bakin ciki da tashin hankali.

A bangaren aadil ma haka abun yake domin shima hankalinsa a tashe yake kwata kwata bashida walwala sai sakar zuci yake, dan haka koda Salima tayi bacci falo ya koma ya zauna yayi tagumi, yayinda bacci yayi kaura daga idonsa.

Wannan dare darene mai cikeda fargaba, kunci, takaici, bacin rai ga mutane guda uku wato jawad, aadil da pherty, domin itama tun lokacin da jawad ya tafi ya barta take kuka dakyar su Sadiya suka sata tayi shiru, amma idonta kyamas babu alamun bacci.

Washe gari da safe bayan aadil yayi wanka yayi breakfast ya shirya domin fita zaije yaga pherty sannan yaje gidansu, lokacin da yaje makarantar yana ganin pherty yasan akwai matsala saboda fuskarta duk ta kunkunbura alamun tayi kuka ta more amma tambayar duniya yayi mata taki fada masa gaskiya,
Kallonta yayi cikeda damuwa "pherty na ban sanki da haka ba, ada bakya boye min komai amma yau kin canza daga yanda nasanki"
Murmushi ta dan kakaro "yayana yau ma ba canjawa nayi ba, gaskiya na fada maka babu abinda ke damuna"
Kallo kawai ya bita dashi amma bai yarda da abunda ta fada ba sam,
daga karshe dole ya hakura ya tafi.

Yana zuwa gidansu yayi parking din motarsa a gurinda aka tanada ya tasamma cikin gidan yana shiga ya hango jawad akan dinning yana yin breakfast shida Ummi, kamar kazar da kwai ya fashewa aciki haka ya karasa inda suke, durkusawa yayi ya gaida Ummi sannan ya mike yana kallon jawad wanda yayi kicin kicin ya hade rai, shi dinma aadil din ta ciki na ciki yake kallon jawad cikeda jin haushi, falo ya koma ya zauna yana jiran Ummi tagama tazo, shi kam jawad sai hararar aadil yake kasa kasa gudun kar Ummi ta ganesu.
******
Tun tafiyar Aadil pherty take faman kuka kamar ranta zai fita, cikeda damuwa pherty da Sadiya suka sakata a tsakiya,
"Pherty dan Allah kiyi hakuri, shifa auren nan ba mutuwa bace" A'isha tafada tana dafa kafadarta,
"Ni nafasa ma auren, shima yaya aadil din nafasa aurensa tunda abin hakane" tafada cikin kuka,
"Kinada hankali kuwa?" Sadiya tafada cikin razani,
"Wallahi da hankalina Sadiya, da hankalina,idan na auri yaya aadil zan haifar masa da matsala tsakaninsa da dan uwansa, zan jawo rikici a tsakaninsu wanda har sai duniya tayi ala wadai dani, haka auren jawad ma bazai haifar min da kwanciyar hankali ba domin idan na aureshi banyi wa yaya aadil halacci ba sannan nazama butulu wadda take mance alkairi hakan zaisa nan gaba mutane suji tsoron yiwa wani taimako domin idan sunji labarina zasu dauka kowa mai irin halina ne"
Cikeda mamaki dukkaninsu suka kalleta
"Bamu ganeba kin bamu abu a dunkule" Aisha tafada,
"Dan Allah ki daure ki warware mana ko mafi fuskantarki" Sadiya ta fada tana kallonta,
"Tabbas nasan zamanmu daku ban taba sanar daku labarina da matsayin yaya aadil agareni ba, to amma yau ya zama dole nasanar daku labarina wanda babu komai acikinsa face, gargadi, bacin rai, tausayi, ban mamaki hadeda ban haushi, labarina cike yake da sarkakiya da abun mamaki nagaske, ina so ku nutsu ku saurareni domin jin wannan labari nawa domin ina so ya zamo izina ga yanmata da iyayenmu mata"
Nutsuwa suka yi cikin mamaki sukace "muna sauraronki, amma kafin ki fara meye alakar aadil da jawad?"
"Aadil yayan jawad ne uwa daya uba daya, zaku fahinci hakan idan kuka biyo labarina"
"Muna sauraronki" suka fada a tare.

Masu karatu kun shirya jin labarin pherty??

Nidai Ummi Shatu na shirya, dani daku mubi pherty Xarah dan jin labarinta, gaisuwa gareku masoya masu bibiyar labarin.
Chapter 5 · 0% Book details