Sashe 7
Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na tambayi kaina, lallai kam dan gashinan dan gayu dashi nafada acikin zuciyata,
"Yau idan kun yi siyayyar ku kawo na ajiye muku kunji?" Ya sake magana da turanci,
"Mun gode kuma zamu kawo" Hawy ta bashi amsa, fuuuu najata muka shige cikin kasuwa muna tafe muna fada sai faman masifa nake mata na kulashi da tayi, daga nan nace mata
"Wallahi idan dan yankan kaine babu ruwana iyakaci idan ya yanke kanki na kaiwa su mama labari"
Dariya ta fara shekawa sannan ta bani amsa
"Dadinta ma dai bani yake so ba balle har ya yanke kaina"
"Eh sai kifadi wanda yace yana so"
Muna siyayya muna fada nida ita har muka gama dama fada sabon mu ne amma da yake kowa yasan kowa shiyasa baya zama na gaske da zarar munyi fadanmu kuma zamu ci gaba da hira,
"Dan Allah hawwan mama ko ya sake tasowa karki kulashi" nafada ina rikeda hannunta
"Haba ta mama, wulakanci fa babu kyau, gayen nan wallahi sonki yake"
Ban bata amsa ba saboda ganinsa da nayi ya taho inda muke
"Kun gama ne?"
Ya tambayemu yana kallona, nikam dauke kaina nayi, yayinda Hawy ta bashi amsa da "ehh"
"Nazo na kaiku gida?"
Nanma bashi amsa tayi da "ehh"
Yana tafiya dauko motarsa na harareta amma banyi magana ba ita kuma ta mayar min martani da murmushi
Wata mota hadaddiya new end of discussion ya dauko baka mai kyau, gidan baya nabude zan shiga, hawy ta rikeni "karki bada mu mana, ki shiga gaba pls"
"Ke meya hanaki shiga gaban" nafada cikeda masifa nashigewata gidan baya, itama bayan ta shigo, muna tafiya suna hirarsu da hawy ni bana saka musu baki da haka har muka karasa unguwar mu, kasancewar ga gida ga gida tsakanin gidanmu da nasu hawwa yasa muka sauka a kofar gidansu ban tsaya jiranta ba na dauki kayan na shige gida, nan nabarta suna magana dashi.
Ta dade awaje kafin ta shigo tana dariya "yau dai kin samu matsala a kwakwalwarki ko?" Na fada ina hararta "wlhi ras nake kawai keda saurayinki ne kuke bani dariya" ta fada lokacin da take zama kusa dani
"Saurayinki dai malama" na fada ina kallonta
Zama tayi kusa dani ta fara yimin bayanin maganganun da suka yi dashi wai yana sona kuma zai zo gobe,
"Ke nifa na fada miki ba yanzu zanyi aure ba"
"Eh nasani phertyn mama to amma at least dai ace kanada wanda zaka aura a hannu ai da dadi, saboda kinga yanzu idan kika rike wannan kuna soyayya har ki gama karatunki, lokacin da kika gama sai ayi maganar biki kinga lokacin kun gama sanin halin juna basai an tsaya binciken halayen juna ba"
"Eh maganarki gaskiya ce ta mama amma nifa kin san natsani fita zance gaskiya"
"Duk wannan mai sauki ne ku zaku tsara kayanku"
"Shikenan tunda kince haka sai dai naga kamar baya jin hausa fa"
"Eh ai daidai kenan" tafada tana dariya nan muka shantake har bayan magrib sannan ta rakani gida.
******
Washe gari bayan na dawo daga sch da yamma sai ga hawy ta shigo, adaki ta sameni ina kwalliya, "ke bakonki fa har yazo"
"Dan jaraba ko dan me?" Nafada ina dariya
"Dan Allah yi sauri muje"
"Sai kiyi kuma"
Kaya natashi nasa wani material ash colour nasa farin hijab, muna fita hawy tace gani nan ta kawoni bari ta shiga gida, tana tafiya naji na takura kasancewar wannan shine karo na farko da na fito zance
"Pherty my queen" ya fada cikin daddadar muryarsa
Kallonsa nayi ta gefen ido yana sanye da bakar t shirt da bakin wando na jeans, gaskiya ya hadu ba kadan ba, hira yayi tamin duk kuwa da cewar maganar tasa a hankali yake yinta dan da alama bashida yawan surutu kuma bai da hayaniya,
Ya dan jima sannan ya tafi, yana tafiya nashiga gidansu Hawy nafara bata labarin hirar da salim yayi min domin yace min sunansa salim dariya kawai take yi har nagama bata labarin
"Bana son wulakanci fa"
"Allah ya baki hakuri" ta fada tana dariya.
Tun daga lokacin soyayya mai karfi ta kullu tsakanina da salim, yanzu yana zuwa wurina duk bayan kwana biyu sai dai wani abu da yake daure min kai dashi shine yawan son taba jikina da yake yi,
Yauma kamar yadda ya saba zuwa yazo bayan sallar magrib, hijabi nasa nafita na sameshi zaune cikin motarsa, gaban motar na shiga na zauna,
"Queen" ya fada yana kashe min ido
Dan murmushi nasaki
"King" nafada nima ina kallonsa
Hannu ya miko zai shafi fuskata amma sai na dauke kaina,
"Wai queen bakya sona ne?
Kullum idan muna hira sai ki rinka kyamata"
"Ni ban kyamaceka ba salim, lokacine dai bai yiba wanda zaka rinka taba min jiki"
"Yaushe ne lokacin?"
"Idan munyi aure"
"To ai kafin aure ma akwai taste before marriage"
Kallonsa nayi cikeda kuruciya a tare dani
"To ai ni ban saniba"
Hannunsa yasa wanda yake baibaye da gashi ya kamo nawa hannun
"Ki kwantar da hankalinki queen bazan taba cutar dake ba, aurenki zanyi"
Hannun yakai kan fuskarsa ya fara shafar fuskarsa dashi in banda shock babu abinda jikina keyi wurin kamar mintuna biyar nace mishi zan shiga gida saboda abbana ya kusa dawowa daga masallaci kuma idan yazo ya sameni anan fada zai yi.
Yana tafiya nashiga gidansu hawy na sameta, hannunta na janyo muka fito waje "hawy mutumin nan fa gaskiya dan iska ne" nafada ina kallonta
"Meya cemiki, maganar iskanci yayi miki?"
"Hawy nidai gaskiya zance ya daina zuwa saboda kullum fa sai ya rinka wani shasshafa ni yana kokarin sai ya rike hannuna ko ya taba jikina"
Kallo na tayi kafin tayi magana muka hango abbana yana tahowa ganin haka yasa kowacce shigewa gida batare da mun karasa maganar ba.
Ummi A'isha
[5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [5/3, 5:52 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
36-40
~~~ Koda nashiga gida naci abinci nayi sallah shirin kwanciya nayi amma koda na kwanta sai nafara tunani acikin raina shin me salim yake nufi dani?
Nafarko dai ni agaskiya nafara tsorata dashi saboda yadda yake shafata idan muna hira gashi kullum bashida zance sai na ni kyakkyawa ce yasan yanda nake da kyau awaje aciki ma haka nake, abunku da kuruciya sai dai nayi murmushi nace nagode, da yake yarinta na damuna tuni na watsar da zancen nayi baccina.
Da safe kamar kullum nayi shirin tafiya sch, ta gidansu Hawy na biya lokacin tana kokarin shiryawa, bayan mun gaisa da mamansu ne nafara yiwa Hawy masifa "kullum ke kike makarar damu, gaskiya sai kin taho" nafada lokacin da nake kokarin fita daga cikin dakin, "yi hakuri phertyn mama"
Juyowa nayi na kalleta "wannan sunan bazai fita daga mouth dinki ba ko?"
Murmushi tayi "ai sunanne ya shiga bakina sosai"
Dariya nayi saboda tun ina karama aka lakaba min wannan sunan yan unguwa ko kwatance za ayi da gidanmu sai dai ace gidansu phertyn mama,
Bayan ta gama shiryawa ne tafito muka dauki hanyar makaranta muna tafe muna hira,
"Yawwa phertyn mama maganar jiya tsakaninki da salim meke faruwa ne?"
"Um hawyn mama ai salim dinnan dai dan iska ne, abubuwan da yake min sun fara yawa gaskiya"
"Meya ce miki?"
"Ai ba wani abu yake cemin ba ni kawai taba min jikin da yake ne bana so"
"To idan ya sake kokarin tabaki ki hade rai ki bata fuska kice ke bakya son haka"
"Na fada masa fa amma dai zanyi hakan"
"Yawwa kiyi masa haka, kin san su irinsu sunada jarabar son taba mace gashi dai yace a mecca yayi rayuwarsa, amma baya tsoron Allah"
"Wallahi kam, Allah dai ya kyauta"
Haka muka karasa makaranta muna tafe muna hirar salim.
Yau ma da daddare salim yazo dan haka na shirya na fita, acikin motarsa yake zaune sai kamshi turare ne ke tashi yayi kyau sosai cikin farar t shirt da red din wando ya gyara sumarsa da sajensa, ahankali na shiga na zauna kaina akasa na gaida shi,
Wani mayaudarin murmushi yayi min sannan ya fara kokarin matsowa jikina da sauri na dakatar dashi raina abace "salim meye wannan?" Nafada cikin fada,
"Sorry my queen wannan ai itace soyayyar kece baki sani ba"
"Nidai ka bari gaskiya bana so" nafada kamar zanyi kuka
"Ashe bakya sona?" Yafada cikin fillanci
"Ina sonka mana" nafada ahankali
"To tunda kina sona ai dan na tabaki babu damuwa, wannan abunfa shine son"
Shiru nayi bance komai ba,hannuna ya kama na kwace,
"Nidai ka daina gaskiya"
"Allah ya baki hakuri phertyma, amma daga yau bazan sake dawowa gidanku ba tunda abun hakane"
Hankalina naji ya tashi domin gaskiya ina son salim sosai,
"Kayi hakuri, wallahi ina sonka sannan kasan babu kyau mutum ya rinka taba mace in dai ba aure suka yi ba"
Dan murmushi yayi "sai yanzu nagane abunda kike nufi, wato gani kikeyi kamar ba aurenki zanyi ba ko, tunda hakane ina komawa gida yau maganarki zan yiwa dad dina za azo a nema min aurenki a kawo komai gidanku in yaso kina gama karatu sai ayi bikinmu"
Wani dadi naji ya shigeni yanzu kam nasan da gaske salim yana kaunata,
"Yawwa kaga haka yafi" nafada cikeda jin kunya, yan yatsuna naji ya kama
"Jarababbe ai bazai hakura ba" nafada cikin zuciyata.
Sai da yagama mammatsa min yan yatsuna sannan ya tafi amma ni duk sai ban kawo komai ba araina tunda aure za muyi.
Lokacin da nashiga gida abba na yana biye dani a baya yana shiga falonsa naji yana kwalla min kira, da sauri na tafi wurinsa,
"Waye wanda naga yanzu?" Tambayar da abba ya jefo min kenan
"Abba sunansa salim" nabashi amsa
"Meye alakarki dashi?"
Shiru nayi banyi magana ba,
"To daga yau kar nasake ganinsa a kofar gidana idan ya sake zuwa ki fada masa kar nakara ganinsa, idan aurenki zaiyi ya bari idan kika gama karatu sai ya fara zuwa, idan kuma bazai iya jiranki ba to Allah ya hada kowa da rabonsa"
"Haba Malam ya za ai kace haka?