Sashe 6
Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ummi A'isha🏻
[5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [5/1, 7:32 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
31-35
~~~ Kowaccensu gyara zama tayi ta nutsu ta fara sauraron labarin pherty wacce ta fara da cewa
"phertyma maitama Umar shine cikakken sunana asalin mahaifina dan gombe ne acikin wata local government da ake kira da kumo, muna zaune acikin unguwar tudun wada, mahaifina Malam Umar sunyi aure da mahaifiyata tun auren saurayi da budurwa kuma suna zaune lfy basuda wata matsala sai ta rashin haihuwa, duk zamansu shekara da shekaru basu samu haihuwa ba amma hakan bai Sa mahaifina kara aure ba,
Mahaifiyata malama Adama yar asalin gombe ce acikin karamar hukumar funakaye,sana'ar mahaifina itace kasuwanci kuma a unguwa shine na'ibin limamin unguwarmu kasancewar mahaifina mutum ne mai addini,
Tun lokacin da aka haifeni na taso cikin gata da kulawa domin rayuwar gidanmu rayuwace ta babu yabo babu fallasa iyayena suna gudanar da rayuwarsu cikin godiyar ubangiji.
Nayi karatuna na primary har nakai ga secondary gashi babu laifi nayi karatun addini daidai gwargwado.
Tun daga makaranta har gida banida kawaye, kawata kwaya daya ce hawwa wacce muka taso tare sannan hatta makaranta tare muke zuwa.
Lokacin da nashiga aji hudu a makarantar secondary a lokacin ne samari suka fara yimin caa gashi dai ba wani girma gareni ba sai dai kyawuna wanda ya fara bayyana a lokacin domin nafara zama cikakkiyar budurwa.
A zahirin gaskiya nikaina nasan inada kyau daidai misali kuma inada kirar jiki mai daukar hankali wannan dalilinne ma yasa samarin fara bayyana min soyayyar su adai dai wannan lokaci.
Kamar kullum yau ma nadawo daga makarantar boko jikina sanye da uniform riga da wando jajaye da farin dankwali da farin hijabi, kafata sanye da takalmi sandal in banda yunwa babu abinda ke damuna domin da safe banyi kyakkyawan breakfast ba natafi kasancewar na makara,
A gaggauce nashige gida duk kuwa da cewar naga wani saurayi sai bina yake amma ban saurare shi ba domin nagama gajiya, ko sallama ban iya yiba nashige cikin gidan "phertyma ya ko sallama babu" muryar mama najiyo daga cikin kitchen
"Mama nagaji ne ga yunwa wlhi"
"To ai maganinki kenan tunda kullum bacci kikeyi bakya tashi da wuri kinga kuwa ai dole ki rinka makara"
Daki nashige naje na tube uniform dina na dauro zani kawai na fito na nufi kitchen wurin mama, Ina zuwa na tarar ta tana jifan dan wake, "sannu mama" nafada ina kokarin jawo filet
"Sannu phertyma, an dawo, amma kin shanyo rana" mama tafada cikeda tausayina
"Wallahi mama yau ana kwalla rana ga zafi"
Dan waken na zuba na saka mai da yaji nan na zauna nafara durashi acikina,ina ci muna hira da mama acikin hirar tamu har korafin samarin dake yawan damuna nayi mata, amma sai tace babu komai Allah ya zaba min abinda yafi Alheri agareni, daf da zan gama cin abincin naji sallamar hawwa kawata,
Dan waken na zuba mata muka shige daki muka kule "hawy nikam ina fama da jarabar samari, kema suna damunki haka?"
Murmushi tayi tafara gauraya dan waken dake gabanta tace "pherty ai kin san dama su samari haka suke da zarar sunga ka kusa gama makaranta sai subi su addabeka"
Baki na tabe na dubeta
"Hawy nidai gaskiya ko zanyi aure to sai nagama university saboda ni kinga ni kadaice a gidan nan banida yaya banida kani dole nice mai taimakawa su mama, gara ke kinada yayyu"
"A'a pherty nima fa ina son yin karatu saboda gaskiya karatu yanzu shine babban gata"
"Yawwa to kin gani, dan haka kuwa in dai zamuyi karatu to dole mu share samarin nan na zamani"
Yar dariya hawy tayi tace
"Ai dama hakan shine mafita"
Hirarmu muka ci gaba dayi har tsawon wani lokacin kafin hawy tayi min sallama ta tafi gida, gun mama nakoma na zauna muka fara hira.
Haka rayuwata taci gaba da tafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali domin banida wata damuwa da haka muka shiga s s 2 komanmu nida hawy muke yi, ajinmu daya bencinmu daya, kuma koda yaushe agida muna tare.
Lokacin da bazan taba mantawa ba shine lokacin da muka shiga s s2 second term har a wannan lokacin banida saurayi kuma ban taba son wani saurayi ba,bayan mun taso daga makaranta nake cewa hawy zata rakani kasuwa da yamma sai tace itama dama tana son zuwa akwai abunda zata siyowa mamansu, bayan nadawo gida nayi wanka naci abinci na huta wurin misalin karfe 3 na yamma na biyawa hawy gidansu anan nasamu yayanta nan ya fara tsokanata
"Kaga phertyn mama me kukan kitso"
Dariya nayi nace "kukan kitso sai kace hawwa"
"Ke me kike nufi, nice me kukan kitson?" Hawy ta fada daidai lokacin da take saka hijabinta
"Oho miki" nafada ina dariya, fitowa tayi muka kama hanyar kasuwa, cefane na iyowa mama sannan na siyo mana kayan amfanin gida, ganin kayan sun yimana yawa yasa na ce wa hawy mu ajiyesu in yaso idan mun karasa siyayyar sai muzo mu dauka mu tafi gida, wata sabuwar plaza muka je a bakin kasuwa, kuma da alama ma ko fara amfani da shagunan ba ayiba, "kinga mu bayar ajiyar anan" hawy ta fada tana nuna min plaza din,wurin mai gadin dake zaune awurin muka je muka bashi ajiyar sai yace mu saka daga dan ciki gudun kar tashi ya kamashi ga kayan awurin, daga ciki din muka saka muka koma cikin kasuwa.
Bayan mun kammala siyayyarmu ne na dubi Hawwa nace "gaskiya sai dai mu nemi keke napep saboda kayan nan namu da yawa"
"Nima haka zan fada kika rigani phertyn mama" tabani amsa cikeda zolaya
"Kya karata dai hawwan mama" nafada ina dariya amma dariyata sai ta tsaya saboda ganin kayanmu a warwatse agaban wannan plaza din, wani matashin saurayi muka gani tsaye sai yatsina fuska yake yanata nuni da hannunsa sai kace wani bebe, sai alokacin na iya daga kaina na duba sunan plaza din JAWAD PLAZA haka aka rubuta da manyan harrufa,
"Kut, kan bala'i" nafada cikin jin haushi
"Wannan rashin mutuncin fa" Hawy ta fada itama cikin bacin rai,
"Kuyi hakuri kunji me wurinne yazo, kuyi hakuri yayana" mai gadin wurin ya fada yana kallonmu
Nanfa naji na kulu saboda hango always din da nasiyo ayashe ana gani, "waye me wurin?
Shi ba acin arzikinsa?" Na tambayi mai gadin
"Kuyi hakuri kawai yara"
Bakin cikine ya rufe mu dukkanmu nida hawy saboda tsakanin nida ita babu mai iya zuwa ya dauki always dinnan dan kunya, "wallahi bazan hakura ba na fada cikeda masifa"
Wannan saurayin na gani ya nufo inda muke sai a lokacin na yi masa kallon kurulla farine jawur kamar kana taba fatarsa jini zai fito, yana sanye da doguwar riga jallabiya baka da wando jeans aciki, da hannu yake tambayar mu wai me ya faru yaga muna fada, "rainin hankali" nafada da karfi
"Ba yajin hausane yanmata daga turanci sai larabci, eh ai balarabe ne kuma bature" mai gadin ya fada yana washe baki
"Kar yaji din" nafada da karfi
"Yana ma ji, wulakancine kawai tsaba" inji hawy
Ganin munki kulashi yasa ya fara tambayar me gadin wai me ya faru nan yayi masa nuni da kayanmu da ya zubar mana, hannuwansa ya hada guda biyu ya dan risina a gabanmu alamun muyi hakuri, kayan yaje ya fara tattara mana, sai da yazo kan pad din sai ya jiyo yana kallonmu,dauke kaina nayi acikin raina ina cewa "dan iska kawai meye zaka wani kallemu" ina juyowa sai naganshi tsaye a gabana yana miko min ledar pad din "take, and am sorry queen" fuska na hade na bata rai na karbi ledar naja hannun hawy muka je muka deddebi kayan muka karasa bakin titi muna zuwa muka yi sa'a muka samu mai keke napep muka hau,har lokacin wannan saurayin yana tsaye yana kallonmu har sai da ya daina hangomu.
Hannuna hawy ta dafa "yauma da alama kinyi sabon saurayi"
"Tab, wannan ya zama saurayina ai fada zamu rinka yi saboda naga kamar ya fiya iyayi"
"Irinsu ai sunfi, sune first class" tafada cikin zolaya, haka muka rinka hirarsa har muka isa gida.
Tun daga wannan lokacin ba mu sake zuwa kasuwa ba har wurin sati biyu sai acikin sati na ukune sannan muka shirya muka tafi, kamar yadda muka saba kowacce tasha hijabinta dogo har kasa "phertyn mama wai mu meyasa ba zamu rinka irin wannan kwalliyar ba kullum mu kenan acikin hijabai" hawwa ta tambayeni daidai lokacin da zamu tsallaka titi,
"Kin San dai ko ana bidi'a bai kamata a yita agidan na'ibin liman ba ko?" Nafada ina murmushi caraf muka hada ido da wannan saurayin na rannan yana zaune akan farar kujera a bakin plaza dinnan,
"Kinga gayen nan na rannan amma karki kalleshi sosai kar ya gane maganarsa muke yi" na radawa hawy a hankali,
Ganinsa kawai muka yi tsaye a gabanmu yana murmushi, "barkanku da fitowa yanmata" ya fada cikin harshen turanci,
Mamaki nafara araina wai dagaske wannan bai iya hausa ba?