Sashe 10
Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwana nayi ina kuka har gari ya waye lokacin mutane suna wucewa jifa jifa masu zuwa office da masu kai yara makaranta dakyar nasamu ruwa nayi alwala nayi sallar asuba sai lokacin na tuna da cewar ko sallar magrib da isha jiya ban yiba,tashi nayi na fara neman gidansu jawad,sai wurin karfe 10 sannan na samu gidan, gidane mai mutukar girma da tsari kwankwasa gate din na fara yi ahankali mai gadin yazo ya bude min,
"Nan ne gidansu jawad ko?" Na tambayi mai gadin
"Eh nanne" hanya ya bani na wuce ciki, bin gidan kawai nake da kallo saboda tsaruwarsa ta isa, wani babban falo na shiga, ina bude kofar na hango jawad zaune daga shi sai three quarter baki da farar body hug yana yin tv game, daga can kuma wata matace tamkar balarabiya zaune tasha jan kunshi taci ado cikin koren lace tasha dauri tana lallatsa wata fankaceciyar waya,
"Assalamu alaikum"
Nafada lokacin da nake karasawa cikin falon
"Wa alaikis salam"
Matar ta amsa min, wacce kallo daya nayi mata na fahinci itace mahaifiyar jawad domin babu ta inda jawad ya barta, kamar su daya,
Ina shiga nasamu wuri na zauna, gaba ne yayi masifar faduwa saboda ganin irin kallon da jawad ya jiyo ya watso min, kallone mai nuna alamun ban sanki ba, ban taba ganinki ba sai yau,
Ahankali na gaishe da matar cikin sanyin jiki, na dan kalli jawad ta gefen ido wanda yafi mayar da hankalinsa akan game din da yake yi, nan na fayyacewa matar komai duk abinda ya faru tsakanina da jawad sai da na fada mata har kayan auren da ya kaimin da zancen cikin jikina,
"Jawad kasan wannan?" Ta jefa masa tambaya
"Ummi ni ban taba ganin wannan yarinyar ba sai yanzu" ya fada hankalinsa yana kan tv
"To kinji bai sanki ba, kila wanda ya kwatanta miki gidan bai kwatanta miki daidai ba, idan kuma wani ne ya turo ki dan ki bata mana suna agari to ki koma ki fada masa yakoma yabi wata hanyar"
Wasu zafafan hawaye masu dumi naji sun fara zarya akan kumatuna kamar an bude fanfo
"Jawad kaji tsoron Allah, ka tuna zaka mutu ka tarar da Allah, abinda kayi min nabarka da Allah shi kadai ne zai yi min sakayya"
Kofa aka bude aka shigo, wani matashi nagani mai kamada jawad amma daga gani ya girmi jawad din,
Cigaba nayi da fadin "jawad ka cuceni ka rabani da MARTABA TA, ka rabani da iyayena ka rabani da mahaifata, to insha Allahu sai Allah ya saka min...!"
"Ke maza tashi ki fice min daga cikin gidana, ya zaki zo har gidana kina yiwa dana mummunan baki?"
Murmushi takaici nayi nace "danki ya aikata fin haka shi yasan duk abinda nafada babu karya aciki amma ki binciki danki saboda Allah ne kadai yasan yawan yanmatan da ya yaudara yayiwa ciki"
Kallon jawad din nasake yi bayan na mike "jawad zan shiga duniya da cikinka ajikina kuma zan haifeshi zan reneshi har sai yayi girman da zai nemoka ya kasheka" ina kaiwa nan najuya na fita ina zubar da hawaye zuciyata tana tafarfasa, shi dai wannan yayan jawad din yana tsaye cikin mamaki yana kallonmu, ina fita nabi lungun gidan nafara tafiya ga azababbiyar yunwar da nake ji, ko kadan bana ganin abinda ke gabana, ban ankara ba sai ji nayi na fada kan wani dutse take dutsin ya bugi gefen marata ta dama, wani azababben zafi nafara ji yayinda marata da cikina suka gauraye suka fara ciwo babu kakkautawa, wata kara nasaka daidai lokacin da naji marata ta murda jini ya fara bin jikina.
Ummi A'isha🏻
[5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [5/5, 5:36 PM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
46-50
~~~Wata kara nasaka daidai lokacin da naji marata ta murda jini ya fara bin jikina, juyowa tayi ta kalli Sadiya da A'isha wadda ko wacce acikinsu hawayene kawai ke bin kumatunta sun rafka uban tagumi,
"Kun san meya faru?" Ta tambayesu tana murmushin takaici
"Tayaya zamu sani alhalin baki fada mana ba" suka fada atare
"Amma meya biyo baya?
Ni na kagu naji karshen labarin" Sadiya ta fada tana goge hawayen fuskarta,
"Zakuji ai amma ba yanzu ba saboda ko sallar azahar ba muyi ba gashi har lokacin la'asar yayi,kuma ni yunwa ma nake ji"
"Ai ni yau labarinki ya kosar dani dan ko yunwar ma bana ji" A'isha ta fada a hankali
"Hmmm duniya kenan kaji abubuwa iri iri, ku tashi kuyi salla ni tunda bayi zanyi ba sai na dafa mana indomie" Sadiya ta fada daidai lokacin da take tashi daga kan gadon, wurin da suke girki ta nufa domin dora musu abinci yayinda A'isha da pherty suka fita yin alwala.
Bayan sun idar da sallar ne suka fara cin abinci, wayar pherty ce ta fara ringing tana neman agaji, dauka tayi ta duba, yaya aadil ne da kamar ba zata dauka ba sai kuma ta daga tafara magana a hankali
"Yayana"
"Pherty na yau shine bakya nema na?"
"Ayya yaya aadil bana son shiga hakkin anty nane shiyasa"
Murmushi ya danyi sannan yace da ita "kinaji da antyn nan naki kila ma idan kikazo gidan hade min kai zakuyi"
"A'a yaya" tafada tana dariya,"kaga zaka sani in kware gashi abinci nake ci"
"Zaki ci dani?"
"Why not?"
"To aci dadi lafiya" yafada yana murmushi.
Kashe wayar tayi tana dariya "kuji yaya aadil da tsokana ko a ina dadin yake, shi dan makaranta ai baya wani samun dadi"
"Mudai kici gaba da bamu labari kawai malama" Sadiya ta fada
"Gaskiya kam" A'isha ta sake fada,
"Hmmm to,tunda kun matsa bari nakarasa yanzu, tunda na fadi ban sake sanin a inda nake ba sai bayan wani lokaci sannan na dawo hayyacina, ahankali na bude idona,acikin wani daki naganni wanda abisa dukkan alamu dakin asibiti ne, gefena na kalla wannan saurayin nagani yana zaune yana jiran farkawa ta, koda muka hada ido dashi sai naji nafara hawaye, da sauri ya karaso gaban gadon da nake kwance "sannu pherty, kin tashi?" Ya fada da sauri, ban bashi amsa ba illa kukan da yaki tsayawa wanda nake yi ganin haka yasa shi juyawa ya fita da sauri.
Jim kadan sai gashi shida wani doctor sun shigo tare, da sauri doctor din ya karaso inda nake "sannu, inane yake miki ciwo?" Muryata a dashe nace "gefen marata ne yake min ciwo sosai gashi ina ji kamar an anjiye min wani katon dutsi a wurin"
Kallon yayan jawad likitan yayi ya girgiza kai, "Aadil am sorry to say gaskiya yarinyar nan ta samu matsala sosai a mararta wanda ina tunanin idan ba wani iko na Allah ba bazata kara iya daukar ciki ba balle har ta haihu, ina jin gaba daya wurin yayi damage dan ko lokacin da na dauki hoton wurin naga yadda buguwar da tayi ya haddasa mata matsalar zubewar cikin jikinta, gashi kaga she's still bleeding, jini take fitarwa kamar zata karar da jinin jikinta"
"Pls doctor help me, pls and pls try your best pls..!" Wanda aka kira da suna aadil ya fada a rude
"Aadil am so sorry because i hv trying my best but abunne yafi karfina, duk wanda yace maka yarinyar nan zata sake iya daukar ciki to ya yaudareka ne kawai, saboda gefen mararta gaba daya ya tashi daga aiki, kai harta rayuwar aure ma dakyar idan zata iya saboda za arinka fama mata wannan ciwon da take tare dashine, but ga shawara guda daya ka fitar da ita kasar India kawai, ina jin idan Allah ya taimaka zata iya samun lafiya but is under probability" yana kaiwa nan ya juya ya fita daga cikin dakin,
Juyowa aadil yayi ya nufo inda nake kwance ina kuka mai tsuma zuciyata "yanzu shikenan ni ba mace bace?" Tambayar da naketa yiwa kaina kenan acikin zuciyata,
"Pherty" ya fada idonsa cikeda hawaye
"Kiyi hakuri kinji, nayi miki alqawarin zan taimaki rayuwarki har sai inda karfina ya tsaya, sannan ina son ki manta da duk wani abu wanda ya faru dake a baya, ki fuskanci rayuwar da zata zo miki nan gaba, kuma ki yarda da qaddarar data hau kanki, ki dauka hakan wata jarrabawa ce daga Allah subhanahu wata ala"
Daga kaina nayi na kalleshi abin mamaki sai na ganshi yana kuka, hawaye suna bin kumatunsa,
"Nagode yaya Aadil amma karka wahalar da kanka wurin taimako na saboda mutuwa zanyi, ni yanzu ba mace bace, babu namijin da zai yi sha'awar aurena, jawad ya cuceni ya rabani da MARTABA TA, mutuwa yanzu itace tafi dacewa dani"
"Karki sake fadin haka pherty domin zakiyi sabo, babu kyau bawa yana nemarwa kansa mutuwa, kidaina yiwa kanki fatan mutuwa kinji, ki dauki kaddarar da Allah ya aiko miki da ita, nikuma da taimakon Allah zan yi duk iya bakin kokarina na ganin kin samu lafiya sannan zan dawo miki da martabar ki"
Idanuwa na narufe naci gaba da hawaye yayinda shi kuma ya fice daga cikin dakin da sauri, hannu nasa na shafo marata wadda ke radadi da zugi ga wani bleeding da naji ina yi kamar an bude fanfo.
Ban sake ganin yaya Aadil ba sai dare, yana shigowa ya hada min tea ya taimaka min nasha, doctor yazo ya bani magani nasha ba tareda bata lokaciba bacci ya dauke ni.
Kwanana uku a asibitin ina fama da ciwo kullum babu sauki, a kwana na hudu ne yaya aadil yazo da driver suka daukeni muka tafi airport lokacin ko tafiya bana iyawa, acikin jirgi ma ajikinsa ya jinginani nayi barci har muka je kasar India.
Wani hadadden hospital aka kaini aka kwantarni nan manyan doctors suka taru akaina suna yimin aiki.
Nasha wahala mutuka domin bayan sun gama min aiki harda wankin ciki suka yimin da wasu karafa, bayan an gama aikin ne yaya aadil ya shigo cikin dakin nake, sannu yayi tayi min nan ya samo min abinci naci nasha magani, duk wata kulawa wacce marar lafiya yake bukata to ina samunta wurin yaya aadil shine ya rinka kulawa dani har na tsawon sati biyu amma har a lokacin zan iya cemuku har yanzun nan da nake baku labarin ina jin wannan ciwon a marata domin ba karamar buguwa nayi ba.