← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 27

Sashe 1

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hausa novel blog
‹ › Home
View web version
Friday, 6 January 2017
aisha ummi at 08:34
MARTABA TA 1-50
5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
Pg 1-5
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI!!

A gaggauce take fitowa daga cikin bathroom din tana daure da towel wanda ya rufe iya gwiwarta, da sauri ta nufi room 4 dakinsu, tana shiga ta isa gaban mudubi ta fara shiryawa cikin sauri nikaina Ummi A'isha sai da nashiga mamaki saboda ganin tsaruwar dakin wanda sam baiyi kama da na yan makaranta ba, komai a jimulle yake acikin dakin tamkar dakin gida, bayan ta gama shiryawa ne ta isa gaban makeken akwatinta ta bude ta ciro wata hadaddiyar doguwar riga kalarta blue mai duwatsu tayi mutukar tsaruwa, da sauri ta saka doguwar rigar bayan ta feshe jikinta da daddadan turaren Mazda, dan siririn mayafi blue kalar rigarta ta yafa tayi rolling tare da daukar wayarta wadda ta kasance kalarta blue kirar galaxy s7, dogon takalmi ta sa baki ta jiyo da zummar ficewa daga cikin dakin, cubus suka yi da wasu yan mata guda biyu.

Kallon kallon suka fara, cikeda fada daya daga cikin yanmatan ta kalleta "wai yau ma haka zaki fita ba kiyi mana girkin ba?

To wallahi yau a dakin nan sai dai kowa ya zauna da yunwa dan wallahi nidai ba zanyi girkiba"
Kallonta budurwar tayi "haba Sadiya kinga fa nakusa makara tun jimawa aka shiga lecture, dan Allah kuyi mana girkin ko taliya ce ku dafa mana" ta karashe maganar kamar zata fashe da kuka
"Tab wallahi yau kowa tashi ta fissheshi fati amma wallahi ba zanyi girki ba, ke kullum babu abinda zakiyi da zarar anyi magana sai kice lecture kamar ke kika fi kowa karatu"
Sai a lokacin daya budurwar tayi magana wadda tun lokacin da suka fara mahawarar take tsaye tana kallonsu "ya isa haka ku da kullum baku da aiki sai na fada, in dai girki ne ni zanyi, shikenan period magana ta kare"
Harararta Sadiya tayi "sai kiyita yi ai, dama ai dan kina yine shiyasa bata son yi"
"Eh din ina ruwanki sai tayi din" fati ta fada tana hararta, "ya isheki haka malama" Sadiya ta fada cikeda masifa
"Maza dai kar ki tafi har afito daga lecture din kin tsaya neman fadan da kika saba" A'isha ta fada lokacin da take shiga cikin dakin murmushi fati tayi tareda yiwa sadiya gwalo ta fice daga cikin dakin da sauri, tana fita A'isha ta kalli Sadiya tana dariya "Allah ya barni daku yaran nan kuna bani dariya wallahi"
Dariya Sadiya tayi "ai nasan zanyi missing din fati idan muka gama makarantar nan" dariya A'isha tayi ba tareda tace komai ba.

Koda fati ta fita a hankali take takunta har ta fita daga harabar hostel din, jin karar wayarta ne ya sata rage takun da take tare sakin wani murmushi "hello yayana yakake?" Tafada tana murmushi shima murmushin yake daga inda yake zaune akan luntsumemiyar kujerarsa ta office sai juyawa yake, office din nashi ya tsaru mutuka, farine bufulatani na asali,dogo marar kiba yana da dogon hanci mai tsini tareda manyan idanuwa farare kakal, sumarsa kawai zaka kalla kasan cewa ruwa biyune,yana sanye da blue din riga mai dogon hannu da bakin wando, wuyansa daure da necktie baki,a yanda na kiyasto muku shekarunsa ba zasu haura 34 ba,
"yanmata yakike?" Yafada yana murmushi mai kayatarwa
"Yaya Aadil kaga ka hana Sadiya, kullum kullum sai ta jani da fada" takarasa maganar cikeda shagwaba
Tsam ya mike daga kan kujerar da yake ya nufi window din office din, ahankali ya sauke glass din ya fara hango mutanen daketa kaiwa da komowa a kasan benen nasu wanda ya kasance hawa bakwai kuma shi office dinshi a last floor yake.

"How comes?" Ya fada yana dariya "common baby,haba yanmata yau ma sai da kuka yi fadan?

Ke tsokana gareki ita kuma Sadiya saurin fushi, amma duk me ya kawo fadan?

Fada min kinji sha lele" ya fada cikin sigar lallashi
Rausayar da kansa yayi tareda kurawa wani dan kayataccen lambu dake girke a can kasan office dinsu ido, "kin san bana son bacin ranki ki fada min menene"
Shiru tayi bata bashi amsa ba tana nazarinsa a hankali
"Kina so ki tayar min da hankali ko?

Kina so hankalina ya tashi na kasa samun nutsuwa?"
Dan murmushi tayi hakan ya sake rudashi dan duk a zatonshi kuka take
"Kuka kike?,uhm?"
Sai a lokacin tayi murmushi "Kai yaya Aadil nifa ba kuka nake ba, kawai dai ina tunanin irin son da kake yimin ne, domin na kasa banbance tsakanin nida anty Salima wadda kafi so"
Murmushi ya saki mai kayatarwa ya saki dan zaren labulen dake hannunsa ya fara takawa a hankali ya nufi kayataccen falonsa.

Murmushi kawai yakeyi "kema kin san nafi sonki ai, shiyasa ma nabar Salima a gombe saboda ke idan na aureki nan zan kawoki kusa dani yanda zan samu damar kulawa dake"
"Hmmm yaya aadil kenan to kuma idan anty salima taki fa?"
Fridge ya bude ya dauko madara mai sanyi ya zauna ya fara kurba kafin ya fara bata amsa
"Ai itama antyn naki tasan irin son da nake miki saboda kin san ance amarya bata laifi"
Bata rai tayi kamar yana ganinta "ni baka sona dayawa, idan kana sona kayi min waka"
Dariya ya fara harda kwarewa "waka kadai kike so yanmata?"
"Ehh" tafada cikeda shagwaba
"To zanyi miki kar kiyi kuka pls, karkade kunnenki kiji zan fara"
"Ina jinka" ta fada a hankali
"Fatima, fatima yar auta, fatima tauraruwar mata
Dafari da farko, fatima gunki nataso da kidan jita fatima daure leko
Yau ga mai sonki fatima dauke da sako
Nidai fatana fatima kice dani miko,
Ki amince min fatima nayo roko zan sa kuka in bakya sona yanmata"!

Dariya fatima tafara kyalkyalawa "ayya yaya aadil basai kayi kuka ba, ina sonka kar kayi kuka"
Dariyar shima yayi "to tunda kin hanani shikenan bazan yi ba amma da baki hanani ba da kuka zanyi"
Murmushi tayi "wakar tayi dadi yaya aadil, dama ka iya waka shine baka taba yimin ba?

Tunda ka iya yanzu kullum sai kayi min".

Murmushi ya saki mai hadeda farin ciki dan bashida buri illa yaga fatinsa tana cikin fara'a da annashuwa
"Zan rinka yi miki, amma yanzu me kike?"
"Lecture zan je"
"Kinyi laifi, dama lecture zakije shine baki fada min ba, kika biyeni na rike ki da hira?

Idan nazo gombe sai nayi punishing dinki"
"Am sorry yayana"
"Na hakura amma kiyi sauri ki shiga lecture"
"Yes sir" tafada tana dariya tareda saurin zare wayar daga kunnenta dan tasan bazai kara cewa wani abuba tunda tace mishi lecture zatayi.

Sai alokacin da ta gama wayar sannan ta fara daga kafarta da niyyar taje ta iske lecture din amma sai me?

Tana bullowa ta wurin hall din ta hangoshi tsaye jikin motarsa kirar BMW ash colour, shikuma yana sanye cikin dark red din t shirt da black din trouser, sumar kansa tamkar ta larabawa domin a kanannade take akalla shekarunsa ba zasu wuce 30 ba a duniya, yana da kyau mai mutukar daukar hankali, nidai Ummi A'isha nakasa tantance tsakanin saurayin farko da wannan na biyu wanda yafi wani kyau da aji.

Take ta murtuke fuska domin a rayuwarta idan da wanda ta tsana to JAWAD ne, nan fa ta fara harare harare marassa dalili, a hankali ya taso yazo yasha gabanta,
"Fatima Xarah" ya fada yana kallon fuskarta
Dauke kanta tayi tamkar bata san da mutum a Gabanta ba,
Ahankali ya fara yi mata magana tamkar wani me yin rada,cikin hausarsa marar fita me kamada ta yan koyo ya soma yi mata magana amma abisa dukkan alamu hausar bata samu gurbin zama ba a bakinsa saboda fillanci da turanci su yafi iyawa sai wasu lokatan yakan dan hada da larabci domin asali ma shi hausa wahala take bashi saboda bai iyata ba shiyasa bai fiya yawaita yinta ba, ganin zai wahala da yawa yasa ya fara yi mata magana cikin harshen turanci,
"Queen why all this hateness?

Meyasa kika tsaneni yanzu?"
Wata harara ta wurga masa kafin tayi magana cikeda gatsali
"Kaga Malam ni dama can ban sanka ba, balle har na soka, so stay away from..."
Cikin sauri ya katseta idonsa har ya sauya launi daga fari zuwa ja
"Karya kike fatima kin sanni, kuma kin soni, kuma har yanzu kina sona, kuma wallahi dole kici gaba da sona har abada"!

Wani dan malalacin murmushi ta saki kafin ta kalleshi fuskarta cikeda masifa
"Kai zan so?

Hmm har abada bazan taba sonka ba, kasa a ranka fatima makiyiyarka ce ta har abada, dan haka ina mai shawartar ka da ka cire Fati daga sahun masoyanka domin bata kaunarka ko kadan"
Kallonta yayi ido cikin ido
"Karya kike, ke masoyiya ce agareni ba makiyiya ba, kuma sunanki da matsayinki bazai taba gogewa daga masoyiya ba, zanci gaba da tattalin sonki acikin zuciyata kamar yadda kema nasan kullum da sona kike kwana kike tashi"
Sausauta muryarsa yayi tareda ci gaba
"Queen ki sausautawa ranki, ki taimakawa zuciyata da taki mu ci ribar soyayyar da mukewa junanmu"
"Dawa zaka rayu?" Ta tambayeshi cikeda bacin rai
"Kar ka kuskura kayi gangancin rayuwa dani, domin tsanar da nayi maka tana iya sawa na kasheka"
Cikin bacin rai ya kalleta idanuwansa sunyi jajur
"Sai na rayu dake in yaso ki kashenin domin na shiryawa mutuwata in dai ta sanadinki ne, amma ki sani da sonki zan koma ga mahalicci na"
Yana kaiwa nan ya juya ya nufi motarsa cikeda bacin rai kafin wani lokaci har ya bar cikin makarantar cikin wani mahaukacin tuki, itama fatin cikeda damuwa hadeda bacin rai ta ta juya tabar wurin, lecture din da bata shiga ba kenan.

Ummi A'isha🏻
[5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
Pg 6-10
~~~Cike da bacin rai pherty ta juya tabar wurin ta nufi hanyar hostel tana tafe zucyarta na yi mata tukuiki kamar wuta,
A daidai wata baranda ta zauna ta fara kuka "nikam me zan yiwa jawad ya kyale rayuwata na huta?

Na tsaneka jawad bana sonka bana kaunarka, bana kaunar duk wani me kaunarka, i hate u!"
Haka take ta furtawa tamkar wata zautacciya.
Chapter 1 · 0% Book details