Sashe 65
Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
............Yau safiyar Laraba muka tashi da labarin dawowar wasu manyan jami'ai na wannan hukuma tamu kamar yanda manyanmu suka sanar.
Na kasance a cikin tawagar masu zuwa tarbarsu da aka ɗiba a cikin mu ƙananun ma'aikata, akwai kuma manyanma.
Hakanne ya tabbatar mana lallai waɗanda zamuje tarar sunada muhimmanci a wannan hukuma. Haka kawai na tsinci kaina da faɗuwar gaba, zuciyata sai wani irin zallo take kamar zata faɗo ƙasa.
Ƙirjina na dafe ina lumshe idanu, dama tun jiya nakejin tamkar wani gagarumin abu na kusanto rayuwata, sai dai bansan minene ɗinba.
Mun iso airport ɗin akan lokaci, dan jirginma bai kai ga saukaba sai nan da minti arba'in kamar yanda aka sanar damu.
A yanda mutane suke kallonmu musamman ma mu matan da muka kasance mu biyu kacal yasa duk na takura, sanye muke da Uniform wanda ni kaina nasan sunma surata matuƙar ƙyau, tabbas bani da ƙyawu mai tsanani amma ALLAH ya azurtani da ƙyaƙyƙyawar surar dake da wahalar samu ko a cikin matanma, wadda itace ke fisgar maza da yawa a gareni, akwai baby hijjab dana saka kafin na ɗora hular Uniform ɗin a saman kaina, hakan ne zai baka amsar kasancewata musulma kai tsaye.
Addu'a na rinƙayi a zuciyata, saima na saka eyeglasess a idona saboda kallon ya gundunreni.
Adadin mintuna na cika jirgin da muke tabbacin jira ya iso, saida ya gama shawagi a sama kafin ya sauka a inda ya dace, wannan shine karon farko da nazo airport a rayuwata, hakan ya sakani tsarkake sunan UBANGIJI daya sanya fasaha ga zukatan waɗanda suka ƙera jirgi, sannan ya bashi ikon tashi sama duk da girman da yake dashi.
Bugun zuciyata ya sake sauya salon bugawa da sauri-sauri, hakan ya sakani rumtse idanu dukkan jikina na wata irin tsuma, haka kawai sai nakejin kamar na kama kuka.
Taɓanin da akaine ya sakani buɗe ido da sauri, ɗaya daga cikin ma'aikacinmu ne da yake nema takurama rayuwata, na kallesa ina ɗauke kaina dan haushi yake bani, shi a dole wai sona yake, tun a wajen training ya maƙalemin, sai kuma akai rashin sa'a muka tsinci kanmu a waje guda.
Ganin ya gyara tsayuwa zai fara magana nai gaba abuna. Dai-dai fasinjojin jirgin sun fara fitowa.
Duk wanda ya fito a jirgin idonmu a kansane, sai dai ganin babu wanda ya motsa daga jami'anmu ya tabbatarmin namu tawagar basu fitoba har lokacin.
Sai da kowa ya gama fitowa har babu alamar sauran mutane kafin wata mata da yara biyu ta fito, sai wata kuma a bayanta ita riƙe da hannun yaro namiji, sai wata na biye musu baya itama.
Suma sai da suka sauka duka sannan sannan fitowar wani sadauki da tai daidai da tsananta bugun ƙirjina ya fito.
Zaratan mazaje uku da doguwa budurwa na biye dashi a baya.
Jinai ƙafafuna na neman gaza ɗaukata, hakan yasani saurin jingina da ɗaya a cikin motocinmu gudun karna faɗi.
Jawaad dake fitowa ya sauke idanunsa akan sir Ahmad barewa, kafin yaci gaba da bin ma'aikatan tadabbaci ke nuna sunzo tarbarsu ne.
Kansa tsaye inda su sir Ahmad da wasu manya suke suka nufa, inda shima Sir Ahmad ɗin ya nufesu fuskarsa cike da fara'a da farin cikin ganinsu.
Gaba ɗaya sauran ma'aikatan sukaja layi alamar girmamawa, miƙewa nai ina sauke numfashi tamkar wadda tai gudun fanfalaƙe.
Sai da ya gama gaisawa da manyansa kafin su nufomu su dukasu.
A tare muka buga ƙafafu tare da yin salute nasu cikin nuna tsantsar girmamawa.
Jawaad dake tsaye yana ƙare musu kallo idonsa ya sauka kan matashiyar budurwa mai hijjab.
Ganin ya tsura mata idanu Jabeer da suke bayansa yay mata umarni data cire glasses ɗin idonta a ɗan kausashe.
Kawai jinai idanuna sun cika da ƙwallan da bansan dalilinsu ba, na zare eyeglasess ɗin idona kamar yanda aka umarceni tsigar jikina na wani irin tashi tamkar nai gamo da halittar ban tsoro.
Babu zato idanuna suka shige cikin nashi idanun masu wani sinadarin da baki bazai iya faɗaɗa bayani akaiba.
Kasa jurewa nai na janye nawa ina rissinar da kaina tamkar zuciyata zata faɗo ƙasa.
Shima cikin basarwa ya janye nasa idanun cikin wani salo na halin ko in kula.
Sai da ya gama ƙare mana kallo mu duka kafin yay guntun murmushin daya saka kumatunsa loɓawa.
Saitin inda nake yay mana nuni da hannu alamar mu bashi hanya, hakan ya sakamu darewa muka rabu biyu ya gittamu ya wuce, mayen ƙamshin turarensa na rige-rigen shiga ƙofofin hancinanmu.
Da sauri wasu a cikinmu suka nufi motocin suka bubbuɗe musu har manyan mu da mukazo tare wajen, ni dai bamma iya koda motsiba daga inda nake, saboda bani da wani ƙarfi sam balle samun kuzarin yin abinda ya dace.
Sai dai idona akan motar daya shiga shi kaɗai baya aka maida aka rufe masa, haka kawai naji tamkar ana kallona, kallo kuma irin na ƙurilla, sai dai iya dube-dubena banga alamun kowa da idonsa ke kainaba, saboda mutane sunata hada-hadarsu ne.
Hannu na ɗora a hankali bisa ƙirjina dai-dai saitin zuciyata ina lumshe idanu, wasu ƙananun hawaye suka silalomin a kan kumatu, saurin jan hulata nai sosai yanda zata hana kowa kallon halin da nake ciki kafin nasa handkherchief na share cikin dabara ina nufar mota nima.
Jawaad da tunda ya shiga mota idonsa ke akanta yana ƙare mata kallon da shima baisan dalilinsa ba ya lumshe idanu yana huro iska ta ƙofofin hancin, kuma buɗewa yay sai yaga wayam babu ita a wajen, cikin halin ko in kula yaɗan taɓe baki yana ɗauke idanunsa daga kallon wajen ma baki ɗaya ya maida ga wayarsa.
Tanda muka fara tafiya nake jerama kaina tambayiyin da bansan amsarsu ba.
“Miyasa nakejin tsoro? Miyasa yay min kwarjini fiye da kowa? Miya sakani kuka? Minene ma'anar halin dana shiga bayan banida wata alaƙa da wani abu daya taɓa shafar irin wannan yanayin dana tsinci kaina a ciki balle nace na tunashine?”.
Waɗanan tambayoyi su naita jerama kaina har muka iso, tarbar da muka iske an shirya musu ananma ce ta sakani samun damar zare jiki na koma can gefe na zauna ina maida numfashi da addu'ar samun daidaituwar wannan baƙon yanayi nawa da baida alaƙa da komai.
Dafanin da akayine ya sakani juyowa, Ummie ce, hakan yasa tana zama sai kawai na fashe mata da kuka.
Ɗunbin mamaki ya bayyana a fuskar Ummie, tai kasaƙe tana kallona tamkar wata sokuwa,
“Bily lafiyarki kuwa?”.
Ban bata amsaba, saima ƙarfin kukana dana ƙara, tai shiru kawai ta sakamin ido, saida nayi mai isata nai shiru dan kaina sannan ta sake jefamin tambaya.
“Bilkisu mike faruwa ne wai? Ko an miki wani abune da kuka tafi?”.
Kaina na girgiza mata alamar “A'a”.
Tace, “To minene ya faru? Ko baki da lafiya ne?”.
“Lafiyata ƙƙalau kawai na tuna su babane” na samu kaina da mata ƙarya batare danasan dalilin hakanba, dan nasan bama ɓoyema juna abu sam.
Numfashi ta sauke tana dafani, cikin tausasa murya ta shiga lallashina damin nasihar addu'a su baba ke buƙata bawai kukana ba.
Kaina na ɗaga mata kafin nace, “Nagode Ummie, insha ALLAH bazan sake yiba”.
Tai murmushi tana canja akalar firar tamu zuwa wata,
“Kutt Bily basawannan namu da kuka tarofa sunji gishiri da magi, musamman mai green ɗin Suit ɗinnan”.
Gabana ya sake faɗuwa jin ta ambacesa, amma saina danne cikin ƙaƙaro murmushi nace, “Kingani ban wani tsaya ƙare musu kalloba, yanzu haka babu kamannin wanda zan iya kawowa a cikinsu”.
Tace, “Tab, amma lallai kinyi gwari dan wlhy anci kasuwar sama babuke Babie, ai har sunan mai green suit ɗinma na riƙe”.
Kallonta nayi da mamaki, tare da jin zuciyata tai zallo, kamar na tambayeta yaya sunan sai kuma na taɓe baki ina miƙewa, “Kinga dan ALLAH bar wannan shirmen tashi muje, yaushe kika fara lalacewa ne haka Ummie?”.
Dariya ta tuntsire da ita tana dukan kafaɗata, tace, “K nakai aurefa, sannan dukkan burikanmu sun cika, miya rage mana kuma? Musamu mazajen aure kawai, kodan ke kin samu Yah Qaseem a hannune”.
Kallonta nayi a wani irin yanayi jin ta ambaci yah Qaseem, sai ban iya furta komaiba nai gaba abina ina murmushin ƙarfin hali.
Itama bata sake maganaba ta biyoni da hanzari muka dai-daita tafiyarmu.