← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 75

Sashe 32

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan mun gama cin abincine ya ɗaukeni a napep ɗinsa zuwa ƙyamiz, an bani magani tare da allura muka dawo gida.
Mamaki ya kamamu saboda iske jibga-jibgan motoci guda biyu da mukayi a ƙofar gidan, sai walƙiya suke.
Na kalli Yaya Shu'aibu ina faɗin, “Yaya baƙinmu ne waɗannan kokuwa?”.
Cikin jimami yace, “Wlhy ban saniba Bilkisu, amma inhar hakane to lallai inaga Kawu Ali ne kuwa yazo, dama lokaci-lokaci yakanzo su gaisa da Inna idan ya samu dama?”.
“Kawu Ali? Shikuma wanene shi?”.
Da mamaki sosai akan fuskarsa ya kalleni, “Bilkisu kina nufin wai baki san Kawu Ali ba shima? Yayansu Inna ne fa, ɗakinsu ɗaya da Inna ai”.
“Wlhy ban sanshiba Yaya, kana nufindai shima babansu ɗaya da Innata kenan?”.
“Ƙwarai kuwa Bilkisu”.
“Yaya to ko shine suke cema Ɗan iya?”.
“Ƙwarai kuwa Bilkisu shine, amma nayi mamaki, na lura dai ke babuma wanda kika sani a dangin kenan?”.
Murmushin yaƙe nayi zuciyata na suka, murya na rawa nace, “Ai yaya sanda Innata nada rai babu wani ɗan uwanta dake raɓarta, nasan dai lokacin ina ƙarama takanje dani wasu wajajen gidan dangi, amma sai na lura saboda tana da nakasa kamar kowa gudunta yakeyi, Inna Zainabu ma abinda yasa ban manta da itaba ita da Kawu Manu saboda Innata na yawan ambatarsune”.
Tausayina sosai na gani a fuskar Yaya Shu'aibu, ya girgiza kansa kawai yana sauke numfashin tsantsar takaici, “Karki damu Bilkisu, komai na rayuwa da kika gani akwai ƙalu bale, watarana sai labari, irinku da kuke tashi cikin rashin gata ALLAH yafi ɗaga darajarku da ni'imomi masu yawa da komawa birge wanda suka juya muku bayan a lokacin da kuke buƙatar taimako, mu shiga ciki kinji, ALLAH ya ƙara miki haƙuri da jimirin cinye jarabawar rayuwa”.
Murmushi nayi ina share hawayen da suka zubomin a fuska, kusan a tare muka fita zuwa cikin gidan.
Ashema ba shi kaɗai bane harda iyalinsa, matarsa da ƴaƴansa namiji da mace su biyu, kallo ɗaya nai masa na gano asalin kamanninsa da Inna zainabu, yana kuma yanayi da innata itama, da yake ni sam ban biyo innata komaiba, gaba ɗaya kamannina na babana ne, dan dana biyo Innata da nazama ƙyaƙyƙyawa kuwa, dan su jinin fulanin asaline.
Inna tanata hidima da baƙinta, bakinta kam a washe tamkar gonar audiga.
Duk tsugunnawa mukai ni da Yaya Shu'aibu muka gaishesu, inna daketa faman washe haƙora tace, “To ka gantanan Ali, wannan itace ɗiyar Asiyar da nake faɗa maka”.
Idonsa a kaina yace, “ALLAHU akbar, ashema ta zama budurwa? Koda yake rabona da ganin Asiya tunfa kafin nabar ƙasarnan, lallai sheɗan ya jagoranci zukatanmu wajen raunana zuminci, yanzu ace ɗan uwanka da kuka tashi gida ɗaya dan aure ya ɗaukesa shikenan sai zuminci ya yanke? Manu ne ma wlhy yake sanarmin rasuwa lokacin bana ƙasar shiyyasa banzo ta'aziyya ba, ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata, ke kuma data bari ALLAH ya rayaki kinji”.
Hawaye na share ina amsawa da amin.
Daga nan ya koma kan Shu'aibu yana masa tambayoyi akan yanzu mi yakeyi?.
Matarsa dai da ƴaƴansa basa cewa Uffan, saima faman danne-dannen wayoyi sukeyi.
A cikin tambayoyin da yakema Yaya Shu'aibu ne yakejin ai ya kammala diploma ɗinsa, daga haka karatun ya tsaya, a take yace ya bashi takardun zai nema masa makaranta ya koma, ya juyo gareni yana tambayata nifa?.
Kaina a ƙasa nace, “Ai kawu ni koma Secondary ɗin ban kammala ba”.
Ya ɗan nuna damuwa saman fuskarsa, hakanne ya sakashi maida kallonsa ga Inna yana faɗin, “To nifa inaga wannan itace hanyar dazan gyara kuskurena akan Asiya, Zainabu zan tafi da Bilkisu ta zauna a gidana cikin ƴan uwanta, itama ta samu ilimin da zata taimaki kanta koda anan gaba babumu a raye”.
Take fuskar Inna ta canja launi, hakama matarsa da ƴaƴansa wani kallo na sukemin mai kama da wannan ƙazamar?.
Yaya Shu'aibu ne kawai ya bayyana tsantsar murnarsa a fili, kafinma inna ta bada amsa tuni Yaya Shu'aibun nata godiya.
Hakan ne ya dakatar da ita daga son hawa dokin naƙin datai niyyar yi.
Niko bammasan yazan fasalta muku yanayin dana shigaba, ɗumin hawaye kawai nakeji suna bin kumatuna, duk da naga rashin jin daɗin iyalansa hakan bai hanani ƙwaɗayin binsu ba, koba komai burina nayin karatu mai zurfi ashe zai cika a duniya, insha ALLAHU zanyi haƙuri da kowane irin halin daza fuskanta daga garesu domin samun cikar burina”.

Abu kamar wasa sai ga magana ta zama babba, dan kuwa dai Kawu Ali cayay nai shiri mu wuce, ba kuma saina ɗauki komi ba, ni kaɗi suke buƙata.
Tashi nai nayi wanka kamar yanda Yaya Shu'aibu ya umarceni, sai gani na fito tsaf cikin irin kayan da Sani ɗan gidan Uwargida ya bani kala uku.
Yanda na ɗanyi tsaf na kula ya sakasu mamaki, dan sanda nake ɗazu kam tamkar an kwatonj da ga bakin kura ne.
Kewar Yaya Shu'aibu kawai naji, amma Inna da Lawusa banji komaiba kam, Yaya Shu'aibu ya kwantarmin da hankali akan ai tunda inacan zai dinga zuwa dubani, da dai kam baya zuwa, dan sau ɗaya ma ya taɓa zuwa gidan, tunta kuma matar Kawu Alin tai masa wulaƙanci shi da inna bai sake zuwa ba koda wasa, amma yanzu darajar zan zauna a gidan zaike zuwa insha ALLAHU.
Yamin nasiha yanda zanyi ƙoƙarin zama da kowa lafiya ba tare da anyi kuka da niba, ya sake maimaitamin muhimmancin haƙuri a duk halin da zan tsinci kaina.
Godiya nai masa cikin share hawayena.

Da zamu wuce har mota suka rakomu, Kawu da matarsa suna a mota ɗaya, yaransuma motarsu daban, to nima sai akace na shiga motar yaran nasu.
Ina kallon namijin baiso hakanba, dan harda guntun tsaki yaja, macenma tanata ƙunƙuninta da ba kowa kejiba.
Suna gaba niko ina zaune a baya a maƙure tamkar wadda aka sace, a haka muka bar anguwar su Inna na ɗaga mana hannu, niko ina share hawayen sabo dana farayi dasu.......

________________________
JAWAAD
________________________

Koda suka baro gidan Alhaji kokino station Gimba ya nufa dasu, Jawaad kawai ya fita a motar amma banda Aliyu, dan ɓoyensu akeyi ba kowa yasan da dawowar tasuba.
Gimba ya juya da mota domin maida Aliyu gida, yayinda wani ya ƙaraso da sauri ya amshi kayan hannun Jawaad bayan ya gaidashi cikin girmamawa.
Fuskarshi da ɗan murmushi ya amsa masa, yana gab da shiga Office ɗinsa ya hango Qaseem na fitowa daga Office ɗinsa cikin hanzari, da alama dai wani uzirin zaije, baki Jawaad ya taɓe ya shige abinsa.
Aiki garesa danƙam a office ɗinan, harma tunanin ta ina zai fara yakeyi, ya zauna yana sauke numfashi bayan ya rataye rigar suit ɗinsa jikin kujerar.
Yana duba sabbin files ɗin daya iske a saman tabir ɗinsa yana murmushi sai kace wani zararre, shi kaɗai yasan mi yake tufƙawa a zuciyarsa.

★★★★★★
Chapter 32 · 0% Book details