← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 75

Sashe 18

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da safema koda suka tashi bai zoban, harta gaƙaraci mitarta akan Shahudah da bata tashi tai sallaba tai shiru, sai kuma ta koma kan Jawaad.
Da mitar Jawaad ɗin a bakinta su baba Usman suka shigo suka sameta, bayan sun gaisheta take sanarmusu komai.
A take suka aika a kira musu Jawaad, amma sai akai rashin sa'a aka iske ya wuce aiki abinsa.
Takaicin hakan ya hanasu motsi har saida suka fara jiyo kakarin aman Shahudah daga bedroom ɗin Mama Atika.
Itace ta shiga ta isketa duƙe tanata amai cikin banɗaki, mamaki ya kamata, amma saita ajiye mamakin ta taimaketa harta gama sannan ta bata ruwa ta wanke bakinta suka fito.
Sannu taketa jera mata da tambayarta komi taci haka daga tashinta?.
A galabaice Shahudah ke faɗin, “Ni banci komaiba Hajiya, dan rabona da cin wani abu tunma jiya da yamma, bansan miyasaba kwana ukunnan kullum da amai nake farkawa da safe, narasa mike damuna”.
Tsiramata ido mama Atika tayi ba tare da ta iya cewa komaiba, tsawon wasu sakanni tana a kanta tana nazarinta, sai kuma ta fice daga ɗakin a hanzarce tare da wani irin ɗoki akan fuskarta.
Shahudah kam kanta ta maida ta kwantar barci ya kuma kwasheta.

Albishir ɗin da tsohuwa takaima ƴaƴan nata ne ya sakasu miƙewa zumbur a wani irin razane.
Kowa na ambaton mama da gaske?.
Dariyar jin daɗi tayi tana zama, “Ƴaƴannan mizaisa na muku ƙarya nikuwa, sam bakwa bina bashin rantsuwa akan wannan maganar haka take. Amma danku tabbatar a kira likita ya gwadata yanzunnan”.
Duk da sun yarda da batun mahaifiyar tasu haka suka nemo Doctor domin sake tabbatarwa a aikace.
Jikin Shahudah rijib da zazzaɓi zuwa yanzun, haka dole Mama Atika ta tasheta, tambayoyi likitan yaymata tare da bata tsinken gwaji saboda ba'a buƙatar jan lokaci.
Gwajin farko ya tabbatar akwai ciki, tuni falon ya ruɗe da wani irin murna, kowa fuskarsa a washe saɓanin ta Shahudah dake a rikice.
Ciki kuma? A wannan shekarun natane zatayi ciki? Kai da sakal wai anbama mai kaza kai, sam babu tsarin ɗaukar ciki a gareta a nan kusa, yaushema sukai auren da har tagama morarsa da za'ai batun ciki a jikinta, so ake ta ragwagwgwaɓe da wurima kenan tamkar wata matar Afirika, ina wannan shirmen bamai yuwuwa bane, dolene Jawaad yazo asan abinyi, dan bazata haifi wannan cikinba koda za'a tada yaƙin duniya na ukune.

😱😱hummm ashe akwai kallo, dan inba'a tada yakin duniya na uku ba to lallai Shahudah za'a tada na ƙarshe akanki🤣🤣, yanda naga cikin yazama burin mutane da yawa aiko yagalgalaki zasuyi harma da Fans din ƙwai cikin ƙaya😆😂.

★★★★★★★★

Ya isa ƙofar kurkukun (Jail) da abokansa uku kuma aminansa suka tsinci kansu a ciki dalilin ƙaddara, dan kuwa shekarunsu na biyu kenan a wajen bisa sharri da akai musu dan a durƙusar da Jawaad ɗin, yayi iya bakin ƙokarinsa a lokacin ganin sun kuɓuta amma sai hakan ya gagara, dankuwa ƙulline mai cike da ruɗani a ka ƙulla dan kawai a dakusheshi tunda ansan abokansa suna cikin manyan abinda ke ƙara masa ƙwazo da ƙarfin gwiwa, duk yanda yaso gano wanda ya aikata masa hakan kuma bai samu nasaraba, shiyyasa ya tattara komai ya maida hannun ALLAH, sai gashi a yanzu cikin sauƙi ALLAH ya kuɓtar dasu.
Shigarsa wajen ta saka ma'aikatan gidan yarin bashi girma na musamman, dan sunsan wanene shi da matsayinsa, tunda dama jail ɗin bana kowa da kowa bane, jami'an tsaro masu laifi kawai ake sakawa a ciki.
Bayan shigarsa Office ɗin shugaban wajen na wasu mintuna aka kammala komai, yana nan zaune aka fito dasu.
Idanu suka tsurama juna da ga shi harsu, tuni idonsa ya kaɗa yay jazur tamkar an hura barkono, jijiyoyin kansa sunyi wani irin fitowa ruɗu-ruɗu, ya miƙe ahankali yana tunkararsu tamkar yanda shima suke nufoshi cikin wani irin yanayi na kewa da farinciki, dan shekaru biyun da suka ɗauka a rufe sam an hana Jay ganinsu.
Rungume juna sukai su huɗu, dukda yanda jikinsu yake baiji ƙyamarsuba, kowanne hawaye masu raɗaɗi suna kwarara a idanunsa.
Su dai ma'aikatan wajen kallonsu kawai sukeyi.
Kusan mintuna uku suna a haka, kafin su ɗago kowanne yana ƙokarin sharema ɗan uwansa hawayensa, sai kuma suka sake rungume juna suna dariya saikace wasu zararru.
Nanma kusan sakwan arba'in suka ɗauka kafin suyi haramar fitowa ba tare da ko bakin ɗayansu ya saɓa ba wajen furtama juna magana.
Gimba dake jikin mota tsaye ya hangosu suna fitowa daga cikin Jail ɗin a yanayin da yasansu a baya, jarumai kuma aminai, sannan ƴan uwan juna masu ɗaukar kansu JINI ƊAYA.
Cike da wani irin ɗoki yake washe musu baki har kunne, lallai yau farin cikin boss ɗinsa sun dawo, yanzu sauyi zai sake zuwa a hukumarsu, hannunsa ya dunƙule waje ɗaya yana cigaba da washe bakinsa, yama kasa magana saboda tsabar farinciki.
Suka dafashi a kusan tare suna dariya suma.
Da ƙyar ya iya furta, “ALLAH mun gode maka, yau ga basawan boss sun dawo gareshi, tarkon da makiya suka kafa ya buɗe”.
Jawaad da fuskarsa babu walwala ya girgiza kai kawai ba tare da yace komaiba ya buɗe mota yana musu nuni dasu shiga.
Basu ɓata lokaciba suka bar wajen zuwa gidan Jay ɗin dake Empty babu kowa ciki, gidan yayi ƙyau sosai, gashi anguwar da yake babu yawan hayaniya.
Suna shiga gidan dukkan farin cikinsu da suka danne da kewar juna sai ya bayyana, dan sake rungume juna sukai a tare kowa na faɗo yanda yay kewar ɗan uwansa.
Tsawon lokaci suka ɗauka a haka har Gimba ya dawo da ledojin abinci ba tare da sunsan zaiyi wannan ɗawainiyarba.
Godiya sukai masa duk da kuwa yana ƙasansu, ya nuna musu hakan ba komai bane tare dajin daɗinsa na murna da sukai, ya jajanta musu da addu'ar ALLAH ya kiyaye gaba.
Wanka suka shiga su duka a mabanbanta banɗakin dake cikin gidan, sun ɗauki tsawon lokaci, dan Jawaad ma harya fice zuwa wani kiran gaggawa daya samu daga office ya barsu akan kafin ya dawo su tabbatar sunci sunsha sun huta.......

______________________
BILKEESU
______________________

.........Har dare babu labarin bilkisu a cikin anguwar, ga kuma ƴan sanda ta ko'ina an bazasu nemanta, sai kuma yaran Jazuuga dasuma ke aikinsu domin taya ƴan sandan.

Ina cikin mankarar har dare, tun ina kuka da hawaye da murya harna koma na zuciya kawai nake iyawa, hankalina bai gama tashiba sai da na farajin motsin mutane masu shigowa sallar magriba, kuma nutsuwa nayi a wajen duk da ƙarfina ya ƙare, hannuna dafe da bakina gudun kar wani mai ƙarfin ji ya iya jiyo fitar numfashina.
ALLAH ya aramin wannan lokacin har akai sallar magriba aka kammala.
Sosai ƙarfina ya gama ƙarewa, na gaji da tsaiwar, burina kawai na zauna nahutama raina, ƙafafuna sunyi nauyi tamkar ba'a jikina sukeba, gashi wasu suna a massallacin basu gama ficewa ba, sun zauna har sai anyi sallar isha'i.
Haka na cigaba da dauriya a wannan yanayi mai wahalar musaltawa har lokacin sallar isha'i yayi ya wuce, mutane sun fara barin massallacin, inda akabar tsirarun da suka koma fita ɗai-ɗai.
Wani da ya fita na ƙarshe shida abokinsa naji suna faɗin ƙarfe goma da rabi na dare, bana a hayyacina zuwa lokacin sosai, amma bayan fitarsu da wasu mintuna saina leƙo kaina cikin massalacin, babu kowa sai mutum ɗaya dake barci, da gyar na tattaro ɗan sauran ƙarfina na janye mankarar na fito, tafiya nake tamkar bugaggiyar da tayi mankas da kayan maye, ni kaina bansan a ina nake jefa ƙafaba, tafiya kawai nake tamkar bahagon raƙumi.
Ƙwaƙwalwar kaina sam bata aiki da zuciyata, ni kaina na fara manta wacece ni?.
Ƴan sanda biyu dana hango gabana suna tunkaroni yasani firgicewa, nai saurin komawa baya na maƙale jikin bangon wani gida, ta gabana sukazo zasu wuce suna magana wadda na fahimci akainace.
Ɗaya a cikinsu ke faɗin, “Oga kana ganin Alhajin nan zai bamu maƙudan kuɗinnan kuwa daya faɗa inhar aikinnan ya kammala yanda akeso?”.
“Hhhh bayarwa kuwa zaiyi ɗan sambo, bakaga yanda yake a firgiceba, bashi da burin daya wuce akama yarinyar, sannan ɗansa ya kuɓta, shiyyasa nima nace muyi ƙaimi, dan inada tabbacin tana cikin anguwarnan bata fitaba, sai dai idan wani munafikinne ya bata mafaka a gidansa”.
“Shegun ba, ai zamu kamatane, idan kuma har kuɗinan suka tabbata lallai lokacin ƙara aurena yayi kenan, dan wlhy zama da kubra kawai nafi ƙarfinsa”.
“Hhhhhhh!! Wato ɗan sambo shiyyasa nake sonka wlhy, kai abokin neman arziƙine, idan kana abu sainaji daɗi saboda lallai kana kan tsarina, saikace uwa ɗayace ta haifemu”.
Dariya suka kwashe da ita tamkar wasu mahaukata su duka biyun, da wannan mahaukaciyar dariyar suka wuceni batare da ɗayansu ya hankalta dani ba.
Numfashi na sauke cikin gajiyawa, sai da na tabbatar sun ɓacema ganina sannan nacigaba da tafiya ina zirar da hawaye, wace irin ƙasa muke da ita hakane? Masu bada tsaro da kariya sune suka koma masu ɓata tsaro da zalunci?.
Ta yaya har muke tunanin samun shugabanni adalai bayan muma talakawan azzaluman junane?.
Nacigaba da tafiya ba tare da namasan ina nakeba, abinda na sani kawai shine nayi nesa da anguwarmu kam tabbas, sannan ina buƙatar zama na huta, sai dai tsoro da fargabar kar azo a kamani sun hanani damar samun wajen yada zango.
Chapter 18 · 0% Book details