← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 75

Sashe 17

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani barcine mai daɗi ya sacesa take a wajen, gashi har lokacin ruwa ake zabgawa.
Kamar kullum dai yauma dai mafarkinsa akan mahaifiyarsa yake, hakanne ya sakashi farkawa a firgice, sai da ya karanto addu'a kafin ya miƙe zaune sosai hannunsa dafe da kansa.
Barcin nasama bawani nisa yayba, dan bai wuce mintuna ashirinba.
Dukda abinda ke nuƙurƙusar ransa bai barsa yay tasiriba tamkar yanda ya saba, miƙewa yay yanata sauke ajiyar zuciya a jere-jare, falonsa ya fito, inda ya hango kulolin abinci saman D/table, takawa yay ahankali zuwa garesu, dan ɗan barcin saiya saukar masa da kasala, ga kuma sanyin ruwa da garin ya ɗauka.
Kulolin yabi ɗai-ɗai yana buɗewa, yay ɗan guntun murmushi a kasalance, dan kuwa abincin da yafi sone a rayuwarsa, wato Masa, tayi ƙyau suɓu-suɓu, ga miyar taushe mai tsafta da tasamu ingantacciyar dahuwa.
Sauka yay ƙasa inda ya ɗakko filet dama duk abinda zai buƙata ya dawo.
Yana zama a kujerar dani ɗin Shahudah na fitowa daga ɗakinta saboda motsinsa da taji.
Duk da yasan itace sai yay biris ya cigaba da hidimar zuba masar sa,
Fuskarta da alamar damuwa taja kujera ta zauna kusa dashi gab, ta ɗora kanta jikin damtsen hannunsa ta kwantar tana lumshe idanu, tare da maƙalesa da hannayenta duka.
Nanma bai motsaba, bai kuma kalleta ba, saima laumar masa da ya fara kaiwa bakinsa cikin zaƙuwa.
Taunawa yakeyi a hankali yana wani luuu-luuu da idanu, ɗari bisa ɗari daɗinta yakai a yabama mai hidimar girkata.
Shahudah ta ɗago kanta tana kallonsa da mamaki, sai faman ƙyaɓe baki take tana wani yamutse fuska saikace taga kashi, itafa sosai kyankyamin abincin gargajiyar nan takeyi lokuta da dama, ji wata irin miya dan ALLAH......
“Wai dan ALLAH bb baka tsoron irin waɗanan abincin su sakaka yin nauyi da yawa?”.
Banza yay mata kamar baijiba.
Ta daki damtsen hannunsa kaɗan tana buga ƙafafu da turo baki cikin shagwaɓa.
“Kai kaji tsiyarka riƙon masifa, ba nazo na baka haƙuri ba amma dan wula ƙanci ka kulle ƙofarka dan karna shigo”.
Nanma ɗin banza yay mata.
Tagumi tayi hannu biyu ta zuba masa idanu tana hawaye.
Yi yay tamkar baisan tanaiba, yaci abincinsa yay nak, hannunsa ya wanke cikin ruwan daya ajiye, ya ciri tissue yana goge bakinsa da hannunsa. Duk dai Shahudah na kallonsa tana cigaba da kukanta.
Miƙewa yay zai bar wajen ta miƙe itama a zafafe, sai ta faɗa bayansa ta zagayo hannayenta a cikinsa ta sakar masa kuka mai sauti.
Cak ya tsaya bai motsaba, kusan mintuna biyu suna a haka, idonsa a lumshe yana sauraren sautin kukanta da saukar hawayenta a gadon bayansa.
Hannu yasa ya cire nata dake akan cikinsa, ya tureta daga jikinsa yay gaba zai bar waje.
Kuma kamo hannunsa tai da sauri tana fadin, “Haba bb, miyasa kakeson wulaƙantani ne? Kodan kaga inasonka da yawa haka? Nasan bakason a tara maka mutane a gida, amma nima ka dubi uzirina mana, kaji tausayin kaɗaicin da nake zama a ciki, ka hanani fita, dukda nasan ƴancinane na fita inda nakeso a lokacin da nakeso, amma nai haƙuri saboda kayi farin ciki, ya ka ke so na rayu dan ALLAH? ban saba da wannan rayuwar takuba, rayuwar ƴanci na taso a cik.......”
Yanda ya juyo a zafafe ne ya saka bakin Shahudah rufewa akan dole.
A tsawace tare da matsota kamar zai hadiyeta yace, “Ƴanci ko jahilci? Hudah ke wace irin daƙiƙiyace ne wai? Miyasa fitilar ƙwaƙwalwarki bata haska miki hanyar da zaki sanya ƙafa? Wlhy nayi nadamar aurenki, nadama irin wacce bama zan yafema kainaba, wawuya kawai mai koyi da toshewar basirar jahilai”.
Shahudah dake tsaye tamkar wata gunki ta bisa da kallo harya shige ɗakinsa, duk da bagama fahimtar kalaman nasa tayiba sun girgizata, dan ita hausarma bakomai take ganewa a cikiba saboda ba yimusi akeba, ɗan dawowar tasun nanmane take ƙara fahimtar wasu abubuwan🤦🏻‍♀️(kaga turawa😆😝 ).
Hawayen da suka sakko mata a farar fatarta ta goge, duk da kayan dake jikinta basu dace wani ya ganta da suba, haka ta fice daga sashen nasu, ga yayyafi har yanzu anayi ƙaɗan-kaɗan.
Da gudu ta isa sashen tsohuwa Mama atika, (wato kakarta data haifi mamanta).

Zuciyar Jawaad a wuya take sosai, gaba ɗaya Shahudah ta sake ruguza masa dukkan farincikin da Ummansa ta bashi tare da ƴar uwarsa Batool.
Haka yay shirin barci yanata sauke ajiyar zuciya, yanayin shafa'i da wutiri ya haye gado yay kwanciyarsa.
Amma sai barcin yaƙi zuwa sam, haka yayta tunane-tunane har kusan ƙarfe uku, kafin barci ɓarawo ya sacesa.

★★★★★★

Da safe haka ya tashi babu walwala, yana dawowa sallar asuba yay shiri ya fita wajen aiki batare da ya yarda kowa daga jama'ar gidan ya fito ya sameshi ba.

Koda suka iso gimba ya buɗe masa motar ya fito.
Da Qaseem ya fara cin karo, ya tara zaratan matasan ƴan sanda yana musu magana, da alama dai ya haɗa rundunane.
Wani mugun murmushi yayma Jawaad yana kanne masa ido ɗaya.
Waishi a haukarsa ai ya karɓi damar da Jawaad ɗin ke takama da ita.
Shima Jawaad ɗin murmushi yay masa, tare da sumbatar yatsun hannunsa biyu ya nunama Qaseem alamar saƙo.
Saikuma abin ya soki zuciyar Qaseem, tuni fara'ar fuskarsa ta bace ya koma bin bayan Jawaad da wani mugun kallo.
Baima san yanayiba, dan tuni Jawaad yama shige sashen da zai kaisa Office ɗinsa.
Yana zama da saƙo yafara cin karo.
Zumbur ya miƙe ya fice tamkar zai tashi sama dan rawar jiki.
A ƙofar Office ɗinsa yaci karo da Qaseem Ali, kallon mamaki Jawaad ke binsa dashi, amma baice komaiba.
Qaseem yay wata dariya yana watsa hannaye gefe,
“Yaya dai gwarzon ma'aikaci, yaya kaga wasan nawa? Ka shiga ruɗani ko? Aikin da kake takamar dashi an amshe cikin lokaci ƙankani an bani, nine zan jagorancesa yanzu, dama iyakar izzar taka kenan?”.
Murmushi Jawaad yayi cikin ƙokarin katse Qaseem, buso iska yay daga bakinsa yana takowa cikin tsantsar takama da izzar jarumta irinta zaratan matasan da jini ke yawo ta kowace kafar jikinsu zuwa gaban Qaseem ɗin, ya dafa kafaɗarsa da hannu,
“Na yarda kayi nasara my dear, ni kuma na faɗi, sai dai ina baka shawara akan ka kula kafin wani ya kula da kai, sannan ba'a cika baki da nasara kafin a nemota, nasara anan take Qaseem, (ya faɗa yana nuna saitin zuciyar Qaseem da ɗanyatsa), ina baka girma dalilin kaiɗin yayan matatane kuma ɗan uwana, sannan ogana a wajen aiki, karka bari zuciyata ta fara ƙoƙarin yin fito na fito da kai ko maida murtani. Nabarka lafiya, tare da fatan nasara jarumin ma'aikaci”.
Ya ƙare maganar da salute ɗinsa, tare da zagayesa ya wuce.

Harya shiga mota suka fice daga station ɗin Qaseem na tsaye kamar bishiyar giginya, zuciyarsa na tafarfasa da ƙuna, tare dajin tsanar Jawaad mai tananin gaske..................✍🏻

https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q

*MANHA HAUSA NOVEL'S* takuce, maza garzaya domin bada gudunmawarka, danna Subscribing domin nuna ƙaunarka garemu🤩, kuyi shiri na musamman domin samun daɗaɗan shirye-shiryenmu tare da nagartattun labaran novel's masu daɗi da ma'ana nan da lokaci ƙanƙani, MANHA HAUSA NOVEL'S ta shirya tsaf domin baku farin ciki insha ALLAHU, ku garzaya kada ƙuda ya rigaku😂, Bilynku ma har taje tayi subscribing tun farar safiya, goyon bayanku shine ƙwarin gwiwarmu🥰🥰😉🤩.

MANHA HAUSA NOVEL'S
(Ƙyautar ALLAH).

Ku isa da hanzari domin samun ƙyautar kuma, dan ALLAH a danna subscribing🙏🏻.

Ga link ɗinnan a sama

https://youtu.be/YHEmwk9ovP0

littafin *ƘARAYAR ARZEEƘI!!*

A Odiyo, maza garzaya MANHA HAUSA NOVELS domin saurare, danna subscribing domin nuna soyayyarka garemu🥰🥰😻🤳🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu.😭🙏🏻*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na goma sha ɗaya_
*______________________________________*

.............Mama Atika tsohuwa mai ran ƙarfe dake zaune a falonta tana jan cazbaha ta ɗago tana kallon Shahudah data shigo a guje kamar an korota, ga jikinta harya fara jiƙewa da yayyafin da har yanzu akeyi, sai da ta ƙarema guntun wandon jikin Shahudah da bai gama zuwa koda rabin cinyartaba kallo da riga mara hannu, wadda inda zata ɗaga hannu sai anga cibiyarta.
Janye idanunta tayi daga barin kallonta sannan ta girgiza kanta.
Ƙarasowa Shahudah tayi ta zauna a jikinta tana kumbura fuska ga hawaye na kwarara.
Mama Atika ta shafa addu'a tare da maida hankalinta ga Shahudah.
“Kekuwa Sabirah miya jamiki fitowa a haka cikin wannan ruwan? Ko ɗankwali ma babu fa a kanki, baza dai kibar wannan shigar ta bayyana jikinki ba ko?”.
“Ni ki daina cemin Sabirah, idan bazakice Shahudah ba basai kin kira sunanaba, Wlhy hajiya nagaji da abinda Jawaad kemin a gidansa, ni gaskiya ku kirasa kuyi masa faɗa”.
Mama Atika tace, “Hummm, yauma tsiyar kuka sakeyi kenan? Waishi wannan yaron wane irine? Ni abindama ke ƙaramin takaici dashi kokin kawo ƙarar tasa an kirasa sai yace shi baki masa komaiba, narasa irin wannan rikitaccen zama naku”.
Kuma fashewa da kukan shagwaɓa Shahudah tayi, sai kuma lafewa jikin tsohuwar takeyi.
“K yanzu yasan kin fitone?”.
Mama Atika ta tambayi Shahudah.
“Ni ban sani masaba, dan fitowata kawai nayi bayan yamin wulaƙancin”.
“Hummm, to shikenan, yanzu tashi ki koma, da safen zansa iyayenku su nemeku”.
“Ni dai anan zan kwana, dan inason ya gane kuransa yau”..
Murmushi irin na girma mama Atika tayi tana gyara zama, “Shikenan, tashi kije ki sauya waɗanan shiɗanun kayan ki kwanta muga idan zai biyoki, idan bai zoba ai iyayenki zasuzo gaisheni da Asuba zan sakasu kiransa ayi zama yau, dan bazan yarda da irin wannan halin na wulaƙanciba, sai dai yasan mai yuwuwa”.
Jin hakan da Shahudah tayi saiya sake kai kanta sama, ta shige bedroom din ƴar tsohuwar da aka narkama dukiya ta kwanta abunta.

Tun mama Atika na zuba idon ganin ko Jawaad zai shigo a daren harta fidda, dan har tagama cin abinci da duk abinda ta saba yi kafin ta kwanta, har lokacin kuma babu Jawaad babu labarin.
Chapter 17 · 0% Book details