← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 75

Sashe 38

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

...........Guri Jawaad ya samu yay fakin nesa da gidan Alhaji kokino, ya ɗauki ƙaramar wayarsa yay kiran Rose, bugu biyu ta ɗaga.
Kafin yace wani abu tai saurin faɗin, “Sir komai ya tafi dai-dai, yanzu haka ina ƙyautata zaton kowane lokaci zata iya tahowa”.
“Yayi, yanzu haka ina ƙofar gidansu, zankira su Aliyu suzo da ƙawar tata, duk yanda za'ai karki bari tazo ta sameki a wajen koda ta rigasu zuwa”.
“Okey sir”
Rose ta faɗa cikin girmamawa.
Wayar ya katse, ya tada motar ya ƙarasa ƙaton gate ɗin gidan Alhaji kokino.
Horn yayi, babu ɓata lokaci baba mai gadi ya buɗe dan yasan da zuwansa, yay fakin motar ya fito, a kuma dai-dai wanna lokacinne Hajiya Usaina ta fito kamar a rikice, motarta da Jawaad ya kare ta nufa, sai da ta zira key zata buɗe ta juyo da nufin yima baba maigadi magana ya buɗe mata gate idonta ya sauka akan motar Jawaad, yanayin da take cikine ya hanata fahimtar motar bata gidan bace ba.
Ranta a ɓace ta shiga kwala kiran “Baba Dauda! Baba dauda!!”
Jikin Baba mai gadi na rawa ya rugo zuwa gareta yana amsawa da “Na'am hajiya, afuwa naɗan zagaya banɗakine wlhy”.
Batako sauraresa ba ta nuna motar Jawaad, “Uban waye yay fakin mota a gurin nan? Bayan ansan ko yaushe zan iya fita tunda inada mara lafiya a asibiti”.
“Kiyi haƙuri hajiya baƙone yanzu kuma ya shigo shima” ‘Baba yay maganar yana nunamata Jawaad dake tsaye jikin motar yana waya hankalinsa kwance tamkar baisan mi sukeyiba, nanko dukkan hankalinsa na kansu’.
Kaɗan ya rage key ɗin motar data zare daga jikin motar ya faɗi, tai saurin damƙesa dan ba ƙaramin razana tai da ganin Jawaad ɗinba, fasa buɗe motar tayi ta nufo inda Jawaad yake tana ma baba maigadi alamar ya tashi da hannu.
Jawaad ya janye wayar daga kunnensa yana maida hankalinsa gareta, cikin harɗewar harshe tace, “Yallaɓai lafiya kuwa a daren nan? Ko anga Alhaji ne?”.
Fuskarsa ya kauda daga gareta tamkar baiji mi taceba, ya tura wayar tasa a aljihu yana komawa jikin motarsa ya jingina, cike da nutsuwa ya maida hankalinsa gareta, “Nazone inason magana da ɗaya a cikinku, ke ko Hajiya babba”.
“To Yallaɓai nidai amin afuwa jikin mamana ne ya motsa, shine aka kirani asibiti”.
“Okey babu damuwa, bara na bari sai da safe na dawo, ALLAH ya bata lafiya”.
“Amin ngd” tai maganar tana barin wajen cike da sauri, dukta rikice, da alama kuma ganin Jawaad ne ya kawo hakan. Cikin gida ta koma ba tare da tasan mizatayo ba kuma.
Murmushi Jay yayi yana ɗauke ido daga kanta, ya maida dubansa ga baba maigadi yana faɗin, “Buɗemin gate, ina fatan komai done?”.
“Komai dai-dai ƴallaɓai, ALLAH ya ƙara nasara”.
Murmushi Jawaad yay masa, ya buɗe motar ya shige ya bar gidan saboda baba ya buɗe masa gate ɗin.
Yana ƙoƙarin harba motar kan titi yana kiran waya, ya ajiyeta a saman cinyarsa bayan ya saka a hansfree.
“Hello Hafiz!, kuyi maza mu haɗu acan ɗin, idan kun rigani zuwa saiku jirani, inaso saina fara ajiyeshi kafin ku sauketa kuma, saboda tsarin yayi dai-dai”.
“Okey Boss” Hafez ya amsa daga can yana gimtse wayar, zuwa yanzu kam ya fahimci mi Jawaad ke shirinyi, dan haka ya kalli su Jabeer da suma sunji komai saboda a hansfree ya saka.
Dariya sukayi gaba ɗaya, dan sun fahimci inda aikin ya dosa yanzu kam.
Chapter 38 · 0% Book details