← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 75

Sashe 3

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ring ɗin wayarsa ne ya farkar da shi da ga nannauyan barcin da yay nisa a ciki, ya janye bargon da ga kansa da ƙyar tare da miƙa hannu saman dirowan gefen gadon ya ɗauki ƙaramar wayarsa da ke vibration. Ba tare da ya duba wanene ba ya ɗaga kawai ya saka a kunne yana sake maida idanunsa ya lumshe. Tsawon seconds arba'in yana sauraren mai maganar da ga can, kafin ya furta “Ok sir” cikin nutsatstsiyar muryarsa da ke gauraye da barci. Ƙarƙashin filon ya tura wayar yana sake juya kwanciyarsa hankali kwance, sai faman ɓata fuska yake na jin takaicin katse masa barci da akayi. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya ture bargon yana jan dogon tsaki, ƙaramin agogon dake gefen dirowan gadon ya kalla, ⏰11:29am, numfashi ya sauke a hankali dan sam baiyi tunanin barcin nasa yayi dogon zango haka ba, tashi yay ya sauka daga gadon gaba ɗaya.
Sosai ƙyanƙyamin bayin nan yakeyi, dan yakai kusan kwana huɗu kenan babu wanki, tun randa Batool tazo bai sake ganin gyara ba saboda tsabagen lalacin matar gidan.
A ɗarare yay abinda zaiyi ya fito ba tare da ya sake wanka ba, baƙar jallabiyarsa mai dogon hannu ya ɗauka ya zura kawai da silifas ya fice zuwa ƙasa.

Sai sha ɗaya saura Shahudah ta tashi a sabon barcin da ta sake komawa, sai faman ɓata fuska take tamkar ance ta tashi dole ne, rigar barcinta ta zame tare da sakinta a tsakkiyar ɗakin tai tsaye tsirara da ga ita sai pant wanda shi da babu duk ɗaya, hankalinta kwance ko tunanin bayan jinsinta akwai na aljanu da ido baya ganinsu a ɗakin batai ba, a haka ta nufi bathroom.
Tsawon lokaci ta ɗauka a ciki kafin ta fito ɗaure da wani mitsitsin tawul kalar ruwan hoda, shima tana zuwa gaban mirror ta sakeshi ƙasa, a haka ta shafa mai kafin ta buɗe Wadrobe ta ɗauki doguwar riga ɓaƙa ta saka, tare da naɗa ɗankwalin rigar ta ɗau abin salla ta shinfiɗa.

🤥tsantsar mamaki da al'ajab sun rufeni ganin sai yanzune Shahudah zatai sallar asuba, sha ɗaya da kusan ƙwata🤦🏻‍♀️.

Ina nan zaune ganin ikon ALLAH harta idar da sallar tata a cikin ƙanƙanin lokacin da bazai gaza mintuna uku ba. Rigar ta sake cirewa ta ajiye, ta ɗauki tawul ɗinta ta sake ɗaurawa tare da jan stool ta zauna aka fara tsara ƙwalliya ta garari.

Kai tsaye ɗakin Shahudah Jawaad ya shiga, juyowa tai ta ɗan kallesa ta ɗauke ido ita a dole fushi takeyi da shi.
Shima sai da ya fara ƙarema ɗakin kallo kafin ya kai dubansa gareta, kallon kusan seconds goma yay mata sannan ya cigaba da takowa cikin ɗakin, jikin bangon da mirror yake ya jingina tare da harɗe ƙafafunsa waje guda ya tura duka hannunsa a aljihun jallabiyar.
Tsayuwar tasa sai ya zam tamkar sun fuskanci junane shi da Shahudah, hakan yasa ta sake ƙwaɓe face ɗinta tana cigaba da zana kwalliyarta.
Tsawon mintuna biyu suna a haka, babu wanda ya cema ɗan uwansa ci kanka, sai zuwa can Shahudah ta ɗago manyan idanunta da gashin ya sake jin maskara ya miƙe gazar-gazar fiye da da ta kallesa, “Nikam karka cinyeni dan ALLAH bb”.
Idanunsa ya janye a kanta yana sakin guntun murmushi da ya saka kumatunsa loɓawa, itama Shahudah sai tayi murmushin.
“Breakfast fa?” yay maganar yana sake maido kallonsa gareta.
Sosai ta sake zuba masa idanunta tana narke fuska, sai dai batace komaiba.
Hannayensa ya zare daga aljihu ya maida a ƙirjinsa ya harɗe, “Yanzu nan Hudah kina ganin wannan rayuwar itace ta dace da matar aure ta hausa fulani? Wata bakwai kawai da aurenmu amma matsaloli sunzo sun mana ɗaurin goro a cikin gida, wanda duk kece sanadinsu, shin ke wai bazaki taɓa canjawa bane?!.....” ‘Ya ƙare maganar a tsawace’.
Razana tayi matuƙa, dan haka ta zabura tana jan jikinta baya tare da waro manyan idanunta waje, “Wai ni bb ya kake so in maka ne? Kaifa nace a ɗakko kuku da wanda zaike mana gyara amma kace baka yarda ba, ta yaya kake tunanin zan iya aikin gyaran wannan ƙaton gidanne saboda ALLAH, kum....”
Haɗiye sauran maganar tata tayi tana ƙunƙuni saboda wani ɗan iskan kallo da yake mata, wanda ta tabbata yafara harzuƙa, idan ko ta bari ya kai ƙarshe zai iya ɓarota a kujerar ya haɗa kanta da mirror.
“Shahudah baki kai matsayin sakani yin abinda ban niyyaba, dan bazan taɓa kawo wani ƙaton banza gidana ba da sunan ma'aikaci, ki kama kanki kafin na raba shi da wuyanki a gidannan wlhy, stupid girl kawai”. Ya ƙare maganar da juyawa zai fita.
Cikin ƙunƙuni Shahudah ke faɗin, “Karka kawo ɗin, kata zama a gida tamkar tirken akuyiyin ƙauye kuwa, dan nikam ba ƴar wahala bace, kake wani cewa kamar ba matar hausa fulani ba, ALLAH ya rabani zama irinsu waɗannan kidahuman da basusan ko yanda zama su gyara jikinsu ba balle su san miye rayuwa, da ana canja yare ma da tuni na canja nawa anbar dangantani da wasu hausa fulani can mtsowww.

🤔tab, babbar magana, Shahudah anya kinada man kai kuwa? Matan hausawan ne bamusan abinda mukeba😨🤦🏻‍♀️? Rigiji gabji☹️.

Sarai Jawaad yaji abinda Shahudah ta faɗa, amma sai ya fice ko waiwayota baiyiba, bedroom ɗinsa ya koma ransa duk a jagule, ya ɗau babbar wayarsa da ke a kashe ya kunna, wata Number ya lalubo tare da danna mata kira, bugu biyu aka ɗauka.
Sama-sama sukai gaisuwa da wadda ya ambaci sunanta da Hibba, kafin yace, “Cikin yarannan wace a gida?”.
Bansan mi aka ce masa da ga canba, ya dai sake faɗin “turomin ita” kawai ya yanke wayar ya ajiye.
Tsaki yaja yana jingina da fuskar gadon tare da lumshe idanunsa ya afka duniyar tunani............✍🏻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*🧺

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_SADAUKARWA:_*
_Aunty Fareeda Gachi_
_Aunty Rahma A-Majeed_

*_Wattpad_*:- _BilynAbdull😉_

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na uku_
*______________________________________*

..........Zaman duniya da kayan cikinta buƙatar kowacce, amma waɗanda duniya ke buƙata da amfanuwa da kayan cikinta mutanene ƙalilan. A lokacin da wasu mutane ke bushasha da wani yanki na jin daɗin cikinta wasunsu kuka suke da kwankwaɗar ɗacin cikinta.
Yayinda idanun wasu ya bushe da ga kwaranyar ruwa mai amsa sunan hawaye, a lokacinne ijiyar wasu ke ambaliyar zubarwa da buƙatar abin gogewa koda ace ruwan hawayen bazai dakata daga malala ba.
Zuciyoyi duk iri ɗayane a suna, amma a aiyuka kowa da irin tasa. In dai zuciya zata kasance mabanbanta a ƙirazan mutane, to lallai dolene launin halayya da ɗabi'unsu ma ya banbanta. Sai dai wanda ya halicci duniyar da kayan cikinta, ya fika sanin miyasa ya banbanta ma'abota mu'amulantar ta da shawagi a cikinta harma da gudun zukatansu.
Kamar yanda duk ilimin ɗan adam bai isa ƙayyade numfashin da ke fita daga huhunsa zuwa maƙogwaro ya fita ta hanci ba, to lallai babu mai ilimin ƙa'idance ko banbance yawan jinsin ƙabilu da mutanen dake danƙare da duniyar nan sai wanda ya halicceta. A lokacin da fankama da tinƙahonka ke kwarzanta abincin tukunyar gidanka, da zaka leƙa ta gidan wani sai kaga ta fita abin kallo da kayan alfarma masu armashi.
Sai dai duk wannan ba shi bane tushen zancen, ba kuma shi bane abin dubi da hange ko burin riska, tsarin shine waiwaya can bayan bayanka ka hango waɗanda ko tukunyar ɗorawar basu da ita balle tunanin hura wutar da zata dafa musu.
Wani tun haihuwarsa ALLAH ya azurta tushensa ko zuri'arsa da rahamar fitowa cikin gingimemen hasken da ko baka mallaki komai ba a duniya sai shi to lallai ya gama maka komai, domin ya baka abinda ya fi komai tsadar tsada a cikin alfarmarsa. Sai dai abin mamaki da al'ajabi sai ka samu mafi yawan masu wannan damar sunyi wasarere da ita tare da mata riƙon sakainar kashi suna hange da gudun kamo wasu al'adu da ke da alaƙa da kishiyar nasu.
Zancen nawa a bayyane yake, sai dai fa fahimtarsa ba kowace kwanyace hasashenta zai kai canba, ba kuma toshewar basira ce zata kawo rashin fahimtar ba, sam ko kusa ba hakan bane, ɗunbin abin tarawa ne kawai kema ƙwaƙwalen jama'a yawa su gaza warware wani ƙullun igiyar a jikin gugar da takai kimanin dogon zamani ana cuɗanya da ita a rijiyar mai bakandamiyar alfarmar ruwa buƙatar kowa.
Shi wancan dama ya samu, amma rashin fahimtar hanyar da yake jefa ƙafa ta sakashi gaza fahimtar akwai waninsa da ke da buƙatar koda kwatankwacin tasa damarce shima ya shigo a dama dashi.
Gashi dai a cikin duniyar irinta wadda ke da damar a tafin hannu, ga kuma gangar jiki da fitar numfashi duk ALLAH ya haliccesa da ita shima, sai dai sam ba ƙofa ɗaya ya ke shiga da fita tsakaninsa da mai damar a cikin duniyar ba. Hakan yasa yake kallon tasa duniyar da ban a cikin duniya, ba dan baya ci ko sha ba kamar kai, hatta barci da kake domin hutu da dariyar farin ciki duk ALLAH shima ya azurtashi dasu, abin lurar shine kai duniyar rungumeta kayi tsam, itama ta tallafeka tare da sake cusaka jikinta kuna kwasar ɗumin juna saboda tsantsar buƙatarka da takeyi, Shiko waninka rakaɓe yake a jikinta tamkar hawainiyar da ke ɗauke da ciki ta ke jiran ranar haihuwa.
Bara dai mu ajiye duk wani dogon zance mu tsunduma cikin labarin ko mai karatu zaifi fahimtar gonar audigar da nake masa nuni da ita mai ɗauke da buɗaɗɗiyar kaɗa da gwaiduwarta ta fashe sumfut a filin gona.
Chapter 3 · 0% Book details