← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 75

Sashe 39

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Daga jikin kamfanin ta baya yay fakin motar, ya fito a ɗan hanzarce bayan ya saka baƙar safar hannu a hannunsa, bayan motar ya buɗe bayan ya wawwaiga babu alamar mutun ta ko ina, yakai hannu ya jawo mutum a seat ɗin baya da ƙyar, dan babu laifi yanada jiki, kuma da alama a sume yake ma. Da ƙyar ya iya saukeshi ƙasa, sai hakki yake, ya sake ɗagashi da ƙyar zuwa wani ƙaramar baca ta kwano dake wajen ya ajiye saman kujera, igiya ya saka ya ɗaɗɗauresa kafin ya zaro allura a aljihun wandonsa yay masa a hannu, bai jira komaiba ya zare abinda suka rufe masa fuska ya fice da hanzari yayo waje.
Mota ya koma, da babaya yajata yaɗan koma nesa da wajen sannan ya kashe ya sake fitowa, wayar dake hannunsa ya ɗora a kunne yana fadin, “Zaku iya kaita”.
Bai jira misu Aliyu zasu ceba ya yanke wayar ya koma kiran Rose wadda tana daga can ɗan nesa da kamfanin itama, tana ɗagawa yace, “Kin ajiye wayar da kika kiratane a bacar?”.
“Yes boss, tun ɗazun ma”.
“Okey kizam cikin shiri, dan bayan awa ɗaya kacal zamu far musu kafin suyi tunanin kashesa”.
“Angama boss”.
Katse kiran yay yana lumshe jajayen idanunsa tare da dafe kai, babu abinda yake buƙata sai hutu, dan a matuƙar jigace yake.
A haka Su Jabeer suka ƙaraso inda yake, dan Aliyu ne kawai yakai matar cikin bacar da Jawaad ya ajiye Alhaji kokino.
Fitar Aliyu da kamar mintuna biyu Alhaji Kokino ya farfaɗo saboda Allurar da Jawaad yay masa, mutsu-mutsu ya fara yana ƙoƙarin buɗe idanu da ƙyar, hakan ya saka matar da Aliyu ya kawo miƙewa jiki na rawa ta nufesa, dan itama tunda Aliyun ya jefota kanta a juye yake bata fahimtar komai, ta rasa dalilinsu na aikata hakan.
Da yake kuma akwai duhu sai bata san ita da waye bane a wajen, da lalube ta isa inda yake, tana ɗora hannunsa jikinsa wayarta da Rose ta ajiye a bacar ta hau ring.
Cikin tsananin firgita ta juya ta kalli wajen, inda shima Alhaji Kokino ya sauke wani nannauyan numfashi, wayar ta nufa dan ɗan hasken screen ɗin ya haska bacar kaɗan, mamaki ya kamata ganin wayartacema ashe, kuma Hajiya Usaina ce ma ke kira, kasa ɗagawa tai harta tsinke.
Aka sake kira, cikin rashin sanin abinyi ta ɗaga, daga can Hajiya Usaina amaryar Alhaji kokino tace, “Lamcy gani a wajen kamfanin, ke kina ta inane?”.
Sosai Lamcy ta zaro idanu waje, amma sai cikin rawar baki ta amsa da cewa, “Ki duba akwai baca ta kwanon langa-langa daga gefen gabas, sai dai karkizo da mota Usaina, wannan lamarin akwai lauje cikin naɗi ba shirinmu bane”.
Katse kiran Hajiya Usaina tayi, dan tafi buƙatar su karasa ga Lamcy komaima sayi acan, fita sukai daga motar itada Abdul ƙanin Alhaji kokinon, dan tare sukazo, kuma yaji komai da Lamcy ta faɗa.
A baca kuwa ɗunbin mamaki da al'ajab ne ya kama Alhaji kokino saboda ganin Lamcy aminiyar matarsa Uswina, ga kuma furucin datai a waya, wanda ya tabbatar masa cewar da Usainar tai waya, “To minene shirin nasu?” yay tambayar a zuciyarsa.
Kafin ya samo amsa ne Abdul da Usaina suka shigo cikin bacar.
Gaba ɗaya sai tunanin Alhaji kokino ya sake birkicewa, ya kafe ɗan uwan nasa da kallo yana faɗin, “Abdul!” sai dai muryar tasa bata fita sosai.
Dariya Abdul ya kwashe da ita yana maida hankalinsa kan Lamcy dake ƙokarin musu bayanin wannan fa sam ba shirinsu bane, karsu ce zasuyi wani yunƙuri a zagaye suke.
Saurin dakatar da ita Abdul yayi da faɗin, “K dalla malama a zagayenwa? Kefa kika kiramu kika kuma sanar mana komai, ni yanzu babuma maganar ɓata lokaci anan, mu aikashi kawai, dan yanzu ƙarfe biyu saura, ya kamata ace nanda uku mun kammala komai munbar wajennan” ya ƙare maganar yana buɗe jakkar da sukazo da ita.
Duk yanda Lamcy taso su fahimceta hakan ya gagara, sai ma ƙoƙarin saka Alhaji kokino suke akan dole yana saka musu hannu a takardun dake cikin jakkar, waɗanda duk na kamfanoninsa ne da kaddarorinsa dake ƙasashe daban-daban harda na nan ƙasar.
Haushi ya kume zuciyar Lamcy, dan ta kula gaba ɗaya kawunan su hajiya Usaina a toshe suke, da ƙarfi ta hankaɗe Abdul daya kama hannun yayan nasa yana sakashi saka hannun dolen.
Kallonta yay da mamaki mai haɗe da ɓacin rai, “Wai ke mike damunki ne? Kokinsha wani abu dayafi ƙarfin kankine?.......”
“Ba nice banda hankaliba Abdul, kune baku da hankali, to idanma barci kuke ku farka wannan shirin duk wasune da nima ban saniba suka tsarashi!!!”.
Yanda tai maganar da cikakkaiyar gaskiyane ya sakasu kallonta su duka, amma sai hajiya Usaina tai tsaki kuma, “Lamcy karki kawo mana wani ruɗani anan, indai akan maganar abinda kikace za'a bakinne munji zamu baki, ke ni harma wani kaso zan ƙara miki a cikin nawa, ai burinmu ya gama cika, dan yau dai ta Alhaji ta ƙare, kudin da muketa wahalar gadi tsahon shekara shidda gasu komai ya dawo hannunmu, nanda sati ɗaya sunayenmu zasu fito cikin manya-manyan masu arziƙin duniya, hhhhhhhhh!!, sai ni Usaina ɗiyar malam garba, mace ta farko mai arziƙin da babu kwatankwacinsa a wannan yanki, Abdul ka kawoma duniyata haske dalilin buɗamin hanyar auren ɗan uwanka, wanda toshewar basira ke sakashi kallon sonsa nake, besan ina cikin waɗanda zasu zamo ƙatshen rayuwarsa bane, hhhhhhhhhh!!!!!!”.
Ta sake kwashe da wata mahaukaciyar dariya Abdul na tayata, hannu yasa ya fisgota ta faɗo jikinsa, a gaban idon Alhaji kokino dake ɗaure suka hau sumbatar juna tare da yamutsa kansu.
Hawaye masu zafi ne suka wanke fuskar Alhaji kokino, ya duƙar da kansa domin daina kallonsu, wuƙa Abdul ya zaro a aljihunsa, babu wanda ya lura ya sokama Lamcy dake ƙokarin jan hannun Hajiya Usaina, so take ta sake fahimtar dasu ko zasu fahimta, idan sunƙi ta gudu itadai ko ranta ta tsira dashi idanma babu dukiyar.
Ƙara ta saki mai ƙarfi tana ƙanƙame Hajiya Usaina.
Da sauri Hajiya Usaina ta saki Abdul da maida kallonta ga Lamcy.
Sosai ta zaro ido ganin wuƙar dake gefen cikin Lamcy ga Abdul riƙe da ita ya ciza bakinsa yana ƙara dannama Lamcy.......
“Abdul mikakeyi haka kuma? Kasheta fa kayi?”.....
Dariya ya kwashe da ita yana jan wuƙar ya fitar daga jikin Lamcy, “Bata da wani amfani a yanzu a gareni, ta gamamin aiki mizaisa na barta? Dolene ta wuce kafin ɗan uwana da ke ku bi bayanta, ni kaɗaine na cancanta da wannan dukiyar hhhhhhhhh!!!!!!!......”
Tsagwaron tsorone ya bayyana a zuciyar Hajiya Usaina, ta zabura baya da sauri tana ƙwalalo idanun mamakin Abdul, kanta yay gadan-gadan, ya ɗaga hannu zai daɓa mata wuƙar aka riƙe masa hannu ta baya.
Juyowa yay yana huci dan duk zatonsa Lamcy ce bata mutuba ta riƙesa, amma a mamakinsa sai yaci karo da fuskar jami'in dake bincike akan ɓatar yayansa, Jawaad Abdul-aziz yusuf.
A wani irin razane ya zaro idanu yana sakin wuƙar, zaiyi magana Jabeer ya ɗora yatsansa kan bakinsa yana faɗin, “Shiiiiii!!”.
Sai kuma ya daki ƙafar Abdul ya zube ƙasa jiki na rawa.
Aliyu yay ƙoƙarin kwance Alhaji Kokino da Jawaad ya ɗaure, Hafiz kuwa nakan su Abdul da binduga, sai Rose dake ƙoƙarin bincikar Lamcy wadda da alama da wuyama takai labari.
A take suka tattaresu, ana ƙoƙarin fita dasu, tuni jiniyar motor ƴan sanda da Ambulance dasu Jawaad suka buƙata tunkan su shigo bacar har sun iso.
Alhaji Kokino da Lamcy asibiti aka wuce dasu, yayinda Abdul da hajiya karima aka nufi ofishin su Jawaad dasu.

__________________________________

Da daddare duk muna zaune a falo ana hira, duk da ni a takure nake daga can gefe, ina dai saurarensune kawai, na murmushi nayi na mamaki da takaici na girgiza kaina, dukda suna tsangwamata idan na zauna cikinsu hakan bai hanani son zamanba, dan koba komai ina ƙara ilimin sanin duniya daga garesu, sannan ina rage kaɗaici da damuwa.
Aunty Shahudah da dama ita kaɗaice babu a cikinmu ta sakko daga saman bene cikin wando da riga, sai siririn gyale data yano bisa kai, ganin key ɗin mota a hannunta da bag ya saka mummy faɗin, “ke kuma ina zuwa haka mamana?”.
Tana ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai take fadin, “Mummy jirgin su my friend ya kusa sauka, kin sanshi bayason jira”.
“Okey amma ai baƙya fita ke ɗaya ba adaren nan, Salman ya tashi kuje, tun ɗazunma da driver kika tura da bai ɗakkosa ba?”.
“Mum driver kuma? To da wane yaran zai ɗakkosa?”.
Dariya duk suka sanya, banda ni dama na kasa fahimtar zancen, duk da tun ɗazun dama naji tana faɗin zuwan matafiyin dana kasa yarda a raina namijine duk da yanda take alaƙanta komai nasa da suffofin namiji.
Tashi Salman yay yana tuttura baki irin shi baiso zuwanba, ta jefa masa key ɗin hannunta tana harararsa, amma batace komaiba.
Juyawa tai ta kalleni cikin yamutse fuska tana faɗin, “K karna dawo naga wannan baƙar fuskar taki a falon nan, dan jack ya ganki wlhy zaima iya amai, dan bai saba ganin trash irinki ba”.
Murmushi nayi idona na cika da ƙwalla na miƙe na nufi ɗaki ina maimaita kalmar trash data kirani dashi, sai dai kuma abin mamaki abun baimin zafi sosai ba, dan zuwa yanzu a halayyarta kuma kaɗanne bata zubar na ganiba, gado na haye abina, na faɗa duniyar tunanin da yazamar min abokin rayuwa da ɗebe kewa.
Ban sake sanin hidimar da masu gidan keyiba har washe gari, duk da bayan kusan awa biyu da tafiyar su Aunty Shahudah na fara jiyo ƴar hayaniyarsu, sai kuma gidan ya koma tsitt.

★★★★★★
Chapter 39 · 0% Book details