← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 75

Sashe 6

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa ta shuɗa, dan har maryam ta yaye Abdul-aziz, gashi yana tafiyarsa ko ina ga surutu ko akku ta shafa masa lafiya, yaron akwai wayo na haƙiƙa, gashi kullum yana cikin yara idonsa na sake buɗewa.
A hankali duk wasu wahalhalu da yaran ƙauyen keyi Maryam bata hana Abdul-Aziz shigaba, kiwon dabbobin babansa ma shine ya koma bin yara daji yi, ko yabi zugar yara yo ciyawa, shine zuwa gona shuka ko kwaso amfani da kaka, yana girma wahalhalu na sake hawa kansa, gashi yanata zuwa makaranta anan cikin ƙauyen, dan da farko Alhaji Yusif yayi niyyar maida Abdul-Aziz birni ya samu ilimi tamkar ƴan uwansa amma sai Maryam ta hana, cikin hikima ta nuna masa ta fison Abdul ya tashi cikin wahalhalu irinna ƙauyen, hakan zai taimakawa rayuwarsa ta gobe harma wani ya amfani jibinsa. Badan ya soba ya barsa, itako ta cigaba da sakashi duk abinda ya dace, lokacin da Abdull yakai shekara goma sha biyar tsaf zai ja maka kunyar gona sama da ashirin a nome, faskare wannan yinsa yake, ragamar kiwon dabbobin gidan kam ya koma hannunsa baki ɗaya, duk safiya da an fito sallar asubahi yana makarantar allo, zuwa takwas suke tashi sai yazo yay shirin makarantar boko ya tafi, yana tasowa abinci kawai yakeci ya ɗebo ruwa ya zuzzuba a gidan ya ɓalle dabbobin gidan ya tafi jeji kiwo, bazai dawoba sai gab da magriba, da yayi wanka zaije sallah shi da babansa idan yana gari, idan yana birni wajen sauran matansa zaije shi kaɗai, baya dawowa sai tara da rabi, dan ana gama sallar isha'i yake wucewa makarantar allo again.
Sai rayuwar Abdul-Aziz tazam sam babu hutu, har wasu na ganin maryam ta cika tsauri aka sa, gashi shi kaɗai ALLAH ya azurtata da samu, tun bayan haihuwarsa bata sake koda ɓari ba, baza'a ce bata damuba kam, amma ta danne ta cigaba da harkokinta hankali kwance, tasan dai haihuwa ta ALLAH ce, kuma shine ke badawa ga wanda yaso a lokacin da yaso, guda ɗayanma ta godama ALLAH, fatanta ALLAH ya rayasa ya zama amfananne ga al'ummar musulmai da addinin musulinci.
Rayuwa haka ta cigaba da shillawa, Abdul-Aziz shine autan gidansu, dan suma matansa na birni babu wadda ta sake haihuwa, abinda zai birgeka shine zuwa wannan lokacin kuma duk sun saki jiki da maryam, komai ya wuce, yaransu kan ɗanje hutu wani lokacin wajenta, itama Abdul kanje wajensu dukda dai baya jimawa sabida ya saba da ayyukansa anan ƙauye, acewarsa canko sai dai aita yawon banza da barci da kallo bayan anci an ƙoshi, shiko sam bazai iya rayuwar lalaci ba.
Sauran ƴan uwansa sukan masa kallon mahaukacin da baisan ciwon kansa ba, shiko ko a kwalar rigarsa, har zuciyarsa yake faɗar abinda ke ransa ne.
Yayunsa mata kusan duk sunyi aure, mazanne dai babu wanda ya yunƙuro har yanzu, dukda kuwa a cikinsu akwai waɗanda suka isa auren.
Lokacin da Abdul ya kammala secondary ne wasu a cikin yayunsa sukai aure, shiko Alhaji Yusif yay masa zancen dawowa birni dole saboda cigaba da karatu, sam bayason dawowar, idan ta shine abarsa yayta harkar nomansa da kiwo yafi birgesa, secondary ɗinma da yaya ya gamata, gashi yanzu ne mahaifinsu yafi bukatarsa saboda kulawa da harkokinsa na kiwo da noma, dan ƙarfinsa ya fara karewa girma ya fara kamashi, gashi sauran yayyen Abdul babu mai son zuwa ƙauyenma bare su taimaka masa, su kawai boko suka saka gaba da burin samun daula ta birgewa suci duniyarsu da allura, kasancewar mahaifinsu manomi makiyayi ma takaici yake basu, a ganinsu ajinsu ya wuce ubansu ya ƙare a harkar noma da kiwo, bayan kuma da itace duk suka samu tallafin karatun nasu.
Sosai Abdull ke lallaɓa babansa akan baison zuwa makaranta, amma sam yaƙi saurarensa, yace dolene shima ya fita haƙƙinsa akan karatu tamkar sauran ƴan uwansa.
Babu yanda Abdul ya iya dole yay biyayya, amma koda yatashi karatun sai ya karanci fanin kiwo da noma, dan aganinsa yafi fahimtarnan ɗin.
Ƴan uwansa dariya abun yayta basu, dan aganinsa abunfa na haukar Abdull ya fara wuce makaɗi da rawa, yaro kamar tsatson ƴan rawar banjo. Sam baya kula zancensu, abinda yasa a gaba yakeyi, ga ƙwarin gwiwa yana sake samu da ga mahaifiyarsa da babansa.

Kammala karatun Abdull babu jimawa ALLAH ya ɗauke Alhaji Yusif a duniya, wannan mutuwa ta girgiza dukkan ahalinsa musamman maryam da Abdull, abin ya taɓasu masuƙa, ansha ruguntsumi da tashin hankali har komai ya lafa zukata suka dawo hankalinsu bayan haƙuri da dangana da ya riskesu bisa rahamar UBANGIJI.
Ranar da akai addu'ar arba'in a ranar aka ɗakko zancen raba gado, babu wanda yay jayayya wajen amincewa akai rabo, ita dai maryam bata da abin faɗa, dan ɗaya tilo ne gareta, ita babban tashin hankakinta ma ta yadda zata bar ƙauyen, dan tasan tilas zamanta ya ƙare kenan, gashi ta saba da kowa da komai na yankin.
Ilai kuwa hakance ta faru, dan a yanda rabon gadon yazoma sai da gidan sukayi, dukda Abdul yace abasa zai saya da ɗan kuɗinsa kakarsa ta wajen uwa mahaifiyar maryam sukace zasu cika masa kuɗin, amma tsabar mugunta aka hanasu saya, maryam da ta lura zamansune ba'a sonyi saita lallaɓa Abdull akan yayi hakuri yabar zancen, duk inda ALLAH ya sake ƙaddara zamansu suyi haƙuri su karɓa kawai.
Da wannan nasihar taci ƙarfinsa yayi biyayya, angama raba gado tsaf, ɗan filin gonar da Abdull ya samu ma bawata mai yawa bace, dan haka yay zuciya ya saida tasa, cikin yayyun nasa da aka haɗasu ya saye suna masa dariya akan ya gama wahala amma ya tashi babu tsuntsu babu tarko.
Abdul ma yanada haƙuri, amma lallai akwai zuciyar masifa idan aka kai haƙurinsa tunga, wannan kalmomi da aka jefesa da sune suka bashi ƙwarin gwiwar mikewa da ƙafafunsa ya shiga fafutukar neman na kansa, yayinda maryam ta koma gidansu ta cigaba da rayuwarta, dukda kuwa ana takura mata da batun tayi aure tunda bata wuce yinsa ba.

Abdul ya zage damtse wajen neman halalinsa, ya manta ma da wasu takardun kwalin shaidar gama karatu, kai gaba ɗaya yama manta kansa matsayin ɗan boko, dukda kuwa ga yayyensa sunaci da biro cikin sauƙi, 100% kuma shima ya goyi bayan mahaifiyarsa akan tayi aure, dan shine mutuncinta.
Maryam bata musaba tai aure anan ma cikin anguwar kusa da gidansu, ta auri wani bawan ALLAH da matarsa ta rasu ta bar masa ƴaƴa har huɗu duk mata.
Mama maryam mace ce da ta san kanta, ta kuma yarda ɗa na kowane, dan haka ta rungumi yaran a jikinta tamkar nata, ta kuma tsaya tsayin daka akan tarbiyyarsu musamman babbar da ta zama budurwa. Wannan dalilinne ya jefa ƙaunarta mai tsanani a zukatan yaran da mahaifinsu, harma da danginsa da na mahaifiyarsu. Shima sai ya sake jan Abdull a jikinsa tamkar shine ya haifesa, ya kuma sake nuna masa hanyoyin neman na kai masu sauƙi, dan shi ɗan kasuwane.

A cikin amincewar UBANGIJI sai ƙauna mai ƙarfi ta shiga tsakanin Bilkisu ɗiyar mijin mama maryam da Abdul-Azez, duk da babu burin aure kusa a ransa sai gashi ta canja masa dukkan tunani da tsarinsa, ya rikice ya fara kafa manufofinsa a gareta, koda mahaifinta ya fahimta sai yayta murna, dan shikam dama halayyar Abdul na matuƙar birgesa, hakama mama maryam taji daɗi sosai, ga yaran akwai tarbiyya dama, sannan gasu ainahin ƙyawawa abin son kowa.
Abdul sam bai ɗakko maganar auren bilkisu ba sai da yasamu ɗan abin dogara wajen riƙeta, dan shima dai kudin farko da ALLAH ya albarkacesa dasu a kasuwa saiya koma ƙauyensu ya sai gona ya tsunduma harkar noma tamkar mahaifinsa, ga kuma ɗan kasuwanci yanayi na sai da dabbobi da abincinsu anan cikin binni, ganin yanada abinda zai riƙeta gwargwadon iko sai kawai aka saka biki, haya ya kama na ɗakuna biyu a wani gida, su biyune kawai suke haya a gidan, dan haka komai sai ya zam musu da sauƙi, dan matan nasu duk masu hankaline, babu mai rawar kai aciki.
A Ɓangaren ƴan uwansa kuwa kowanne yana fantamawa rayuwa, dan mafi yawansu duk da biro sukeci, matan kam ba laifi suna auren masu hali, arziƙin ƴan uwansa bai taɓa kwaɗarsa ba balle ya zame masa abin rikewa wajen yimusu hassada, harkar gabansa yake da iya gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa, bai dogara su bashiba, bai kuma zauna damuwa da sunfishi ba. Suko kullum cikin kallonsa mafi ƙasƙanci a cikinsu sukeyi, suna ganin ya tashi a ƙauye, sun fishi karatun boko, sun fishi komai na rayuwa, ko tarkacen kwancen kayansu ko wani abu suka tashi saisu bashi, shiko ya amsa cikin murna da girmamawa, bai taɓaji a ransa dan ƙaskanci sukai masa ba, yasa a ransa da yarda sun fisa ɗin da gaske.

ALLAH mai alkairi, harkar nomansa nata bunƙasa, hakama sana'ar saida dabbobi da abincinsu, har lokacin bilkisu bata taɓa koda ɓatan wata ba, sai da suka shekara huɗu da aure ALLAH ya bata ciki, zo kaga murna wajen Mama Maryam da shi kansa uban gayyar da ƴan uwan bilkisu, ciki na kai wata baƙwai haihuwa tazo mata, aiko tasha wahala kafin ta haifi bakwaini biyu tagwaye, ɗaya ma baizo da raiba.
Sun karɓa hannu biyu kuma sunyi murna da jin tausayin kansu na rasa ɗayan, sai dai kuma hukuncin ALLAH shima ɗayan bai kai labariba ya koma.
Tun da ga nan Bilkisu bata ma sake samun cikiba tsawon lokaci.

*Komai na da sanadi*.
Chapter 6 · 0% Book details