← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 75

Sashe 40

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Da safe ƙin fita nai har lokacin da nakeda tabbacin sun kammala yin breakfast, sai da naji gidan yay shiru sosai sannan na fito, babu kowa a falon hakanne ya bani ƙwarin gwiwar nufar kicin, Amina mai aiki nata ƙoƙarin gyara kicin ɗin, gefe kuma kuku na shirin ɗaura abincin rana, gaisawa mukai duk da suna bani girma kamar kowa na gidan, amma hakan baisa na ɗauki kaina sama da suba, Amina maƙwaftan suke da gidan namu, sai dai su ba masu ƙarfi bane, hakan yasa take shigowa aiki a nan duk wata ana biyanta, tacemin da can ita da mamanta sukeyi, da ciwon ƙafane ya takura mata sai ita tacigaba dayi ita kaɗai.
Itace ta nunamin abincina, dan haka saima na zauna a kujerar kicin ɗin kawai nahau karyawa muna hira da ita, inda shima kuku ke ɗan sakko nasa zancen da turanci, sai hausa ɗai-ɗai wadda sam babu daɗin ji daga harshensa.
Wani irin kuka naji a bayan Windown kicin ɗin, hakan ya sakani kallon Amina ina faɗin, “Minene haka ke kuka?”.
Ƴar dariya tayi tana bani amsa da cewar, “Jojon big Aunty ne”.
Nasan Shahudah suke cema hakan, dan haka nace, “Jojo kuma? Waye mai wannan sunan?”.
Yafitoni tai da hannu alamar nazo na gani, na ajiye dankalin dana ɗauka zansa a baki na miƙe zuwa gareta, kaɗan taja labulen Windown ta yanda zan iya leƙa wajen.
Aunty Shahudah na hango zaune cikin korayen ciyayin da aka gyara wajen da wani ɗan ƙaramin kare mai kama da jikin zaki a saman cinyarta tana shafawa, sai wani tsamurarren bature zaune gefenta daf, Aunty Aamila kwance itama a wajen kanta kamar bisa cinyar baturen suna dariya.
Labulen na saki ina sauke ajiyar zuciya, na dubi Amina sosai, “To Amina wanene jojon a ciki? Dan da alama dai wannan shine baƙon da yazo jiya kenan?”.
Tace, “Karen dake cinyarta shine Jojo, baƙon kuma Jack, a farkon fara aikina gidannan nazo na iske Big aunty da wani karenta jojo, sai dai wataran tsautsayi Boss yazo gidannan ya takashi da mota ya mutu, lokacin har a asibiti ta kwanta jiyyar saboda mutuwar karennan kuwa”.
“Tofa, ALLAH ya ƙyauta to, akan karen? wanene Boss ɗin to? Dan nasan kam ba ƙaramin fin ƙarfinta yayba da har bata ɗauki wani matakiba?”.
Dariya Amina da kuku sukayi, Amina tace, “Aikam kamar kin sani yafi ƙarfin nata, dan har yanzu batayi ko tari hakan a gabansa ba saboda mutuwar karen, ballema ayi tsammanin bin ba'asin yanda abun ya faru, ba kowa bane face mijinta”.
Kaina kawai na jinjina, na koma wajen abincina batare dana ce komaiba, nikam harma naji inason ganin wannan miji na aunty Shahudah, dan kuwa lallai yana ganin shashanci tsantsa daga gareta, inhar shima ba irinta baneba.
Ina cigaba dacin abincina ina sauraren hirar Amina da kuku harna kammala na tashi na fita.

A falo naci karo da Yaya Qaseem daya shigo ransa a matuƙar ɓace, hannu yasa ya wurgani gefe saboda na shigo masa gaba ba tare dana saniba, kaɗan ya rake fuskata bata bugi tebir din gilas dake wajenba.
Na sauke numfashin ambaton Alhmdllh ina binsa da kallon mamaki harya gama haurawa saman benen yana ƙwalama mummy kira tamkar zai tsaga gidan biyu dan azaba.
Tashi nai tsaye jikina har yanzu rawa yake, na shiga murza hannuna daya bugu da kujera yanamin zogi.
Yaya Qaseem ne ya sake sakkowa yana zage-zage da harshen turanci Mummy na biye dashi tana ƙoƙarin riƙesa da masa magana da hausa ita kuma, amma sam yaƙi saurarenta.
Saiga su Shahudah sun shigo suma daga waje da ɗan gudunsu ita da jack da Aamila.
A take falon ya hautsine da hayaniya, nidai ina daga gefe ina kallonsu, sai dai bana fahimtar komai banda wani suna *Jawaad* danaji Qaseem nata ambata, yayinda Shahudah ke masifa tana nunashi, yako kai mata duka sai da jack ya kare shi aka sameshi.
Abu kamar wasa saiga gidan ya harmutse sosai, Mummy sai fama take dasu amma sunƙi suyi shiru, ganin hakanne ya sakata fashe musu da kuka.
Tsitt falon yayi kuma, sukai kanta banda Qaseem da ya fice abinsa rai ɓace, da sauri jack yabi bayansa, Shahudah da Aamila kuma suka zagaye Mummy, Salman baya gidan dai da alama.

Wannan lamari nasu yayi matuƙar bani mamaki, har yamma kuma ban samu jin abinda zai fahimtar daniba, sai abu ɗaya kacal ne kawai na ɗan gane, da alama dai daga wajen aikine aka fusatar da Qaseem, kuma wanda ya sakashi fusatar yanada alaƙa dasu musamman ma Shahudah da haushin Qaseem yaso ƙarewa a kanta...............✍🏻

*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na ashirin da biyu_
*______________________________________*

Kuyi manage babu editing banajin daɗine🤦🏻‍♀
Chapter 40 · 0% Book details