← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 75

Sashe 31

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mintuna ƙalilan kowa ya hallara, Jawaad ya bisu da kallon nazari, kafin yace, “Inason ku bani haɗin kai, duk maganar da wani ya faɗa daga baya na fahimci ƙarya a cikinta sam bazan yafe masa ba”.
Duk suka amsa da cewar zasu fa ɗi gaskiya.
Kansa ya jinjina musu ya koma cikin kujera ya zauna, “Mai gadi da kai zan fara”.
“To yallaɓai”.
“Kaine a gate, kuma dolene komai nisanka da inda mota tai parking a gidannan sai kaga wanda zai fito a cikinta?”.
“Ƙwarai kuwa yallaɓai”.
“A randa Alhaji ya dawo motoci nawane suka shigo gidannan?”.
“Inaga dai kamar biyarne”.
“Kanaga kokuwa ka tabbatar”.
“Ayi haƙuri yallaɓai na tabbatar”.
“Idan Alhaji zai shigo gidannan kafin ranar yana tsayawa gaisuwa da ku? Kokuwa shigewa kawai yakeyi?”.
“Eh idan aka tsaya da mota ya fito daga ciki sai muje muyi masa barka da zuwa kafin ya shige cikin gida”.
“To aranar kunyi hakan?”.
Jimm mai gadi yayi bai tankaba, sai da Aliyu yace, “Ya dai?”.
Firgigit Mai gadi ya dawo hayyacinsa, cikin in ina yace, “Gaskiya bamu gaisa ba, dan na nufi zan gaishesa kenan bayan rufe gate da nayi sai najiyo suna taraddadin baya cikin motar ai”.
“Waye ya fara ambata baya cikin motar?”.
“Bazan iya ganewa ba, saboda ruɗanin dana tsinci kaina a ciki, kuma darene”.
Jawaad yay guntun murmushi yana lumshe idanunsa, da alama akwai ɗan ɓacin rai tattare dashi.
Da sauri ya sake kallon maigadin da har yaji daɗi an gama dashi, “A daren wace motace ta fara fita a gidannan?”.
“Da yake kasan darene yallaɓai, amma mota kusan uku suka fita, sai dai bazan ce gasuwa da suwanene a cikiba, saboda ruwan sama da ya ɓalle.........”
Da ƙarfi Jawaad ya daki tebirin gabansa a wata irin fusata yace, “Ƙaryane!! Dolene ma ka sani”.
Babu wanda bai zabura ba a falon.
Ya kallesu da jajayen idanunsa cikin matuƙar tsawa yace, “Tabbas wanda ya aikata garkuwa da Alhaji yana cikinku, a cikin gidannan yake!! Akwai haɗin bakin wanda ya sanshi, Idan kuma har ya bari na kamashi da hannuna kashinsa ya bushe!” ya ƙare maganar yana nunasu da ɗan yatsa su dukansu, ya miƙe a fusace yana fisgar rigar suit ɗinsa ya rataya a kafaɗa ba tare da ya sauke hannunsa ba ya fice abunsa.
Aliyu ya miƙe da sauri yazo ya ɗauki lap-top da wayar Jawaad da ya bari yabi bayansa da sauri shima yana faɗin, “Hajiya ku sa ido wa junanku kamar yanda ya faɗa”.
Aiko kafin kace mi, hayaniya ta ɓarke a tsakanin Jama'ar gidan babu maijin ta wani, duk ɗinsu Jawaad ya saka musu zargin junansu da bayanin Aliyu na ƙarshe.

Jawaad kam tunda ya fito a harabar gidan yay tsaye yana dube-dube tamkar mai neman wani abu, nanko nazarin komai yake a cikin ƙwarewar aiki.
Gimba da Aliyu suka ƙaraso, a bayansa suka tsaya suna binsa da kallo, ba tare da ya kallesu ba yace, “Aliyu mika fahimta game da kowansu?”.
“Boss abubuwa da yawa ai, wannan mai gadin da alama yasan wani abu, sai dai kamar yanajin tsoron faɗa, hakama amaryar Alhaji ban yarda da itaba, sai ko dattijuwar data kawo abinci kafin kowa......”
Kallonsa sosai Jawaad yayi, ya tsaresa da idanu tamkar a jikinsa ne zaiga gaskiyar abunda yake buƙatar, sai kuma ya saki lallausan murmushi yaɗan kashema Aliyu ido ya juya a hankali yana takawa cikin izza dajin lallai shi ɗinfa ya kai”.
Murmushi gimba da Aliyu sukayi, dan sunsan halin mai gidan nasu akan iya aiki, tabbas fusatar da yay harya fito ba'a banzaba, yana kan sani ya jefa zargi a zukatan jama'ar gidan baki ɗaya......

_________________________
BILKEESU
_________________________

Yau gaba ɗaya tunda na tashi banajin daɗi, da ƙyar ma na iyayin sallar asubahi na koma na sake kwanciya, kowa yasan ba ɗabi'ata bace baccin safe, dan tunma ina gidanmu na haya bansamun hakan, balle yanzu da aikin gidansu inna zainaba kawai ya isheni.
Cikin barci kawai naji saukar ruwa mai azabar sanyi a kaina.
A matuƙar firgice na tashi zaune jikina na wani irin ɓari na razana da sanyin ruwan, ga zazzaɓi dake jikina daman.
Lawusa ce tsaye kaina tana hura hanci tamkar wata guguwar tsakkiyar rani.
“Sannu isassa, waye ɗan iskanki a gidannan da zai tashi ya ɗaura miki abimci ki tashi kici? K bara kiji, bakifa da maraba da ƴar aiki a gidannan, dolene ki bauta mana mu biyaki da abinci da wajen kwana, inko ba hakaba to lallai kuwa sai dai idan gidan zaki bari”.
Yau rana ta farko a rayuwata da nakejin bazan iya ragama Lawusa ba, hakan yasa na miƙe a bazata na zazzaro mata idanuna dake jajur saboda zafin ciwo, nakai hannu na cakumo mata wuya na maƙureta a bango,
“Tunda gidan Ubanki ne dan ALLAH Lawusa karki barni yau na kwana a cikinsa, ke wai shin jakar wane yankin jejice da bakisan darajar ɗan adam ba?! Ko an gaya miki tsoro kesa ɗan adam shiru-shirune?”.
Na ƙare maganar ina hankaɗata ta bugi da buhun masara dake ɗakin.
Ai kafinma na sake cewa wani abu ta fita a guje tana kururuwa wai akawo mata ɗauki zan kasheta.
Tsaki nayi na zube a ƙasa kamar mara laka a jiki, sai kawai naji hawaye masu zafi na saukamin a kumatu, ga wani irin rawa da jikina keyi tamkar mazari.
A haka naji mutum biyu matan maƙwafta sun shigo suna hayaniya, sai sannama na fahimci daga ni sai Lawusa ne a cikin gidan kenan?.
Sunyi maganar duniya nai banza dasu tamkar banajinsu, sai uhu sukemin a kai wai ban ƙyautaba, kalloma basu isheniba.
Lawusa kuwa tana daga bakin ƙofa taƙi shigowa tana kukan munafunci da danƙaramin zagi ta uwa ta uba da gori iri-iri.
A wannan yanayin inna ta shigo ta iskemu, ta tambayi ba'asi, Lawusa ta zauna ta shirya mata ƙarya da gaskiya, hakama matan da suka shigo, tsabar munafunci harda cewa da ƙyar suka ɓanɓare Lawusa a hannuna.........✍🏻

Maza ku garzaya manhajarmu ta youtobe domin samun daɗaɗan labaran littatafanmu akan tashoshin, ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS a Audio, karka bari a baka labari, dan har sabbin buks ɗin zafafa zaku iya samu a tashar ta ALƘALAMI TV😻🤙🏻.

Karkuma ku manta da ZAFAFAN littatafai da ga marubutanku masu ɗunbin fasaha kamar haka.

Hafsat (miss xoxo)
Safiyya Huguma
Hafsat rano
Mamu gee
Bilyn Abdull

Akan farashi mai sauƙi, dukkansu biyar zaku samesu ne a naira ɗari biyar kacal, karku bari ayi babuku. Dan da gaske ZAFAFAN ne.😋😋😃🤝🏻

zaku iya tuntuɓar wannan number akan ZAFAFA👇🏻

*_+234 903 234 5899_*

https://chat.whatsapp.com/HC0krXHdozBCOUYet4vVgw

Wannan shine group ɗin da kawai zaku ringa samun *ƙwai cikin ƙaya* insha ALLAHU.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na goma sha takwas_
*______________________________________*

*_Babu editing yauma😂⛹‍♀_*

...........A mamakin kowa sai mukaji Inna tace, “To kukam ALLAH ya ƙyauta muku, na lura sam jininku bai haɗuba, bara Aibo yazo, ai na samo maganin wannan yawan fitinar taku mara dalili”.
Ba Lawusa kawaiba, koni kaina nayi mamakin maganar inna, danni a zatonama yau saita koreni a gidan saboda na taɓo ƴar mai ɗinta, amma ji yanda ta nunama halin ko in kula akan zancen, sai daimaganarta na ƙarshe akan mafitar data samo ta tsayan a zuciya sosai, komawa nai na kwanta ina rawar sanyina.
Lawusa kam kuka ta sanya rurus wai dama inna bata ƙaunarta ai a gidan, yau sai ta tattara ta barmusu gidansu, sai inna ta aurama Sha'aibu ni a yau da rana danta nuna ma duniya ni ƴar uwartace”.
Duk surutan nata dai inna bata kulaba, matan kuma da sukazo haɗa munafinci sai gasu suna jan ƙafa suna fita ɗai-ɗai da kunya.
Ina jiyo fitar Lawusa tana cigaba da zagin Inna.
Kaina kawai na girgiza ina mamakin irin wannan tarbiyya ta Lawusa, a hakane wannan zata zama uwar wasu, ita kanta tana buƙatar tarbiyyar balle abinda zata haifa.
A haka wahallalen barci ya kwasheni, ban tashi farkawaba sai lokacin sallar zuhur, shima dai inna ce ta tasheni akan naje nai sallah.
A mamakina kuma na fito zanyi alwala sai naga inna tayi abincin rana da kanta bata tasheni ba.
Salla nayi, ina zaune sai ga sallamar Yaya Shu'aibu ya dawo cin abincin rana kamar yanda ya saba, muryar Inna na tsinkayo tana sanar masa bani da lafiya, hakan ya sakashi faɗin “Subahanallahi, miya sameta kuma?” yay maganar yana ɗage labulen ɗakin.
Sannu nai masa sannan na gaishesa, cike da kulawa ya amsa, ya ƙarasa shigowa ɗakin yana tambayata mike damuna?.
“Yaya zazzaɓine kawai, kuma Alhmdllh yama sauka”.
“Wayyo sannu, ai ko sauron gidannan ya isa saka mutum zazzaɓi, kici abinci saina kaiki kamiz ki amshi magani”.
Nace “to” tare da masa godiya.
Nanma nazata Inna zatace a'a sai naji batace komaiba, sai ma amsar tambayarsa akan Lawusa take bashi, duk abinda ya faru tsakanina da Lawusar ta zano masa, ta ɗora da faɗin, “Ni yanzu na samo mafita akan wannan yawan rigimar tasu, fitar danai yau wani gida ƴar kande ta rakani na samowa Bilkisu aikin wanke-wanke da shara, inasha ALLAHU tananma sai kaga ta haɗa kuiɗin kayan ɗakinta har muma mu mora, kaga bama ta yini gidanba balle wannan fitinar ta cigaba da girmama a gidannan”.
Shu'aibu da fuskarsa ta ɗan nuna alamun damuwa, yace, “Amma Inna ni dai da kinyi shawara dani da ba'ayi hakaba, wane kuma aikin wanke-wanke Bilkisu zatajeyi fisabillahi, ni dai duk da sana'ata ba wata mai ƙwari bace zanyi iya bakin ƙoƙari wajen sauke haƙƙin zuminci akan komai na aurenta, indai dan zaman gidane zanma matarcan ta tsallake magana Bilkisun taje ta fara koyon ɗinkin jakka a wajenta, kinga ko aure tayi ai tasamu madogara insha ALLAHU”.
Ran inna a ɓace tace, “Nikam Aibo bansan miyasa kake nina tamkar ina zalintar yarinyarnanba, yanzu shi aikin da zataje bazai taimaketaba ne? Ko aure tayi ai dai ta samu ta iya komai”.
“Hakane Inna, nima banƙi ta takiba, muyi addu'a to ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi a ciki, idan ta samu lafiya sai muyi maganar”.
“Shike nan”
Inna ta faɗa a taƙaice, da alama dai har yanzu ranta babu daɗi akan canja mata tsari da yayi.
Chapter 31 · 0% Book details