← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 75

Sashe 22

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

............Da sallama ya shigo falon, Shahudah da mama Atika dake zaune duk suka zuba masa idanu, yana sanyene da ƙananun kaya farare tas gaba ɗaya, duk da bana kwalliya bane yayi ƙyau abinsa, ga wani annuri da cikar haibar kwarjininsa na fitowa a fuskarsa.
Babu walwala a kan fuskar tasa, ya risina yana gaida Mama Atika.
Cikin fara'a ta amsa masa tana tambayarsa ya aikin nasa, ta kuma ɗora da ƙorafin rashin zuwansa gaidasu a koda yaushe.
Haƙuri kawai ya bata yaja bakinsa yay shiru, bai ko kalli inda Shahudah takeba, ita kuma ALLAH bai bata tunanin tako gaidashiba.
Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna da basu gaza uku ba, kafin sallamar Uncle Uwaisu ta katse musu tunani.
Yana zama Uncle Bashir shima ya shigo, dan haka Jawaad yay musu gaisuwa a tare cikin girmamawa.
Sai da suka kammala gaishe-gaishen nasu, suma sukai masa ƙorafi akan rashin ganinsa akai-akai, kamar yanda ya saba dai haƙurin ya basu suma da tabbatar musu da yanayin aikinsane ya kawo hakan.
Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shiyyasa suka saki wancan zancen suka tsunduma maganar data tarasu game da ƙararsa da Shahudah ta kawo.
Hakan ba sabon abu bane a wajensa, shiyyasa baice uffanba har suka kammala, itama Shahudah aka sata ta maimaita komai daya faru.
“Jawaad kaji abinda matarka tace, shin hakane? kokuwa akwai kuskuren fahimtarta a ciki?”.
Guntun murmushi Jawaad yayi, cikin nutsuwarsa yace, “Uncle ni dai gareni babu komai, amma tunda ita na mata ba dai-daiba tayi haƙuri, akan rashin sanine”.
Dukansu sagade sukai suna kallonsa, duk da dama a koda yaushe irin wannan zaman ya haɗa amsar da yake basu kenan sai ta yau tafi ƙona ransu, a ɗan fusace Uncle Uwaisu yace, “Jawaad ka daina mana wani ɓoye-ɓoye akan abinda ke faruwa tsakaninka da matarka, mu dai iyayenkune ku duka, bamajin daɗin yawan matsalolin dake kunnowa a cikin aurenku, gashi kai kullum akazo irin wannan zaman sai kace batai maka komaiba, anya kuwa gaskiya kake faɗa?”.
“Uncle gaskiya nake faɗa, da tamin wani abu dana faɗa ɗin......”
“Wlhy ƙarya kake bb, ban maka wani abuba kake cewa kayi nadamar aurena, wai harma bazaka taɓa yafema kanka hakanba”.
Banza Jawaad yay mata bai tankaba, yayinda su Mama Atika suka zuba masa ido suga idan zaice wani abu, amma sai sukaji yaƙi cewa komai.
“To kaji abinda tace Jawaad”.
Uncle Bashir ya faɗa yana kafesa da idanu.
Kamar Jawaad bazai amsaba sai kuma ya gyara zamansa yana kallon Uncle Bashir ɗin, “Uncle wannan zancentane kawai, ita tasan a inda ta samoshi”.
Gaba ɗaya ba ƙaramin haushine ya turnuƙe zukatansu ba, musamman ma Shahudah da kamar zuciyarta zata babbake dan baƙin cikin murɗaɗɗen halin Mijin nata......
Mama Atika tai ƙarfin halin haɗiye nata ƙududun tana ƙaƙalo murmushin yaƙe, “To shikenan yanzu duk abar wannan maganar tunda yace shi babu komai, sai kuyi musu nasiha suyi haƙurin zama da juna kamar yanda kowa ke zaune a nasa gidan, ni dai zan faɗi maka albishir mai gidana Jawaad”.
Ɗago manyan idanunsa da suka sake girma saboda ɓacin rai yay ya kalli kakar tasu, sai dai baice komaiba.
Ta faɗaɗa fara'ar ta tana cewa, “Matarkace ke ɗauke da cikin wata ɗaya da wasu kwanaki”.
Kafeta da ido Jawaad yayi, sai kuma ya janye ya maida kan Shahudah, baka isa fahimtar farin ciki yayi ba kokuwa baƙin ciki.......
Shahudah ta katse masa tunani da faɗin, “Nifa kuma bar lasa masa zuma a baki Hajiya, dan wannan cikin zan zubdashine, dan yazo ne akan kuskure, sainan da shekaru tara zan sake amsar waninsa, lokacin mun cika shekara goma da aure.......”
Cikin Hanzari Uncle Uwaisu dake kusa da ita ya kai mata duka, kaucewa tai tana kumbura baki.
“Wai miyasa baki da hankaline shin Sabira?, mike damun tunaninki ne?......”
Murmushi Jawaad ya saki yana katse Uncle Uwaisu da faɗin, “Uncle barta, tanada gaskiyarta itama, haka muka tsara ba yanzune zamu haihuba saboda gudin karmu tsufa da wuri, “Hudah nawa kike buƙata dazai isheki ganin likitan da zai zubda cikin?”.
A matuƙar razani duk suka kalleshi, banda Shahudah da daɗi ya lulluɓe, babu kunya ta taso daga wajen zamanta ta faɗa masa ajiki tana ƙanƙamesa, dukda yaji kunyar hakan saiya basar shima yaɗan rungumota yana bubbuga bayanta, ɗago kanta tai ta sumbaci goshinsa da laɓɓansa, tana niyyar kissing ɗinsa ya kauda fuskarsa da ɗan tureta kaɗan a jikinsa.
Wannan abu yabama su Mama Atika matuƙar kunya, dan haka duk suka kauda kansu garesu, Shahudah kuwa ko a jikinta, neman ma ɗare cinyarsa take zata zauna yay mata gargaɗi da idanu.
Matsawa tai tana wata siririyar dariya da faɗin, “Bb har yanzu baka wayeba, ai dai matarkace ni balle ace munyi abu mara ƙyau, tunda komai ku hausawa a wajenku baida ƙyau.......”.
“Kinci gidanku Sabira”. ‘Uncle Bashir ya katse Shahudah cikin mata daƙƙuwa’ yaci gaba da faɗin, “Ke yanzu da ƙaniyarki a gabanmu kike faɗar wannan maganar?”.
A hannun kujerar da Jawaad yake ta zauna tana dariya, ta maƙale damtsen hannunsa tana ɗora kanta ta kwantar jikin hannun.
Ko motsi Jawaad baiyiba, ya kuma fuske abinsa kamar ba shi ta kwantama a jikiba.
Rashin mutuncin Shahudah ya wuce dukkan tunanin su mama Atika, dan haka suka ɗauke kansu akanta.
Mama Atika tace, “Kai yanzu nan Jawaad da hankalinka zaka biye mata ku zubda ƙyautar da ALLAH ya baku? Wane irin banzan aƙidane wannan? Ku ba'a haihuwa aka haifeku ne?”.
“Kiyi haƙuri hajiya, ni karkuga laifina, Hudah itace mai ɗauke da cikinnan, sannan itace zata haifesa, ta rainesa, ta bashi tarbiya, to taga bazata iyaba ni mizaisa na takurata, bayan kuma ƴancintane zaɓama kanta duk abinda taga ya dace da ita, inhar batason ta haihu yanzu zan goya mata baya ta zubda cikin, idan kuma zata haifesa zanfi kowa jin daɗin hakan,duk shawarar data tsaida ta sanarmin”. Ya ƙare maganarsa da ƙokarin cireta a jikinsa ya miƙe, “Kuyi haƙuri bara naje, dan nanda awa biyu zan sake fita, inason naɗan huta kafin lokacin”.
Babu wanda ya iya cewa komai sai Shahudah da tai tsigil tana faɗin, “Bb jirani mu wuce”.
Tsayatan kuwa yayi, ta shiga ɗakin Mama Atika ta ɗakko wayarta ta fito, a gabansu Uncle Uwaisu Jawaad ya kama hannun Shahudah suka fice abinsu”.

“Turƙashi”. ‘Mama Atika ta faɗa cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya’.
Daga Uncle Uwais har Uncle Bashir babu wanda ya iya cewa komai, dansu lamarin yafi ƙarfin tunaninsu.
A wannan yanayin Hajiya Humaira ta shigo ta iskesu itama.....

★★★★★★

Suna shiga Sashensu Shahudah ta maƙalƙale Jawaad tana dariya.
“Nagode ALLAH da yau ra'ayina yazo dai-dai da naka bb na, ina sonka harma babu adadi”.
Wani munafikin murmushi ya saki shima ya rungumeta, murya can ƙasan maƙoshi yake faɗin, “Duk abinda matata takeso nima shi nakeso, kuma tsarinki ya birgeni tawajena”.
Da sauri Shahudah ta ɗago kanta ta manne bakinsu waje ɗaya, babu musu Jawaad ya amsheta hannu biyu, tun a falon labari yaso fara canja salo, da ƙyar ya iya ɗaukarta ido rufe suka haura sama.

😉ni dai a falo nai zamana gudun gano abinda malam ya hana😂⛹🏻‍♀️.

Jawaad ya sumbaci goshin Shahudah dake jikinsa a lafe bayan lafawar komai, shi shaidane akan ƙoƙarinta na bashi dukkan farin ciki a makwancinsu, halayyarta da tsarintane kawai matsalarsa, dan ba mu'amular kwanciya kawai ya dace mace ta ƙware wajen mijinta ba, akwai wasu farin cikin dake girmama danƙon zaman lafiya da ƙarfafa soyayya ga ma'aurata, mafi yawancinsu a kula da gidan ma ake samunsu.
Sake matseta yay cikin jikinsa yana lumshe idanunsa alamar sonyin barci........

_______________________
BILKEESU
_______________________

...........Har muka shigo gidan zuciyata da tunanina basu gaza wajen cuɗanya game da gidan dana tsinci kainaba, kamar yanda na saba na ɗauro alwalar barci, har zan kwanta sai zuciyata ta bani ƙarfin gwiwar miƙa kukana wajen UBANGIJI, hakkane yasa na shinfiɗa ɗankwali na kabbara salla.
Ƴar daɓas da Nazy basa ɗakin, bansan ina suka maƙaleba duk da tare muka shigo cikin gidan.
Ina cikin salla naji shigowarsu, duk da hankalina ba a kansu yakeba kusan mintuna biyu da shigowar tasu sai nakeji wani nishi-nishi tamkar wasu mayu sunga nama.
Koda nai sallamar sallata ban kallesunba, saina sake miƙewa na kabbara wata sallar, kafin na idar ne abin nasu yay ƙarfin da har waswasi ya fara min kutse cikin sallata, takaitawa nai nayi sallama dan son ganin wane hali suke ciki? Ni duk tunanina ko wanine baida lafiya a cikinsu.
Cikin matuƙar razana da firgita na ƙwalla ƙara, kafin wani lokaci jina da ganina duk sun gushe.

Ƴar daɓas taɗanyi ƙoƙarin janye Nazy dake mamuƙe da ita dan bama bilkisu ɗauki, amma sai Nazy ta sake matseta tana mata wani salon sheɗancin da ya sata maida hankalinta gareta, cikin narkewar murya Nazy tace, “Barta Sweet, ta firgitane kawai saboda bata taɓa ganiba, a haka harzata saba itama ta fara sha'awar abun a ranta” bata bari ƴar daɓas ta bata amsaba ta haɗe b.......

(Wa'iyazubilla) kaicon wannan mummunar rayuwa al'ummar MANZON ALLAH, yanzu waɗanan fa sune har suke iya bugar ƙirji su kira kansu cikakkun musulmai masu jiran samun aljanna😭, sune suke buƙatar addinin musulunci yay alfahari dasu matsayin al'ummarsa?😭 sune suke buƙatar ƴaƴa suyi alfahari dasu matsayin iyaye😭 ya rabbi ka wajabta mana tsoronka a zukatanmu, ka hanamu shagala da duniya da kayan cikinta, ALLAH ka rabamu da asararriyar rayuwa mara amfani😭😭😭😭🙏🏻🙏🏻.

★★★★★★

Ban tashi farkawa ba sai da zafin rana ya fara dukan fuskata, na buɗe idanu da ƙyar, inda na ganni kwance ya sani tashi zaune a firgice saboda tuna abinda ya faru jiya, waige-waige na farayi a cikin ɗakin, ganina ni kaɗai a cikine ya sakani sauke numfashi ina share hawayen da ke ziraromin, abinda na gani a daren jiya ne kawai ke dawomin cikin idanu da zuciya......
Shigowar Nazy ɗakin ya saka gabana faɗuwa, nai saurin duƙar da kaina saboda wata kunya data kamani, sukuwama da suka aikata ko a kwalar rigarta.
Ina jiyo sautin murmushinta ta zauna kusa dani, “Oh Balkisa minene damuwarki? Idan abinda kika gani jiyane karya dameki Please, wannan shine ƴancin ai, ki gwada harkarnan zakiji daɗinta, uwa uba zakiyi arziƙi, ki zama hamshaƙiyar mace abar kwatance a duniya, dan yanda ALLAH yay miki jiki mai ƙyau ɗinnan wlhy abincin manyan hajiyoyi zaki zam.......”
Chapter 22 · 0% Book details