← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 75

Sashe 23

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Wa'iya zubillah” na faɗa a fusace ina zazzaroma Nazy idanuna da sukai jazur, ga hawaye na kwarara a cikinsu, cikin nunata da ɗanyatsa nake cigaba da faɗin, “Karki sake danganta ni da wannan shaiɗancin mai gusar da imani, ina roƙon UBANGIJI na ya shiryeku, kuma zukatanku su buɗe, tunaninku ya fara gudana akan bigiren gaskiya, kukuwa wace amsa harsunanku suka tanada wajen bama UBANGIJIN al'arshi aranar da gaɓɓai ne kawai zasu bada amsa ba bakuna ba? Wa kuke taƙama dashi da zai tsaya muku a ranar da rana take gab da ƙwakwalen mutane? Wani ƙwarin gwiwa kuke dashi na gujema makoma irinta mutanen ANNABI LUƊU da suka gushe akan wannan mummunar ɗabi'ar? Wace amsa gareku akan iyayenku da sukasha wahalar baku tarbiyya bayan ɗaukar ciki da haihuwarku zuwa ciyar daku har kuka kai wannan munzalin girman? Wace amsa gareku ga al'ummar daular musulinci da kuka fito a ciki? Tayaya kuke tunanin akan alfahari da MANZON ALLAH zaiyi daku kasancewarku al'ummarsa? Kaicon wannan Rayuwa ta dabbanci, kaicon wannan buri mara amfani, kaicon wannan duniya mara dorewa, kaicon dukiyar da zata zamewa mamallakanta dana sani, kaicon rufaffiyar zuciyar da bata banbance ƙyaƙyƙyawa da mummuna, kaicon sha'awar dake tunzura zuciya bisa ɗabi'ar aladu, inama na tsaya ƴan sanda sun kamani, da inada ilimi akan sanin tarar daku a ƙaddarata dana roƙi UBANGIJINA ya ɗauki ruhina kafin zuwana gareku.......”

Ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurarenta, harshenta ya sarƙe ta kasa cigaba da magana.
Kan ƴar daɓas dake bakin ƙofa tsaye da wasu ƴammatan gidan kusan su shida duƙe saboda wani irin rawa da zucikatansu keyi akan kalaman bilkisu, ita kanta Nazy tsigar jikinta sai tashi takeyi........

Da sauri suka waiga bayansu saboda jin gyaran muryar Uwargida, babu wanda bai ruɗeba a cikinsu da ganinta, dan ɓacin ran dake fuskarta kawai ya isa tabbatar musu da taji komai akan kalaman Bilkisu, darewa sukai biyu suka bata hanya, cikin takunta na izza da bushewar zuciya ta tura kai cikin ɗakin....
Wani wawan mari ta sauke mani a fuska, na ɗago a razane ina kallonta, saukar wani na sakeji, kafin na dawo dai-dai an kuma saukemin wani, tun ina fahimtar adadin marukan har ruɗani ya sani gaza fahimta.
Jinai kawai an sungumeni anyo waje dani, ina kuka da roƙonta amma taki saurarena, ta wata ƙofa dake a cikin gidan tabi dani, ashe gidane mai ƙyau a wajen, wanda shine matsayin sashenta.
Ban damu da kawatuwar gidanba, burina kawai sauka daga jikinta na samu hanyar kuɓuta.
Wani makeken ɗaki daya jiƙu da kayan more rayuwa ta kaini, ta jefani bisa bankeken gadon ciki wanda tashin hankalin da nake ciki bazai barni lissafa muku haɗuwarsa ba..............✍🏻

https://youtu.be/6YuGtf5lQF8

Maza garzaya domin sauraren cigaban littafin *KARAYAR ARZIƘI* Na Bilyn Abdull a *MANHA HAUSA NOVEL'S*.

Ku danna Subscribing domin nuna ƙaunarku garemu, tare da ƙararrawar sanarwa dan samun shirye-shiryenmu a duk lokacin da muka ɗora.

MANHA HAUSA NOVEL'S (Ƙyautar ALLAH).

*takuce, kuma natane, ta hanyar kasancewa da itane zamu sake tabbatar da wanene yafi son wani😉👌🏻😻😻😍😍🥰💃🏻*

🗣 *_RANAR KUKE JIRA YAU GATA TAZO📻📻💃🏻💃🏻💃🏻_*

*_ZAFAFA 👭🕴🏻👫, DA TAMBURANMU GAMU MUNZO💃🏻💃🏻💃🏻📻📻_*

*_MASOYA MUKE KIRA DAN KUWA MUNZO💃🏻💃🏻🤫😉😂_*

*_Dan dan dan dan dan, ina masoyan suke?, ga fa ZAFAFAN BIYAR sun sake faso muki da wani SABON KAFCE mai tsuma zuciyar abokin tafiya_*

_ZAFAFAN dai nan nakune, waɗanda suka barbaje basirarsu a littatafai biyar da suka shuɗe, masu saka nishaɗi da tada kunnuwan mai karatu sama tamkar yana tailunar kilishi😉_.

*_Kunsan wanima abin jin daɗi kuwa? To wlhy ina mai tabbatar muku KAFCEN wannan lokacin ya ɗara na farko, domin kuwa madarar basira zasu kwarayar, tare da nagartaccen ilimi mai garɗin dabino_*

_Maza ku garzayo dan kaɗan ya rage a fara al'amura, farar takarda da biriknmu duk riƙe suke a hannu, hallaruwarku guri gudane zai bamu ƙwarin gwiwar suburbuɗo muku daɗaɗan labaranmu kamar haka._👇🏼

_*IGIYAR ZATO.....*:- Na marubuciya Hafsat (miss xoxo), labarin soyayya mai ƙyatarwa, cakuɗe da tsagwaron cakwakiyar ruguntsumin abin al'ajabi_.

_*ƘAUNAR MU:-* Na Mamu gee, labarin madarar soyayya ƴar asali da babu sirkin ruwa a cikinta, ga wata sambaɗeɗiyar zumar zaƙin daɗi mai saka zuciya zumuɗi._

_*ƊAURIN GORO...:-* Na Hafsat rano, Kitumurmura kenan, amma ta lobayyar baje basirar ƙofofin zukatan masoyan da suka samu ɗaurewa bisa makirci ta cakwakiyar maƙiya_

_*ALƘAWARIN ALLAH:-* Na Safiyya huguma, labari mai tsagwaron nuna jarumtar masoyan da ƙaunar gaskiya ke ambaliya da dulmiya cikin tsantsar ƙauna, dukda ɗunbin zagon ƙasar da ake tafka musu._

_*GUDU DA WAIWAYE....:-* shi ya kawo mugun zato. inji masu iya maga. Na Bilyn Abdull, labari mai ɗaure da sarƙaƙiya a zukatan masoyan da yarda ta amince musu kasancewa a inuwa ɗaya, amma tsagwaron cakwakiya da hargitse-hargitsen ƙaddariri suka tarwatsa hakan._

*_Tabɗi jan, wannanfa shine ZAFAFAN, to kai mai karatu tayaya zaka tabbatar zafafanne?, bari na baka satar amsa😁👇🏼_*

_*Amsar itace😉*👉🏻 ƙoƙarin mallakar ZAFAFA ta tsafta tacciyar hanyar sanƙamawa jagororin tafiyar kuɗi kamar haka.👇🏼_.

_*NAIRA 500*, mabuɗin mallakar litattafan ne gaba ɗaya biyar hankalinka kwance_

_*NAIRA 450*, Zata mallaka maka littatafai huɗu._

_*NAIRA 400*, tikitin mallakar littatafai uku_.

_*NAIRA 300*, zai baka lasisin mallakar littatafai biyu_.

_*NAIRA 200*, Na mallakar littafi guda ɗayana._

*_Kunji wata rahusa ƴan uwa? Yo duk saukinnan saiki zauna daɗaɗan labarannan guda biyar su wuceki duk da gwanayenki ne mamallakansu?🤔😳_*.

_Maza garzaya ki sanƙama ƴan kwabbanki ta wannan asusun bankin domin mallakar zafafa masu sanyaya zuciyar mai karatu._

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na goma sha huɗu_
*______________________________________*

..............Kusan a tare suka farka da ga barcin da ya kwashesu, sai dai yanda Shahudah taci karo da fuskar Jawaad sai zuciyarta ta shiga yimata wasuwasi.
Ya sauka a kan gadon ba tare da yace da ita uffanba, bayi ya shiga, ta miƙe da sauri tabi bayansa, sai dai a mamakinta ya rufe ƙofar bayin.
Ɗan bugawa tai kusan sau uku, yanajinta lokacin yana ƙoƙarin haɗa ruwan wanka amma sai ya shareta kawai tamkar bai jiba.
Dole ta haƙura saboda motsin fara wankanta da tajiyo.
“Mike damunsa kuma?” ta faɗa a fili cike da mamaki, kujerar gaban mirror ɗinta taja ta zauna, bayan wasu mintuna kusan ashirin sai gashi ya fito yana tsane jikinsa da towel.
Yanzun ma dai fuskar babu walwala, bai kuma kalli sashen da Shahudah takeba ya wuce wajen kayansa, jallabiya ya ciro a drawer, ya juyo zai saka suka haɗa idanu da Shahudah data kafesa da idanu.
Janye nasa idon yayi kamar bai ganta ba, saida ya saka jallabiyar a jikinsane ya ƙaraso gaban mirror ɗin yana ɗaukar turare zai fesa.
“K bazaki tashi ki wanka ba kizo kiyi salla?”.
Shiru kamar bazata tankaba, sai kuma ta sauke numfashi tana miƙewa, gabansa ta matso kamar zata shige jikinsa, ya ɗan matsa baya kaɗan yanda zasu sami tazarar data matse.
“Humm” ta faɗa cikin kafesa da ido, muryarta a raunane tace, “Bb yanaga ka canja daga tashinmu? Naga cikin farin ciki muka shigo gidannan”.
Turaren hannunsa ya ajiye, ya juya zai tafi ba tare da ya bata amsaba, saurin riƙo hannunsa tayi, bai juyoba, sai dai a hankali ya furta, “Karki ɓatan lokaci salla zanje”.
Dole ta sakar masa hannu saboda fisgar da yayi, harya fice tana binsa da kallo.

A tsakkiyar falon ƙasa ya tsaya, ba tare da ya kalli ko inaba a cikinsa yace, “K fito, idan kuma kika bari na fito dake wlhy saikin raina kanki”.

Mamaki ya kamani, dan ni dai bilynku banga alamar mutum a falonba, amma maganar Jawaad ta sakani waige-waige, a raina ina tunanin ko aljani ya gano.
kamar da wasa kuwa saiga ɗaya daga ƴammatan gidan ta fito daga ƙasan bene jiki na rawa.
Fitowarta yay dai-dai da sakkowar Shahudah da tai tunanin Jawaad ya fice.
Jikin Amrah sai ɓari yakeyi, dan batasan ta yaya Jawaad ya ganta a falon ba, tunda ta rigasu shigowa shi da Shahudah.
Juyowa yay ya kalleta da rinannun idanunsa masu firgitasu, yay mata kallon sakwan biyu ya janye yana kallon Shahudah dake tsaye jikinta sai tsuma yake dan tsoro, dan batai tunanin Jawaad zai ga Amrah ba.
Murmushin takaici ya saki launin idonsa na sake yin duhu, ya nuna kansa cikin ɗacin da yakeji a zuciyarsa yana faɗin, “Ni kika kirama wata taga yanda zanyi kwanciyar aure da ke Hudah? Saboda kawai ki burgesu akan ina miki duk abinda kikeso ko? To gata nan, saiki zauna kafin na dawo massalaci ki ida sanar mata duk abinda ya faru a cikin ɗakin da bata ganiba”.
Ya maida kallonsa ga Amrah itama, tana tsaye tamkar zatai fitsari a wajen dan firgita, “K kuma yanzu nasan kin yarda inabin dukkan abinda takeso ko? Tunda na amince mata ta zubar da ciki, ta kuma gigitani da salonta a gabanki wanda yasa nake koma mata soko” yay murmushi irin mai nuna tsantsar takaici ɗinnan, kasa cigaba da musu magana yayi ya juya ya fita zuwa massalaci.
Chapter 23 · 0% Book details