← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 75

Sashe 2

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsitt ɗakin yayi bayan tsawatarwar da akayi, yanzu ma ɗaya daga cikin shugabannin ne yay magana.
“Duk wani kace nace bama buƙatarsa anan, kowa yasan wanene JAY akan ƙwazon aiki, ba wannan ne na farko ba da aka bashi irin wannan damar kuma ya magance ta, sai dai ko wanne irin case da ruɗanin da yake zuwa da shi, dan haka a wannan gaɓar mun naɗa Jawaad Abdul'aziz yusif matsayin wanda zai kula da wannan case ɗin, sannan mun saka Qaseem Ali matsayin mataimakinsa, kuna da damar haɗa rundinar jami'ai 30 da zasu taimaka muku, muna fatan zaku bamu gudunmawa ta haƙiƙa wajen fiddamu kunya ku kuɓutar da Alhaji Sadi cikin lokaci ƙankani da baza'a ga rauninmu ko gazawa ba”.
Tunda ya fara magana Qaseem yaji sunansa matsayin mataimakin JAY fara'ar fuskarsa ta ɓace ɓat, hakama magoya bayansa. Ga Jawaad kam bai ko ɗago kaiba balle musan yanayin da yake ciki.
Sun ɗan cigaba da tattaunawa kusan na awa ɗaya, wandda acikin awa ɗayarnan ba ƙaramin a takure Jawaad ya tsinci kansa ba, ana kammalawa ya nema izinin zuwa gida ya ɗan huta koda na awa uku ne.
Babu wani jan zance aka bashi dama, dan yanayinsa ya nuna buƙatuwa sosai na san hutun.....

*___________________________________*

Tunda Gimba yay fakin motar a harabar gidan ya buɗe idanunsa da suka sake masa nauyi da ƙyar, ba tare da ya jira Gimba ya buɗe masa murfinba ya buɗe da kansa ya fice, rigar sanyinsa ce kawai a hannunsa sai bindiga da ƙaramar wayarsa da ya fita da ita kawai.
A yanda ya shigo ya ga falon jiya yauma haka ya sameshi, yaja siririn tsaki yana haɗiye wani abu mai nauyi da ya tsaya masa a maƙoshi, zuciyarsa a matuƙar cinkushe ya ƙarasa sama inda nanne ɗakin barcinsa yake.
Kallo ɗaya yayma falonsa ya ɗauke kai, dan hatta da kofin da ya sha shayi a daren jiya yana a inda ya barsa, sam shi baima san wace irin mace ya aura ba, ƙazama ko ballagaza?. Takaici bai nemi shake numfashinsa ba sai da ya ƙarasa haɗaɗɗen bedroom ɗinsa ya sauke dubansa a kan lafiyayyen gadonsa da har yanzu take kwance, ta wani ƙudundune cikin lallausan bargonsa tana shaƙar barci. Tuni idanunsa sun sake kaɗawa sun koma jajur, yayinda jijiyoyin kansa suka sake fitowa raɗa-raɗa, yasan ko rantsuwa yay baza a bisa bashin kaffara ba akan Shuhudah batai sallar asuba ba.
Bai sake kallon gadonba ya jefa rigar sanyin akan sofa tare da zube wayarsa da bindigar saman tabirin dake shakanin kujerar da gado.
Duk da wani jiri-jiri da yake gani saboda yunwar da ke cin hanjinsa hakan bai hanashi nufar bayi ba dan ya samu ya watsa ruwa ko zai samo kan jikinsa...............✍🏻

*_Turƙashi, wannanfa shine Cakwakiyoyi ba Cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum😉._*

_Ku kasance tare da ni Bilyn Abdull dan jin yanda wannan littafi mai suna a sama zai kasance, minene ma ma'anar *ƘWAI CIKIN ƘAYA!!?*, nasan wannan tambaya ce dake cikin zuciyoyin masu karatu baki ɗaya, wadda ni Bilynku kaɗai zan baku amsarta😚._

*Zata iya kasancewa cikakken buk ɗin sai bayan sallah ƙarama zaizo muku idan munkai da rai, idan kuma na samu dama koda ba kullum ba zanyi wasu pages kafin azumi insha ALLAH☺️🧐*⛹🏻‍♀️

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*🧺

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Ban yarda wani yaymin amfani da littafin nanba ta kowacce hanya, komin ƙanƙantarta, inkuwa hakan ta kasance ban yafe ba☹️._*

_Na sadaukar da wannan littafi a gareku auntys ɗina, dan kune taurarin da Bilyn Abdull ke kallo a duniyar rubutunta, da ku kuma zan cigaba da alfahari *Aunty Fareeda Ado gachi & Aunty Rahama Abdul-Majeed (writer mace mutum)*, alkairin ALLAH ya kai muku a duk duniyar da kuke har gadon barci._🥰😘👌🏻

*Wattpad* ➖ _BilynAbdull_😉

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na biyu_
*______________________________________*

............Motsin ruwan wankansa ne ya farkar da Shahudah, tunda ta yaye bargon da ga fuskarta nake tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali da ya halicci wannan ƙyaƙyƙyawar baiwa tasa. Lallai Shahudah ƙyaƙyƙyawace wadda zamu iya sakata a jerin farko na ƙyawawan mutane, gata fara tas tamkar wata aljana.
Har lokacin bata yaye bargon da ga jikinta ba, kamar yanda alamu suka nuna bata da niyyar tashi ma.
Kusan mintuna arba'in da shigarsa bayin sai gashi ya fito ɗaure da tawul ruwan sararin samaniya, yayinda ya rataya ƙarami fari a wuyansa, ya kama can ƙarshen tawul ɗin yana goge gefen kumatunsa.
Shahuda da har yanzu take kwanci ta a hankali ta buɗe ƙyawawan idanunta ta sauke akansa, hakan yayi dai-dai da kai nasa duban gareta shima. Kuma tamke fuska yay yana kauda idonsa a kanta tare da nufar mirror kansa tsaye. Kamar yanda baiyi magana ba itama sai bata ce uffanba sai binsa da kallo da takeyi.
Duk da Jawaad naji a jikinsa kallonsa takeyi bai juyoba, amma yana kallonta ta cikin mirror, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Kinyi salla?”.
Ɓata fuska tayi tana kuma narketa alamar son yin shagwaɓa, “Haba bb, kamun laifi maimakon ka lallasheni da ban haƙuri saika wani faramin tambaya”.
Duk da ya jita sarai sai ya share tamkar bai jiba, ya cigaba da shafa mansa yana lullumshe ido saboda ciwon da har yanzu ya keyi, sauƙinsa ma ruwannan da ya sakarma kan ya ji daɗinsa sosai gaskiya.
Ba ƙaramin ƙunar zuciya ta kama Shahudah ba jin Jawaad ya shareta, ta turo baki gaba tana yaye bargon da take ciki.
Masha ALLAH na sake ambata ganin haɗaɗɗun kayan barcin da take sanye a ciki, sun mugun mannewa da farar fatarta, tare da zama ɗam jikin surarta tamkar dan ita aka halicci figigiyar rigar barcin da kaɗan ta gota mazaunanta, siririyace sai dai jikinta a murje yake alamar hutu, ba kowa ne zai ga Shahuda ya yarda ta haɗa jini da HAUSA FULANI ba, dan komai nata yafi kama da na masu jajayen kunnuwa.....
Saurin janyeta yay da ga jikinsa jin ta rungumesa ta baya yana kuma ɓata fuska, a matuƙar harzuƙe ya juyo yana sanya jajayen idanunsa cikin fararen nata masu cikar gashi da gira baƙa wulik a sama. Sam bazata iya jurar kallon cikin idonsa ba, dan haka ta wani yi farr da nata cikin salo irin na manyan yara da ke taƙama da wayewa.
Hanya kawai ya nuna mata ba tare da yace uffanba.
Yanzu kam ranta yakai maƙura da haushin wulaƙancin Jawaad, dan haka ta yamutse fuska cikin tsiwa ta taka gaban gadon ta saka silifas ɗinta masu taushi ta nufi hanyar fita.
Sai da ta kama hannun ƙofar ne ta tsinkayo Jarumar muryarsa na faɗin, “Saura idan kinje canma ki sake kwanciya kar kiyi sallar”.
Harara ta watsa ma bayansa da ya juya mata ta fice tana ƙunƙunin da ita tasan mi take faɗa.

Bai sake bi ta kanta ba ya kammala abinda zaiyi a gaban madubin ya nufi Wadrobe ɗinsa ya saka boxer kawai ya fito falo. Kayan tea da ke ajiye saman D/table ya nufa, ya ɗauki kofi ya haɗa komai kafin yaje ga disfensa ya matso ruwan zafi dai-dai buƙatarsa. A haka ya koma bedroom ɗinsa yana juya cokali cikin kofin shayin da keta tururi.
Zama yay bakin gadon yana shan shayin a hankali, ko zafinsa baya ma damuwa da shi. A da can sam baya shan shayi sosai, ya kan sha amma ba ko yaushe ba saboda baya cikin abinda ya damesa, amma tun bayan auren sa da Shahudah suka ƙulla abota da tea, a yanzu baya da abincin da ya bama muhimmanci a rayuwarsa irin shayi, tun yana sha akan dole harya fara zame masa jiki, inma bai sha ba sam baya jinsa dai-dai, a baki sunan kawai yana da matane, amma a aikace ita da hotiho babu banbanci, dan babu wani abu na matan kirki masu daraja da Shahudah ta iya, banda tsagwaron son jiki da son hutu babu abinda ta tara, a ɓangaren gyaran jiki dai kam gwana ce, dan ƴar gayuce ta gani kasheni, sai dai sam babu tarbiyya mai birgewa da akasan ƴaƴan musulmai da ita, komai nata kwaikwayone daga jinin yahudu da nasara, salla wannan sai yayi mata jan ido take yinta, daga lokacin da yay nisan kiwo kuwa a aikinsa baisan wace wainar take toyawa ba a ɓangaren bautar ALLAH....
A hankali ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana ajiye kofin hannunsa saman durowan gefen gadon, magani ya ciro a ciki ya sha kafin ya haye gadon da ke manne da ƙamshin turarensu ya kwanta yana jan bargon ya lulluɓe har kansa.

Koda Shahuda ta koma ɗakinta sam bataji gargaɗin Jawaad ba akan tayi salla, sai ma gado da ta faɗa tana ƙunƙuni wai baza tayin ba, a haukanta da gajeren tunani tunda Jawaad ya ɓata mata rai to itama saita ƙuntata zuciyarsa da ƙinyin sallar da yace tayi, dan haka tai kwanciyarta barci ya sake kwasheta saboda sanyin garin na ruwa da aka maka a daren jiya.

ALLAH ya ƙyauta to, saikace kabari ɗaya za'a saki da Jawaad ɗin Shahuda?🤔 kokuma shike bada sakamako idan anyi sallar🤦🏻‍♀️?, ALLAH ka rabamu da wayewa mara amfani⛹🏻‍♀️.

★★★★★★★
Chapter 2 · 0% Book details