← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 75

Sashe 42

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Jawaad ya baro office ya dawo gida ransa babu daɗi sam, ya kumazo ya iske Shahudah bata dawo ba, tsaki kawai yaja yay shigewarsa ɗakinsa, wanka kawai yay ya kwanta dukda masifar yunwar dake cinsa, amma gajiyar dake tare dashi har bishi-bishi yake ganin gari.
Yana kwanciya kuwa barci mai ɗan karen nauyi yay awon gaba dashi, bai sake sanin wane hali ake cikiba sai gabda sallar magriba.
A rikice ya tashi saboda salloli da suka wucesa, yay azamar yin ramuwarsu yana jero istigifari ga UBANGIJI.
Bayan ya idar yay shirinsa tsaf ya fice zuwa gidan kakansa daya haifi Mamansa, mijin kakarsa mama maryam kenan.
Ya iskesa yana da baƙi, dan haka bayan ya gaishe da baƙin yay wucewarsa cikin falon tsohon, kuloli yaci karo dasu, dan haka ya zauna yana buɗewa, yasan dai bai wuce tuwo ba, kuma daga gidan Ummansa ne ake kawoma baba, dan tunda mama maryam ta rasu bai sake aureba, shi kaɗai yake zaune a bunsa a gidan saisu idan sunzo.
Tuwonsa ya zuba yaci ya ƙoshi yanamai jin nishaɗi, yaushe rabonsa da abinci mai nagarta irin haka? Yanama zaton tun masar da umman ta aika masace.
“Kai ja'iri, tuwon nawa kake cinyewa?”. Baba dake shigowa ya faɗa yana harar Jawaad da wasa.
Dariya Jawaad ɗin yayi idonsa akan kakansa da tsufa ya kama sosai, “Haba mai ran ƙarfe kaimafa tuwon na gidan Umma nane, tunda kaƙi fita a gwaurantaka kayo mana amarya”.
Dariya sosai tsohon yayi, yasa sandarsa ya daki kafaɗar Jawaad da saida ya sosa wajen saboda zafi.
“Dan gidanku, ni da kai munada banbanci ne? Kaima da kake da matar baka da banbanci da tuzurun da baima taɓa aureba”.
Murmushi Jawaad yay yana ɗan taɓe bakinsa, saboda tsoho dai ya taɓo masa inda ke masa ƙaiƙayi, aiko bai bada amsaba ya miƙe yaje ya wanko hannunsa sannan ya dawo ya zauna.
Baba dake binsa da kallo yace, “Daga ina kake a darennan?”.
Jawaad ya zauna kusa da baba yana jingina kansa da kafaɗarsa yace, “Daga gida”.
Shafa kansa baba yayi yana maijin tausayinsa, yace, “Yau an tuna da tsoho kenan?”.
“Nikam dama kana raina, wani aikine kawai ya dabaibayeni sai yau na sauke nauyinsa”.
Murmushi baba yayi, “Naga komai ai a tv Jawaad, shiyyasa a kullum bana haufi a gareka, sai yanzu ne nake sake gaskta maganar mahaifinka da tun bakasan kanka ba yake dangantaka da aikin ƴan sanda, ashe shiya san miya hango mana”
Murmushi kawai Jawaad yay yana haɗiye abu mai ɗaci a maƙoshinsa, daga nan ya cigaba da sauraren yabo da kakansa keta jerawa akan ƙyawawan halayyar mahaifinsa, a haka barci ya sake sacesa.
Baba yakai dubansa ga fuskar Jawaad, ganin yay barci sai yay murmushi yana kai hannunsa ya shafa kumatun Jawaad ɗin.
Ido Jawaad ya buɗe a hankali ya kallesa, baba yace, “Tashi kaje ɗaki ka kwanta”.
Bai musaba ya miƙe ya shige bedroom ɗin baba, lafiyayyen ɗaki dayasha gyara tamkar bana tsohon da rayuwa taima nisa ba, lallausan gadon baba Jawaad ya haye, yaja bargo ya rufe jikinsa yana lumshe idanunsa, kafin kace mi nan nauyan barcin ya sake ɗaukesa kamar wasa.

Yau dai kam Jawaad anan ya kwana tare da kakansa, sai da yay sallar asuba ya karya da breakfast ɗin da Faisal ya kawo daga gidan Umma sannan yayma baba sallama ya tafi gida akan yana nan dawowa anjima zasuyi wata magana da baba.
Baba yace “to ALLAH ya kaimu saika dawo, ALLAH ya tsareka akoda yaushe”.
“Amin” Jawaad ya amsa yana fita.

_________________________
BAYAN SATI BIYU
_________________________

Har wannan lokacin Aunty Shahudah da dai na gida, bata komaba kuma mijinta bai zoba, sannan jack na nan bai tafiba sai kace gidan tsohonsa.
Nikam tun ranar da mukaci abinci tare ban sake zama inda yakeba, saboda har ɗaki ta biyoni ta ƙaremin zagi da cin zarafi akan ko Dad ne ya kuma buƙatar na zauna dasu cib abinci nasan yanda zan zame, idan ba hakaba wlhy saita ci mutuncina.
Haƙuri kawai na bata nikam, dan yanzu ni bana ɗaukarta sahun masu isashen tunani.
Tamin wannan abun ma da kwana uku Dad yace na shirya zuwa makarantar da zanje na zana jarabawata, ranar dai kamar anmin gafara naji, har kukan daɗi nayi kuwa.
Kwana biyu na cika na tattara komai na sayayyar da Dad ya yo mani domin tafiya, dan makarantar boarding school ce, sai dai yanda naji su Aunty Aamila na faɗin wai ban dace da makarantar ba nasan babbar makarantace.
Ranar dazan wuce na lura kowama murna yake da tafiyata, dan Salman harda faɗin, “ALLAH raka taki gona, koba komai sa huta da kallon baƙar fuskata abin amai”.
Dariya mummy da aunty Aamila suka sanya, dan mu kaɗaine a wajen, Shahudah da jack suna can baya suna hira.

Har bakin mota Amina da kuku sukai min rakkiya, sai da sukaga na shiga mota mun fice a gidan sannan.
Na share ƙwallar data zubomin ina murmushin kewa da farin ciki.

😅👏🏼ALLAH ya bada nasa takwara, sai dai fa ni ƴar team Shahudah ce😆😜, bara na fece kafin naci mazga⛹‍♀.

_________________________

Tunda Jack ya bata shawarar zubar da cikinnan burinta ya dawo sabi fil, dan ya tabbatar mata Jawaad burga kawai yake mata babu wani sakinta da zaiyi tunda yana masifar sonta.
Ta shafa cikinta da ayanzu haka yake mata ciwo, tabbas tana wahala akan wannan cikin da bata shiryama zuwansa ba, gashi harya fara sakata ƙiba, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, duka shekarunta nawa da za'ace ta ɗauki ciki? Kamar yanda Jack ya faɗa, ita kanta tasan dan tayi gaggawar yin aurene kawai, bakomai ya jawo hakanba kuma sai ƙaunar Jawaad data tunzurata, da shawarar Mummynta, anya kuwa bazata zubarba kawai ta huta? Iyakaci dai ayi badakalar da za'ai na ɗan lokaci ta wuce, daga baya komai zai lafa a wuce wajen.
Zama tai a bakin gado ta dafe kanta tare da cije bakinta saboda murɗawar da cikinta ke mata, kusan min tuna uku tana a haka kafin ta samu ya lafa mata, sai wani zazzaɓi da takeji wanda ya zame mata jiki a yanzu kullum yamma saita yisa.
Wayarta ta ɗauka ta kira Aamila, babu jimawa sai gata ta shigo ɗakin.
“Sisi lafiya kike kirana?”.
Miƙewa Shahudah tayi idonta akan Aamila, “Aamila na yarda da shawararku zan zubar da cikinnan kawai”.
Zaro ido Aamila tayi tana ɗan ja baya, “Wai da gaske dan ALLAH?”.
“Na taɓa miki maganar hakan?”.
“A'a, ai abunne da mamaki, keda kike mugun tsoron Brother Jawaad karya rabu dake, amma yanzu lokaci ɗaya kizo da batun amincewa”.
Tsaki Shahudah taɗanyi, “Karki damu, ni nasan barazanace kawai, son da bb kemin bazai taɓa yarda ya rabu daniba wlhy, kawai yanamin burgane dan karna zubar, idan kuma yay haƙuri nan gaba ai zan haihun, amma gaskiya ba yanzu ba”.
“Kinyi ƙyan kai gaskiya, yanzu ke mikike buƙata?”.
“Shawarar da nake buƙata kenan daga gareki, ɗazun jack yace yasan maganin da zaimin aiki ba tare da nasha wahala ba, inaga kije kufita tare kozaku samu a wani pharmacy ɗin, sai dai dan ALLAH karki bar Mummy ta sani”.
“Karki damu, insha ALLAHU babu wanda zaiji”.

Koda Aamila ta fice sai Shahudah ta koma ta zauna, wayarta ta ɗauka ta dannama Jawaad kira, sai dai harta katse bai ɗagaba.
Text massege ta tura masa kamar yanda suka shirya da jack, kodaga baya cikin ya zube wai bazai zargeta akan itace ta zubarba.
Mummy batasan mi suke shiryawa ba, a gabanta Aamila da jack suka fita a gidan.
Sun bazama neman maganai cikin manyan pharmacy's ɗin garin, amma samunsa ya gagara, saboda ba kowane ke saidawa ba, dabara ce ta faɗoma Aamila a rai ta kira number Munira cikin yaran gidan su Jawaad, dan ta taɓa bata labarin wata ƙawarta da ta raka zubar da ciki.
Sun sanar mata abinda suke buƙata sai dai basu faɗa mata gaskiyar wanda zaiyi amfani da shiba, itace ta kira likitan daya bama ƙawarta wancan maganin ta haɗasu dasu Aamila, shi kuma yay musu kwatancen inda zasu sameshi.
A asibitinsa da ya kasance privet suka samesa, babu ko ɗar suka biya kuɗin daya yanka musu ya basu allurar da za'ai amfani da ita, a cewarsa itace tafi aiki shap-shap kuma bata cutarwa.
Sai da jack ya duba sukkan bayanan allurar ya kuma tabbatar da maganar Doctor sannan ya suka amsa suka nufi gida.

Jack bashi da shamaki da shiga ɗakin Shahudah a duk sanda yaso, dan haka koda suka dawo a gaban idon Mummy ya shiga, Aamila kuma ta zauna a falon dansu ɓadda hankalin Mummy wai.
Ƙudundune ya iske Shahudah zazzaɓi ya rufeta, ya yaye bargon data rufa yana taɓa gefen wuyanta, buɗe idanunta tayi, ganin jack ne yasata miƙewa da ƙyar tana kallonsa, “Kun samo?” tambayar data fara jefa masa kenan cikin harshen turanci.
Kansa ya ɗaga mata, ya ciro allurar daga aljihunsa yana nuna mata.
Amsa tayi ta jujjuya allurar a hannunta, sai kuma ta kallesa da tambayarsa wai miyasa basu sayo maganinba? Yafasan batason allura.
Bayanin duk yanda sukai ya bata, ya kuma tabbatar mata wannan allurar tafi maganin inganci, hakan ya saka ta aminta da batunsa.
Hannu ta bashi yay mata allurar tana matse baki, can ƙasan zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai biyo baya daga Jawaad.............✍🏻

*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
Chapter 42 · 0% Book details