← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 75

Sashe 11

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shahudah na a falon kwance cikin kujera, ga kiɗa mai taushi ya na tashi ta cikin sifikun da aka ƙawata falon dasu, sanye take cikin wando da riga masu azabar ƙyau kalar ruwan hoda, kasancewar kayan robane sunyi mugun bin jikinta tamkar da fatarta aka haliccesu, wandon iyakarsa gwiwa, sai rigar da bata rufe mata ko cibiya ba, dan ƙyau tayi ƙyau sosai, dolene ka kalleta ka sake kallo.
Gaban ɗayan imaninta nakan waya ɗinta da take cheating, gefe ɗaya tana sauraren waƙa.
Har Jawaad ya gama sakkowa bata sani ba, sai da mayen ƙamshin turarensa ya bugi hancinta ne ta ɗan lumshe ido tana zuƙarsa kafin ta buɗe ta yunƙura ta tashi zaune, ƙyawawan fararen idanunta a kansa.
Shima idanun nasa na kanta, dan kwalliyar tata ta masa ƙyau, sai ya ji kaso mafi yawa na haushinta ya ragu a zuciyarsa, sauran cake ɗin da taci ta rage da kofin da ta sha tea ya kalla ya kauda kansa, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yana sake haɗe fuska.
Murmushi Shahudah da ke kallonsa tayi, dan sam ita bata da riƙo, dama ko faɗa sukai zai ta shareta, itako mintuna kaɗan ta manta sai kuma an sake wani.
Yanzu ma dai hakan ita harta huce, hakanne ya sata tasowa ta shige jikinsa tana magana cikin shagwaɓa.
“Oh My BB kayi ƙyau sosai”.
Shiru yay mata, bai kuma rungumetanba shi.
hakan yasa ta ɗago tana kallon fuskarsa, ta kai lallausan hannunta tana shafa fuskar tana murmushi, “BB kamin murmushi mana”. ‘Ta ƙare maganar da sumbatar laɓɓansa’.
Duk da saƙonta ya shigesa hakan bai hanashi ture hannunta ba daga fuskarsa yana ƙoƙarin janyeta a jikinsa, amma sai ta ƙankamesa tana bubbuga ƙafa cikin shagwaɓa.
Iska ya ɗan huro da ga bakinsa, a daƙile yace, “Wai mikikeyi haka kamar wata tata Hudah? Ki bari karkimin Squeezing kaya”.
“Sai ka sake fuskanka to” ‘ta sake faɗa a raunane’.
Kansa ya girgiza kaɗan yana riƙota sosai jikinsa, hakan ya saka Shahudah ɗago fuskarta cike da annuri ta kallesa, shima kallonta yake cikin ido yana kuma narke idanunsa dake ƙara tsundumata a ƙaunarsa.
“Idan kinaso ki sameni yanda kike buƙata Hudah ki canja kamar yanda nima nake buƙata”.
Yay maganar a hankali tare da sauke laɓɓansa akan nata da keta walƙiyar janbaki, ya sumbata.
Kafin ta samu zarrar magana ya cireta a jikinsa ya nufi hanyar fita yana saka baƙin Eyeglasess ɗinsa a ido ba tare da ya sake koda kallonta ba.
Murmushi Shahudah tayi tana wani juya idanu, tabbas tana ƙaunar Jawaad fiye da hasashen mai tunani, dan shine namiji da ta fara so a rayuwarta, so kuma na haƙiƙa mai cike da tsagwaran sadaukarwa, kuma tana fatan ƙare rayuwarta da ƙaunarsa. Matsala ɗaya da ke tsakaninsu shine banbancin ra'ayi, Jawaad ɗan gayune mai aji da cikar haiba, duk yanda kake tunanin haɗuwarsa ya zarta nan, amma tana mamakin yanda kansa yake a tukunya game da rayuwa irinta manyan yara, ta ɗan taɓe bakinta tana komawa cikin kujera ta zauna, tasan canjawarta ta koma ra'ayinsa abune mai matuƙar wahala da iyawarsa a gareta zaiyi wuya, su dai tafi a hakan kowa da ra'ayinsa zaifi basu zaman lafiya, kan ya matsa sai ta canja ɗin dai-dai da buƙatarsa.

★★★★★★

Ya isa Office ɗinsa da ya ƙawatu da kayan more rayuwa, sai ƙamshi mai daɗine ke tashi a ciki, ya zauna cikin kujera yana mai miƙa hannunsa domin karɓar takardun hannun wanda suka shigo tare. Shafin farko da ya buɗe ya maida ya rufe yana ɗago razanannun idanunsa, “Ina na farkon?”
Ya faɗa cikin karsashi.
Cikin ɗan ruɗewa da tambayar bazata Aminu ya shiga kame-kame, “S...o...so...sorry sir!, dama Sir Qaseem ne ya karɓa, sai yace na kawo maka waɗannan”.
Gira ɗaya Jawaad ya ɗage sama, ya janye idanunsa da ke neman fara canja launi ba tare da ya tankama Aminu ba, cikin nuna halin ko in kula ya mai da hankalinsa ga Computer ɗin da ke saman desk ɗin gabansa.
Tsawon wasu mintuna da basu gaza biyar ba Aminu na tsaye, babu abinda jikinsa keyi sai tsuma, zufa ta hudo dukkan ƙofar gashin da ke jikinsa.
Jawaad dake aikinsa ya kallesa ta wutsiyar ido yana faɗin, “Tsayuwar ka zaɓa ko komawa dasu, idan ka karɓo waɗancan ka haɗa ka kawo min?”.
Sosai tsantsar firgici ya kuma bayyana a fuskar Aminu, ya sharce gumin da ya tsatstsafo masa a goshi tare da gyara tsaiwa zaiyi magana.......
Wani mugun kallo Jawaad dake ƙoƙarin miƙewa ya watsa masa, ba tare da yace uffanba ya zagayeshi ya fice da ga ma office ɗin gaba ɗaya.
Da tsantsar sassarfa ya biyo bayan Jawaad da ko kallonsa baima sake yiba.

Mutanensa biyar na amana suka take masa baya zuwa Office ɗin boss ɗinsu, yayinda Aminu ya bi hanyar da zata sadashi ga ubangidansa Qaseem Ali.
Yardar dake gareshi ga manyansa sam ta hana masa shamaki da neman izinin shiga ofisoshinsu, kansa tsaye yake shiga ba tare da jiran iso ba. Sai da yay masa sarawar girmamawa tamkar yanda al'adar jami'an tsaro take, kafin ya zauna a ɗaya da ga kujerun gaban ƙaton tabirin.

“Jay!”.
“yes sir”.
“Ko kasan maganar sace Alhaji kokino tana neman shigo da shugaba ƙasa a ciki”.
Cikin rashin fahimta Jawaad yace, “Sir! Kamar ya kenan?”.
Shiru ogan yayi na wasu sakwanni, kafin ya ɗago kansa daga wayar da yake dannawa ya maida kallonsa ga Jawaad, wayar ya miƙa masa yana faɗin, “Ɗazun nai magana da shugaban ƙasa kai tsaye babu shamaki kowa a tsakaninmu”.
Idanu sosai Jawaad ya zaro waje, “Sir, miya ce?”. ‘Jawaad yay maganar a hankali, mai nuna alamar tsorata’.
Kaɗan Sir Ahamad barewa ya buga tebirin gabansu yana huro iskar bakinsa, ya miƙe tsaye tare da maida dukkanin hannayensa baya ya goya, sai da yay taku biyu zuwa uku kafin ya juyo ga Jawaad, “Jay! Adadin lokaci, lokaci shugaban ƙasa ya bamu na gaggauta samo Alhaji Sadi kokino, abinda ya bani mamaki annan yanda ya tsaurara, mika fahimta?”.
Jawaad dake bin ogansa da kallo kamar ya samu magiji ya sauke numfashi, tare da taɓe bakinsa yana murza yatsun hannunsa da ke bada ƙarar ɗas-ɗas a hankali, zuwa kusan sakon goma sha biyar sai kuma yaɗan zabura, cikin ƙanƙance idanu mai nuni da na tuno, yace, “Sir sai naga kamar yana tunanin ana zarginsa da hannu a ciki....”
“Exactly my dear!, nima wannan shine tunanina, Jay kana da ƙwaƙwalwa, shiyyasa a komaina nake sonka a gaba” ‘Sir Ahmad ya ƙare maganar yana komawa a kujerarsa ya zauna’.
Jawaad dake murmushin jin daɗin yabon da ogan nasu yay masa, ya sauke numfashi yana gyara zama, “Sir inada shawara”
Sir Ahmad dake kallonsa yace, “ita mukafi buƙata ai ayanzu Jay”.
Jawaad ya lumshe idanunsa tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana jinjina kansa, “Zan turo maka a rubuce Sir”.
“Okey babu damuwa Jay, yaya maganar zaɓin haɗa runduna?”.
“Sir zanje na zauna dasu Asim yanzu insha ALLAH, zuwa yamma zamu aiko da jadawalin sunayensu”.
“Okey, amm......”
Maganar Sir Ahmad ta kakare dalilin Knocking ƙofa da akayi, haɗiye maganarsa yayi ya bada izinin shigowa........

*______________________________________*
*BILKEESU*
*______________________________________*
Chapter 11 · 0% Book details