← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 75

Sashe 59

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe, koda na idar da sallar asuba ban kwantaba, nai dukkan shirye-shiryen daya dace na fidda kayana waje, ɗaki na dawo nai wanka sannan na shirya tsaf na fito.
Nasan dai driver zai kaini, dan haka na nufi wajen motar dana kai kayana.
Cikin girmamawa yace, “Ai kayan suna can” yay maganar da nuna motar Qaseem.
Da mamaki nace masa, “Can kuma? Mikuma ya maidasu can ɗin Nura?”.
“Yallaɓai Qaseem ne yace a maida”.
Kafin na bashi amsa takun takalman Qaseem suka katseni, ba tare daya kalleni ba yace, “Malama ki zagaya mota sauri nake inada wajen zuwa”.
Tamkar na zauna naita ƙwaɗa ihu haka naji, dole nabi umarninsa naje na shiga inda ya buɗemin da kansa bayan ya shiga.
Haka muka tafi tamkar kurame, sai lokaci-lokaci yakan jani da hira, wata na amsa da baki, wata nace, “eh ko A'a”.
Da haka muka iso.
Da kansa ya fito ya taimaka min muka shiga da kayan, ba tare daya zaunaba yace zai wuce.
Sake rakosa nayi wajen mota nai masa godiya.
Harya tada motar sai yace na bashi wayata.
Bashi nayi ina ƙunƙuni a zuciyata, duk da bansan miyayi da itaba naji a jikina number ta ya ɗauka, ya haɗo wayar da kuɗi ya miƙomin.
Zan zare wayar ya harareni, dole na haɗa da kudin na amsa nai masa godiya.
★★:★★:★★
Tun daga wannan lokacin abubuwa suka fara sauyawa tsakanina da Yah Qaseem, tun yana kirana lokaci-lokaci harya fara komawa kullum.
Banaƙin ɗauka, dan koba komai matsayin yaya yake a gareni, sannan banjin zan iya tozarta zuri'ar Dad, Yah Qaseem kuma namijin da kowace mace zata iya sone, dan akwai ƙyawu, yana aikinsa, tunda nake dashi ban taɓa kamashi da wani abu mara ƙyauba, sai dai idan a ɓoye yake kayansa, wannan kuma ya rage nasa ai, matsalar sa dai rashin ilimin addini, wanda gaba ɗaya ɗiyan dad ya zama babban tawaya wa rayuwarsu, tsagwaron wayewarce kawai da duniya suka sani.
Munja kusan shekara ɗaya da rabi a haka, shi baice yan sonaba, sai dai alamomi, dan duk randa ya bushi iska zaizo busting ɗina da kaya niƙi-niƙi, zanma ce yafi kowa ziyarata a gidan, idan kuma naje hutu yata bani kulawa kenan harna taho, ko wani abu Aamilah ko Salman sukaimin sai yayi magana a yanzu.
Kulawar da Yah Qaseem ke bani a yanzu na kula tana ɓata ran Mummy, duk da dai bata magana ni nakan hasaso ɓacin rai a fuskarta.
Ni kaina take-takensa suna tsoratani, dan ni dai nasan yafi ƙarfina ta kowanne fanni, duk da canjin dana samu a rayuwa bansama raina zan samu koda wanda bai kaisaba matsayin miji, ni dai kullum addu'ata ALLAH ya bani nagari da zai zamarmin mijin marainiya.
Muna shekara ta uku a makaranta Yah Qaseem ya fiddo manufarsa fili a kaina a kaina, dan kuwa ya tabbatar min shifa sona yake.
Na shiga tsantsar ruɗani da wannan furuci, duk da na daɗe ina hasashen haka, dama a lokacin munje gida weekend ne, ALLAH ma ya soni ana gobe zan komane, aiko washe gari baisan na gudu ba.
Koda na sanarma su Ummie sai sukaita zugani akan na karɓa masa, dan Yah Qaseem ya cancanta, idan kuma bana sonshine to, amma sun daɗe su dama suna hasashen akwai wani abu a ransa game dani, sudai suna bani shawara nai amfani da damata gaskiya.
Ni dai kasa cewa komai nayi, dan idan nacema banson Yah Qaseem nayi ƙarya, ya fini komai a rayuwa, sannan ya cancanta a soshi, amma idan harna amsa to na ɗeboma kaina gagarumar rigima daga ahalinsa, musamman Mummy da tunkan ya furtama take ƙyamatar abun, inaga yanzun yace yana so.
Bai sake bi takaina akan sonjin amsar na aminceba koni ina sonsa, ya dai ƙara ninka kulawarsa kaina fiye da ta baya.
Yana cigaba da sakani sakin jiki dashi ba tare dana saniba nima.
Shi dai Dad koda ya fahimta baice komaiba, amma Mummy ƙiri-ƙiri ta nuna bazata saɓuba, hakama Aamilah da Salman.
Wannan soyayya ta Qaseem ce ta kuma ƙirƙirarmin samubawar tsangwama da tsana a gidan, a wajen Dad da yah Qaseem kawai nake samun sassauci, gashi Dad ba mazauni bane.
Cikin wannan yanayin tsangwama muka shiga shekarar ƙarshe a makaranta nida ƴan uwana guda huɗu.

______________________
JAWAAD
______________________
A ɓangaren Jay kuwa komai yana tafiya dai-dai, sai dai yau da gobe ba'a kiranta da nasara ko farin ciki ɗari bisa ɗari, dolene wataran tazo da daɗi, wataran saɓanin hakan.
Yana shekara ta biyu da rabuwa da Shahudah wani cigaba na musamman ya zomasa shida tawagarsa, dan kuwa wani horaswa ta musamman aka turasu zuwa ƙasar amuruka.
Duk masoyinsu dolene ya tayasu murna, inda ka cire irinsu Qaseem da suka gaza ɓoye hassadarsu akan maganar.
Dan kuwa dai kowa yasan badan matsayin kujerar Jawaad ta kai bane ya samu wannan cigaba, cancantace kawai da ƙwazonsa ya kaisa.
Da yake tafiyar gaggawace sai basu wani zaman ɓata lokaciba suka fara shiri, horarwas zata zama ta shekaru kusan biyu ce, amma bawai lallai su cika biyunba cif-cif, dan a ƙa'ida ma shekara ɗaya da rabine, sauran watannin da zasu biyo baya na wani tsarine daban.
Hakan yasaka su Aliyu duk da iyalinsu zasu wuce, Rose da Jawaad ne kaɗai babu mahaɗi🥴😂.
Ya sanarma Uncles nashi gaba ɗayansu, sun masa fatan alkairi kuma tare da addu'ar samo nasara.
Sai kuma shawarar mizai hana ya zaɓi ɗaya a yaran dangin a ɗaura musu aure ya tafi da ita, dan ba girmansa bane zama babu mace sam gashi har yana a shekara ta biyu da rabuwarsa da Shahudah, musamman a ƙasa irin wadda zaije yanzun akwai damuwa.
Bai wani jasu da nisaba ya nuna musu suyi haƙuri, maybe zuwa nan gaba idan bukatar hakan ta taso koda yana a cannne zaiyi magana.
Aiko wannan furuci nasa ya sakasu rabama ƴaƴansu lambarsa suyo farautar zuciyarsa bayan wucewarsa daya kirasu ya tabbatar musu ya sauka ƙalau.
Ko Baba ma sai da yay masa maganar auren kafin ya wuce, dan dama yana yawan masa shi dasu Umma, amma a koda yaushe yakan basu haƙurine da daɗin bakin su ƙara masa lokaci, bayason a sake tafka kuskuren baya kamar aurensa da Shahudah.
Sun masa fatan alkairi da addu'ar dacewa da mace ta ƙwarai da nasara akan abinda zashi nema.
★★★★★★
A ɓangaren Shahudah kam taci alwashin sai Jawaad yazo ya nemeta har inda take, dan a nata hasashen gwala rayuwarsa take a haka.
Tasan ɗunbin son da yake mata dolene ya jigatu da rashinta, shekaru biyar ta ɗiba masa cif, sai ya koma ƙaramin mahaukaci a kanta sannan ta bayyana a garesa.
A shirmenta ko ganin ta cinye shekaru biyu bai nemetaba baisa taji a ranta akwai matsalaba, a'a a ganinta kawai ya rasa hanyar da zai iya ganintane, tunda Mummy ta tabbatar mata Jawaad baisan inda takeba har yanzu.
Ita kuma duk motsin Jay Mummy tana sanar mata komai harma Aamilah da Salman, wani lokacinma harda Qaseem, ko dangane da tafiyar Jawaad Qaseem ne ya sanar mata komai.
A duk sanda akai mata zancensa danne zuciyarta kawai takeyi, amma kewarsa da ɗunbin begensa kullum sake mamaye zuciyarta yakeyi, batason ya kalleta matsayin mafi arha a mata shiyyasa tai dauriyar riƙe ajinta gam tunda ta ƙetaro kasarsu tai kunnen uwar shegu dashi, sai dai a kullum hotonsa shine abin kallonta, hakama duk wata kafar yaɗa zumunta datasan yanada accaunt a wajen tana bibiyarsa da sunan da ba nataba.
Ta kasa kula kowane saurayi, ta dai yarda kuyi abota amma ba soyayyaba, to kuma dama can dai gaskiya Shahudah bata iskanci, koshi Jay shaidane akan cikakkiyar budurwa ya sameta, dama can iskancinta baya wuce shan minti, amma bata yarda tarayya da waniba, takance wannan mallakin Jay ne tunma a wancan lokacin, to a yanzunma dai da harma yanzu take ɗauka da aurensa kanta tana taka tsantsan, sai dai fa iya shege da duk wani dandali na taruwar wayayyu tana a wajen babu abinda ya dameta, tunda bawai muhimmancin auren ta saniba balle ƙa'idojinsa, a ganinta duk abinda takeyi ƴancinta ya bata damar yin hakan, balle ta dawo inda babu ruwan wani da wani.
A gurguje⛹♀😏
_________________________
BILKEESU
_________________________
Rayuwa tai nisa, sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun zama yini, yini ya rikiɗa dare, kafin wani dogon nazari daren ya haɗa kwanakin da suka bada satittikan da suka dunƙulle wattani, sai gamu da shekara ɗai-ɗai har huɗu cif a makaranta, yanzu haka jarabawa biyu kacal ta rage mana kammala jarabawar ƙarshen zangon karatunmu na.
Abubuwa da dama sun faru, wasu a iya tunawa, wasu ko zuciya ta manta saboda hidimomin yau da kullum, mun kwankwaɗi madarar ilimi wadda muke addu'a da fatan ta zamewa rayuwarmu dana ƙasa damu alkairi.
Zakusha mamaki idan kukaji a cikin baƙin al'amuran da suka zoma rayuwata ciki harda soyayyar Yah Qaseem datai ƙarfi a tsakaninmu,
Hoo duniya makarantar makaho, kai mai idonma ba ɗage masa ƙafa takeba, wai ni Bilkisu ƴar baƙa mummuna ƴan ƙwalisar samari masu ji da ƙyawu da ƴan canji a aljihu irinsu yaya Qaseem keso? To lallai dai abin da mamaki, sannan yana buƙatar alamar tambaya, shin sone na gaskiya? Kokuwa sone na sha'awa?.
A wannan kaftawar da zamu farane kawai kowa zai iya fahimtar hakan, danni dai har yanzu baiji amsa tayinsa daga bakina ba.
Dan duk wani salon rayuwa da iya zama da jama'a a yanzu Alhmdllh na san gwargwadon ilimin da UBANGIJI ya bani.
Maza da yawa surar da ALLAH ya bani ke ɗibarsu zuwa gareni, ba wai ƙyawuba, duk da ƙoƙarin killace jikina da nake ban tsiraba a wajen mayu irinsu Yah Qaseem................✍🏻
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻[8/11, 5:00 PM] Marsy😘: https://youtu.be/gUGygQ5y5pg

*_MANHA HAUSA NOVELS_*

https://youtu.be/xUINNiDdeH0

*_AL-ƘALAMI TV_*

*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_

*_____________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na talatin da ɗaya_
*_____________________________________*
Chapter 59 · 0% Book details