← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 75

Sashe 56

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

............Ɓangaren su Shahudah ma komai ya caɓe, gashi ma tunda suka fito bata da wani isashshen lafiya, su Mummy kuma sun kasa sanar mata maganar sakin da Jay yay mata.
Jack kuwa washe gari jirgin farko dashi ya tashi.
Abu ya tsayama Dad sosai a zuciya, idan ya zauna yakan tafi dogon tunani game da kalaman Jawaad da yace jahilci na rashin ilimin addini ke ɗawainiya da Shahudah.
Maganar nan na matuƙar sukarshi, dan ya tabbata gaskiya Jawaad ya faɗa, sam a tarbiyyar yaransu babu ilimin addini a cikinta, rabon da yaransa suje islamiyya tun suna ƙananu, irin rayuwar da suka buɗa ido da ita kuma saita goge musu komai, musamman ma daba maida hankali akai ba sanda sunada ƙarancin shekarun, amma yanda yaro bai cika manta abuba dasun tsura da wani abu, koda yake masu iya magana kance duk abinda ba'a tuni a cikinsa yakan lalace ko a canja masa manufa ma baki ɗaya.
Maimakon ya ɗauki mataki akai ko ya zaunar da Shahudah harma da Aamilah yay musu faɗa, ya kuma gyara kuskuren da yay tun farko na sakaci da gidansa, sai ya yanke shawarar tura Shahudah wata ƙasa wai ta huta ko hankalinta ya kwanta.
Koda ya samu Mummy da shawarar tura Shahudah sai ta nuna masa hakan shine dai-dai,
“Wannan shawaran tayi Dadynsu, ni kaina fargabar tunkarar Mamana nake da batun sakin nan da yaron nan yayi, amma idan ta tafi ta huta hankalinta ya dawo jikinta koda tasan babu auren bazata saka kanta a damuwaba, duk da dai munama fatan kafin lokacin ya sakko ya maida auren nasu, kokuma kawai ta koma makaranta acan ɗinma”.
Numfashi mai nauyi Dad ya sauke, yay ɗan gyaran murya kaɗan yana faɗin, “Shikenan to, amma k kina ganin yaron nan zai sakko kuwa? Kigafa abinda ya aikata, yama yanke kowacce alaƙa daku ɗin kanku”.
“Humm ai saima kaga yanda ya rufe ido wlhy, ai ban taɓa sanin Jawaad haka yakeba, dukkan halin mahaifinsa shine tattare dashi, kaita musu abu suyi kamar basu damuba, rana ɗaya saisu birkice maka”.
Murmushi Dady yayi kawai bai iya cewa komaiba.

Kwana biyu dayin wannan maganar Daddy ya samu Shahudah da kansa yay mata bayanin shawarar da suka yanke, amma sun nuna mata zata tafine ta huta har lokacin da Jawaad zai sakko daga fushin zubar masa da ciki da tayi.
Shahudah batayi musuba, dan a ganinta hakan shine mafita a gareta, a yanzu komi zatayi Jawaad bazai saurareta ba, to garama taje ko makarantar ta koma ma ta ƙara karatun zaifi.
Qaseem shine yay tama Shahudah kiciniyar tafiyar har komai ya kammala, ranar da zata wuce tata kiran Number Jawaad amma bai ɗagaba, ta tura masa text message na ban haƙuri shima babu reply, ranta dai duk a jagule ta wuce, taso su haɗu da Jawaad ɗin Qaseem ya balbaleta da masifa, dole ta haƙura tadai rubuta saƙo ta barma Aamilah akan koda nan gabane ta bama Jawaad ɗin.
Ita dai Aamilah ta amsane kawai, amma bata da tabbacin iya badawar, dan ko'a mafarki yanzu bata fatan sake haɗuwa da Jawaad, itama karatun zata samu ta koma tama bar ƙasar yafi mata kwanciyar hankali.

_________________________________

Duk da Jawaad yaga kiran Shahudah da saƙonta bai kulaba, kuma sarai yasan da shirin barin ƙasar da take, amma sai yay tamkarma baisan anaiba, abinda ke gabansa kawai yakeyi.

*_BAYAN WATANNI BIYU😹🥴_*

Zuwa yanzu komai ya lafa tsakaninsu Jawaad, duk da dai ta ciki na ciki akeyi, bai sake bi takan labarin Shahudah ba balle bibiyar inda take kokuma mi takeyi?.
Sai dai akan barin gida da share kowa a danginsa baba ya gyara wannan alaƙar, dan dakansa yaje gidan yakuma saka Jawaad zuwa dan dole.
Dukansu ya haɗasu yay musu nasiha akan zuminci da muhimmancinsa, tare da nuna musu illar wanda yazama silar rarrabewarsa. Dukansu jikinsu yayi sanyi har Jawaad ɗin, domin kuwa shima yasan hakan, tunda yanada ilimin addini sosai, har a yanzu ma bawai ya bar nema bane, take sani kawai yayi da kuma tauna aya dan tsakkuwa taji tsoro.
Da kansa ya nema gafarar Uncle's nashi ya kuma basu haƙuri.
Suma suka bashi haƙuri akan kuskuren da yake gani sun masa. Yace shi basu mashi komaiba, dama dai akan maganar cikin Shahudah ne da duk suka kasa fahimtar an cuta masa suka goyi bayanta.
Sunta baza ido da kunne suji kozai maido musu dukiyarsa daya amsa da kuma maida aurensa da Shahudah sai dai baice komaiba, da Uncle Nasir ma ya takalo masa maganar aure akan bai ƙyautu da mutuncinsa ya zauna babu mataba, cayay suyi masa afuwa akan wannan maganar, maybe zuwa nan gaba kaɗan yayi.
Sunso masa tayin ƴaƴansu sai dai bai bada fuskar hakanba, shiyyasa suka ɗaga masa ƙafa akan sai zuwa gaba.
Shi baima san sunaiba, kwana huɗu da yin wannan zaman Baba ya takura masa sai da ya dawo gidan da zama, randa ya samu dama yakanzo nan ya kwana, wataran kuma acan Barrack nasu yake kwana abinsa, kokuma gidansa, ya dai raba hankalinsa uku babu gaira babu sabar.
Sai dai shima hakan yanacin ransa, yasan da mahaifiyarsa na tare dashi wannan rashin tsayayyyen muhallin da bai samesa ba, dan duk inda take shima anan zai kasance dole.
Ga dai Jawaad ya dawo gidansu da zama, amma zaman sai ya banbanta dana fil azal da yayi, ya ɗaukarma kansa duk safiyar daya kwana a gidan zai shiga ya gaida tsoffin gidan biyu da suka rage, wato su mama Atika, idan yaga yanada isashshen time zai shiga duka sashen Uncles nasa suma, idan bai da kuma shikenan.
A ɓangarensu kuma suma duk sun saka yaransu mata farauto zuciyar Jawaad, kowa burinsa ƴarsa ta samu karɓuwa ga Jay a aura masa.
Sai dai kuma an samu matsala, shi Jawaad ma yaran gidan basu ishesa koda kalloba, yanzu hakama bazai iya kawo sunan wasuba kansa tsaye, yawancin sanda suka taso shi kuma baya gidan yana harkokin karatunsa da wasu abubuwan, amma duk waɗanda ya tashi dasu daga ƙuruciya duk ya sansu yasan sunayensu, to duk sunyi aurema matan, hakama mazan, da yawansu kuma yana gaisuwa dasu ta waya time to time idan sun kirashi.

_________________________
BILKEESU
_________________________

A yau muka tashi da farin cikin da baki kaɗai bazai iya furtawaba, dan kuwa mun zana jarabawa ta ƙarshe zamu koma gidajen iyayenmu, gashi dai yau ranar farin cikice ga kowacce ɗaliba, amma mu saita zamar mana ranar kuka nida ƙawayena su Ummie.
Mun haɗa kai a waje guda munata rairawa abin tausayi, Dadyn Ummie na daga gefenmu yana lallashi, duk sun bani adireshinsu, nima na basu nawa, su dama duk sun san gidajen juna iyayensuma nata zuminci.
Kowacce anzo ɗaukarta daga gidansu, niko Dad ya cema Dadyn Ummie ya kaini, bayan duk tafiyar sauran muka rage ni da Ummie kawai, sai da Dady ya gama kimtsawa muma ya ɗaukemu muka tafi, lallai zanyi kewar makarantar nan, har mukai nesa da ita ban daina kallonta ina hawaye.

Sun kaini har cikin gidanmu, wato gidan Dad, dan a yanzu shine kawai zan bigi ƙirji wajen kiransa gidanmu, tunda ƙaddara ta mallakaminshi matsayin gidan.
Amina ta fito a guje ta ƙadandaneni tana ihun murna, shima kuku sai washe haƙwara yake shi da baba mai gadi damai kula da flowers ɗin gidan, Su Dady basu shigaba suka juya akan nanda kwana biyu zai kawo mani Ummie.
Sai da naji ƙwalla ta cikan idanu, har suka fice ina ɗaga mata hannu itama tana ɗagomin, su Amina suka kwashi kayana zuwa ciki.
Duk da babu wanda ya fito domin tarbata a cikinsu ni ɗokin ganinsu nakeyi, sai dai kuma falon tsit babu motsin kowa, to yanzu dai kunsan wannan ba Bilkisun da bace da suke ɗauka bagidajiya, nima na sake ilimin rayuwa dana zamantakewa, cikin tsantsar son ganinsu na fara kwala kiran sunansu ɗaya bayan, Aunty Aamilah ce ta fara fitowa tana faɗan wake ƙwala mata kira haka? Cikin yatsine fuska.
Bamma sauraretaba na rungumeta, taso tureni a jikinta, amma sassanyan ƙamshin data shaƙo daga gareni ya sakata fasawa, nace, “Aunty Aamilah i miss you so much, irin mai zafin nan, mai hana barcin nan”.
Babu shiri tai dariya tana ƙaremin kallo sama da ƙasa, “Gaki dai kin canja kamar ba keba, sai dai shirman na nan kaɗan, ashe dama ƙazantace ta ƙara miki muni da rashin ilimi ga ƙauyanci, duk da kina nan a baƙarki ai yanzuko baƙin ya zama mai ƙyau a idon mai kallonki”.
Dariya nai mata kawai, duk da dai akwai cin fuska a zancenta sai ban ɓata rainaba, na haye sama ina dariya da ƙwala kiran sunan Mummy da Dad.
A falo naci karo da Mummy zata sakko, nako ɗareta itama ina jera mata kalaman kewa.
Dariya Dad ya shigayi shima dake bayanta yana kallonmu cike da birgewa.
Ni nasan ganin Dad ya saka Mummy amsata hannu biyu, wai har itama na faɗin tayi kewata.
Na saketa na nufi Dad, ya buɗe min hannayensa alamun nazo na shige jikinsa shima, amma sam bazan iya hakanba, sainai murmushi cikin nuna jin kunya da girmamawa a gareshi na durƙusa har ƙasa ina gaishesa.
Hakan ba ƙaramin daɗi yay masaba, dan tun a zuwana gidan idan na durƙusa gaidashi sai yakanji al'amarin da girma, dan bai saba ganiba ga yaransa.
“A tashi haka nan Yarinyar Dad, ALLAH yay miki albarka kinji, barka da arziƙi kwalin secondary ya samu, ALLAH ya kaimu randa zamuga na University haka”.
Cikin girmamawa nace, “Amin Dad, nagode sosai”.

Ban tambayi Aunty Shahudah ba, dan na zata dai ta koma gidan aurenta, Yaya Salman ko da Qaseem nasan basu dawo aikiba.
Ɗakina na nufa inda na iske Amina ta gyara minshi tsaf, sannan kuma an canjamin wasu kayayyakin cikima, ga sayayyar abubuwa dana tarar kala-kala, wanda nasan duk Dad ne, dan duk abinda ya sayama yaransa yanzu na lura bai iya mantawa dani a ciki.
Nayi wanka nai salla, Amina ta kawomin abinci, zama tai inaci muna hira tana bani labari muna dariya cikin farin ciki, mun daɗe da ita sosai a ɗakin kafin ta fita, ni kuma na kwanta danna huta kamar yanda Dad ya maido Amina ta sanar min.
Umarninsa kuwa nabi bayan nai salla na kwanta, kafin wani dogon lokaci barci yay gaba dani.

★★★★★
Chapter 56 · 0% Book details