← Book details Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 75

Sashe 62

Kwai cikin Kaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Rashin Amina ya saka ayyuka da yawa na gidan dawowa a kaina, musamman gyaran sama ɗakin Mummy da Dad da falon saman, sai ko ɗakin Yah Qaseem daya wajabta min shima, da farko har Aamilah da Salman suma sun fara sani, amma sai Yah Qaseem yay magana akan karsu ƙara, matarsa ba ƴar aiki bace.
Harga ALLAH yaban dariyar wannan furuci, yayinda ya ƙona zuciyar Mummy harta yini bata amsa maganata tana fushi dani, Aamilah kam harda cewa wai Mummy ta bincikeni ina niyyar cinye mata kurwar ɗa, dama ta daɗe da zargin ni mayyace.
Ban damuba, danni yanzu a rayuwa mukuma ya rage ban ganiba? Sai dai zaman takewar aure da nakeji jama'a na kira da zaman haƙuri shima.
Kamar kullum yauma na tashi da wuri na kimtsa ɗakina nai wanka, na fito cikin doguwar baƙar riga zuwa kicin, kuku ne kawai keta kiciniyar ɗora breakfast, mun gaisa cikin mutuntawa na haɗa tea na fito falo.
Shi kaɗai nasha saboda sabon makaranta, yanzunma sai ban iya daurewa saina sha ɗin, dan breakfast ma saina ka sha biyu banyiba ko ƙarfe ɗaya.
Sallamar Yah Qaseem ce ta sakani ɗago idanu na, na kallesa ina amsa shi.
Yayi ƙyau cikin suit ɗin sosai, duk da baisa rigar saman ba tana riƙene a hannunsa.
Fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna a gefena dab, hakan ya sakani matsawa nikuma ina gaidashi.
Bai amsaba, sai tambaya daya jeho mani,
“K wai yaushe zakibar gidadanci ne? A zahiri dai ba Bilkisun da bace bagidajiya, amma a baɗini babu abinda ya canja na ƙauyancinta”.
Duk da maganarsa tamin zafi sai nai murmushi kawai, na cigaba da juya cokalin dake a kofin shayin ba tare dana bashi amsaba.
“Baki jinane?” ya sake min tambaya?.
Haɗiye takaicin daya tsayan a maƙoshi nayi naɗan kallesa na ɗauke ido lokaci guda saboda tsareni da yay da kallo, “Naji Yaya, sai dai kasani ni abinda nakeyi ba ƙauyanci bane ko gidadanci, hakan koyarwar addininmu ce, niba muharammarka bace, bamuda hurumin haɗuwar jikin juna a halin yanzu, kodan gujema sharrin shaiɗan mai saka wasuwasi a zukatan bayin ALLAH”.
Jikinsa ya kwantar a kujerar yana ɗan taɓe baki, yace, “Da haka ake cutarku ai dama ku kullum, shiyyasa hausawanmu sunfi kowa rashin wayewar kai, shikenan sai akace dan namiji ya zauna kusa da mace, koya kama hannunta, koya rungumeta wani abu zai faru?”.
Mamaki ya kamani jin furucinsa, sai bance komaiba na cigaba da juya cokalin a cikin shayina nidai.
Babu zato naji ya ɗora hannunsa a saman nawa yana faɗin, “Bani nasha ni”.
Ban sakar masaba, duk da jinake kamar na make hannunsa daya ɗoramin, nace, “Bari na haɗo maka wani to”.
“No barsa, wannanma ya wadatar, sai dai idan bakiso nashanye miki” Ya faɗa yana sake matsowa jikina.
Sakar masa kofin nai kawai na miƙe nabar masa kujerar, domin neman hanyar kuɓuta, ya bini da kallo harna shige kicin.
A ɗan lingun da zai sadani da kicin ɗin na tsaya ina roƙon UBANGIJI akan wannan rayuwar yahudanci, “Ya ALLAH ka kareni ka karemin martabata da mutuncina harna bar gidannan zuwa gidan aure na, ya rabbi ka hananeni saɓa maka bisa ganganci komin farin cikin da hakan zai sakani”.
Na haɗiye hawayen dake neman zubomin kafin na ida shiga kicin ɗin, na tarar kuku harya shirya masa abinci saboda shi yake fara fita a gidan kafin kowa.
Ɗauka kawai nai na kawo masa falon, na iske yana wayane yana shan tea ɗin daya amsa a hannuna.
Yanda yake wayar a zafafe yana ambatar sunan wani Jawaad ya sakani kallonsa, fuskarsa harta koma jaa saboda bala'i kasancewarsa farin mutum sosai.
Koda ya gama wayar tsaki yayta ja da ambaton sai ya kawo ƙarshen iskancin Jawaad ɗin.
Nidai bance dashi uffanba, na haɗa masa abincin na canza kujera can nesa dashi.
Bala'i na cin ransa bai wani ci abincin kirkiba ya tashi zai fice, gabana yazo ya ranƙwafo wai zaimin kiss, nai saurin kaucewa jikina har rawa yakeyi.
Wata banzar harara ya watsamin yana jan tsaki.
“K baƙauya karki ƙaramin ɓacin rai mana”.
Fuska na ɓata nima, nace, “ALLAH ya baka haƙuri Yaya, sai dai ina sake tuna maka bai daceba, kabari sai munyi aure”.
Bai tanka maniba ya fice abinsa yana sake jan wani wawan tsaki.
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina harar bayansa, kai wlhy da sake, dolene nasan maiyuwa da wuri kafin wankin hula ya kaini dare a gidan nan.
Kayan da yaci abincin na tattare na gyara falon, na hau sama canma na gyara da ɗakin Mummy, dan tana ɗakin Dad tunda yana gari.
Sai da komai naga yamin fes sannan na fito harabar gidan tacan baya na zauna ina wani bincike ta waya.
Naja dogon lokaci a wajen kafin na shiga cikin gida saboda kiran Dad daya shigo min a waya.
A d/table na iskesu su duka, dan haka na fahimci dalilin kiran Dad.
Sai da na duƙa har ƙasa na gaishesu shi da Mummy sannan na gaida Aamilah da Salman lokacin da nake zama.
Anacin abincin ana hira, duk da dai babu bakina a ciki sai lokaci-lokaci, shima Dad ke sakoni a maganar na bashi amsa.
Bayan mun kammala ne Dad yace na sameshi sama zamuyi magana.
Duk da inata tunani akan wace magana haka na miƙe nabi bayansa.
Sai da ya zauna a kujera sannan nima na zauna a ƙasa, yace na koma kujera nima, amma saina bashi haƙuri akan nanma ya isa.
Murmushi kawai yayi yana gyara zamansa, idonsa a kaina yace, “Bilkisu nasan zakita mamakin wannan kira ko?”.
Kaina na jinjina masa ina bashi amsa da “Eh wlhy Dad, ALLAH dai yasa banyi laifi bane”.
“A'a bakiyi laifin komaiba mai gadon zinari, akan karatune dama, mizai hana da wannan zaman ki sake komawa makaranta kawai? Kinga saina turaki wajen yayarki Shahudah ko?”.
A zuciyata mamakin rayuwa irin ta Dad nake, maimakon yamin zancen aure amma kunji zancen cigaban karatu yakemin, duk da a yanzu ina cikin shekara ta ashirin da huɗu ne.......
Katsemin tunani yay da faɗin, “Karki ce zaki sakama ranki wata sakarar soyayyar Qaseem kinji, ki tsaya kiyi karatun da zaki tallafi rayuwarki koda bana raye, shi kansa zaifi ganin mutunci da kimarki, duka shekararkima nawa da har zaki sakama kanki maganar aure? Bakiga sakamakon da aure ya bama yayarki Shahudah ba, Rayuwar yau data jiya da mu mukai akwai banbanci kinji”.
Kaina na ɗaga masa ina murmushi, nace, “Dad dama ba aure nakeso ba, sai dai akwai wani buri a raina”.
Da sauri yace, “Wane burine haka ɗiyata?”............✍🏻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[8/11, 5:00 PM] Marsy😘: https://youtu.be/gUGygQ5y5pg

*_MANHA HAUSA NOVELS_*

https://youtu.be/xUINNiDdeH0

*_AL-ƘALAMI TV_*

*_Typing📲_*

*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_

*_____________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na talatin da biyu_
*___________________________________*
Chapter 62 · 0% Book details