← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 40

Sashe 9

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da bai shafeta ba,ke da aka yiwa tambayar me gida kurum saiki zaqe?,bayan kinsan zuciya da fuskarki duka basu da baiwar iya shanye bacin rai da maida komai ba komai ba "Kadanma kika gani,na fiki iya iskanci" ruqayya ta fada tana komawa ciki. Kitchen kawai ta shige abinta,ta canza shawarar shiga dubashi din,a maimakon hakan sai ta jawo wayarta ta tura masa tex tana masa sannu da jiki. Yana fahimtar ta qwarai,tasan ko iya tex din ya wadatar. Data tabbatar ya shiga saita bude fridge ta ciro lafiyayyen kifi mara wadatar qaya ta kwara masa ruwan zafi sannan ta fara aikin sarrafashi. Nau'in kifin da saleem yafiso ne,kuma ita din bata taba rabo dashi koda wanda ya siyo ya qare,tana siya da kudinta ta zuba a fridge din. Jin dadin hakan ya sanya duk sanda yazo yaga ta zuba din zai biyata kudinta harma wasu lokutan ya qara mata. Abun na masa dadi qwarai,saboda na gefin Zainab sau tari saidai yaga an zubda a shara ya lalace,don ba damuwa ta fiyayi da kunna Fridge din kayan miya ba kwata kwata,ko ta kwashe ta bayar kyauta don kawai tayi bajinta. Kafin ta gama aikin ta kira qanwarta "Kizo ku tafi dasu alhassan su kwana gobe sauka idan jikin abbansu yayi sauqi na samu fitowa saimu dawo tare,tun jiya dama na tambayar musu" ba jimawa ta iso gidan,saita sakar mata gyaran kitchen din,ita kuma ta wuce bedroom dinta. Wankanta wani abune da bata wasa dashi,kowanne lungu da saqo da tasan maboyar datti ce sai tabi ta qalqale,ramin cibiya,qasan mama duk da tana da baiwar tsayayyun mama,matse matsin mazaunai,matse matsin cinyoyi,bayan kunne harma da cikin kunnen da qasan mara. Cikin mintuna talatin ta fito fes cikin doguwar rigar atamfa chocolate color din fatartan nan tayi luf cikin qamshi da cream masu taushi,daurin dankwalin kuma ya zauna mata sosai a kanta. Sai da tayi sallar azahar sannan ta dawo parlor din. A falo ta samu anata daru da iftee tace itama sai taje,da farko sai ta qyaleta tanata saka turaren wuta a burner tare da jona humidifier dinta,har ta gama bata bar kukan ba yarinyar,duk da ba'a jima da dawowa da ita gidan daga yaye ba, dole ta hada mata kala dayan itama ta bisu din. Kitchen ta wuce,ta ciro dafaffiyar budurwar kazarta da tasha hadin saqe saqi,kazar da take dafata da hannunta da ingatantattun saqe saqi da kayan da suke bawa jiki garkuwa da lafiya su kuma magance ciwon sanyi. Dan dumamata tayi kadan sannan ta zauna a nutse ta fara ci hankali kwance saboda sashen nata ya dauki shuru. Minti goma sha biyar ta gama,sai ta wuce da kwanon kitchen,ta koma dakinta tayi brush sannan ta dawo ta sake mulke jikinta da turaren da ba kasafai take amfani da shi ba idan ba lokacin kwanciya bacci ba saboda yadda saleem din ke matuqar sonsa. Bata yafa komai ba sai wani dan siririn gyale da yafi kama da mayafin yara wanda ya dace da atamfar jikinta ta fito daga sashen nata ta ratsa babban falonsu da yaron dake musu aike aike cikin gidan tuni ya gama tsaftaceshi ya wuce sabgar gabansa,ta doshi qofar falon sashen zainab din. Tun bata qarasa ba take jiyo ifce ifcen haneefa da khalil,da alama ma fada sukeyi,don tana jiyo muryar uwar tana kwarara musu tsawa wanda sauran kadan ta barke da ashar,tana tuna cewa saleem din yana gidanne da tuntuni ta hadasu data maguzawa,tunda a cewarta ta lura sunfi ganeta. Duk da tayi sallama ba wanda ya jiyota,sun kacame da dambe. Ta sanya qafarta da hanzari don ta isa ta rabasu,saudai tayi kyakkyawan Katarin taka wani abu me danqo. Koda ta dube sai taga ashe tea ne aka watsar har ya fara kama gurin ya soma bushewa. Tsigar jikinta ta zuba,ta janye qafarta tana takata saman carfet din falon saidai a nan ma qasa ta cabo a qasan qafartata. Dubanta ta maida ga tafin qafartata kafin ta dago kai saleem da hayaniyar ta isheshi har ta tayat dashi a bacci ya fito a dakin. Dif sukayi kowanne na neman gurin buya,sai suka fara qoqarin barin parlor din. Bai lura da ita ba saboda baiyi tsammanin shigowarta ba,saidai sassanyan qamshin da ya gauraye parlor din yake shiga masa hanci ya sanyashi wara idanunsa a parlor din. Qamshine da a jikin mutum guda ya sanshi,qamshine da duk sanda ya jishi ya tabbatar zai samu wani irin tarairaya da soyayya me girma,qamshin dake nuni da zai shiga wata duniya me cike da tarin nutsuwa. Ido suka hada daidai da fitowar Zainab daga kitchen wadda ke mamakin me ya sanya haneefa da Kahlil din nutsuwa lokaci guda?. Sarai ruqayya ta ganta amma ko da ido bata nuna mata hakan ba,sai tafi maida hankalinta ga saleem din. "Zuwa nayi na tafi da ango,ban sani ba ko angoncin daka balle jiya ya hanaka gane hanya shi yasa har yanzu baka samu shigowa ba" ta fada a tausashe tana murmushi. Hannu yasa ya shafi sumar kansa,har yanzu baya jinsa ya koma dai dai,kuma har yanzun idan ya tuna jiyan ya kasa nutsuwa haka siddan ya koma haka,ba abinda zai iya dorarwa me shauqin da zaice yayi matuqar qayatar dashi da zai tsaya masa a rai,face wasu irin abubuwa da hancinsa ya shaqa. Idanunsa sun rufe ya zurfafa hancinsa cikin jikinta,abinda dama ba kasafai ya fiya yi ba,wannan din wani sirrinsa ne da ba mahaluqin da ya sani,ruqayyan kadai yake iya yiwa hakan,saboda yasan duk inda zai cusa hancinsa AMINCI zai tarar da marabta me kyau. Gaba daya zainab din ma a tsarinta ire iren wadan nan abubuwan bata lokaci ne,gwara a dinga tafiya zuwa ga babbar headquarter din gaba daya. "Banajin dadi ne" ya fada shima cikin narkewar da baima san yayita ba,kawai wani farinciki yaji yana saukar masa tamkar mutumin dake tsakiyar kogo me duhu masu agaji suka riskeshi don fiddashi hakanan yaji. "Ya salam" ta fada tana nuna zallar alhini a fuskarta tana kuma takowa da sassarfa zuwa kujerar da ya zauna din a kai,yanayin yadda take takun ya bawa qirjinta damar motsawa,wanda ya ciko yayi fam saboda baiwar aqirji da take dashi,uwa uba kuma tana using push off brazier don bahaushe yace idan kana da kyau ka qara da wanka. Ita kanta tana alfahari da baiwar beast da hips da Allah ya bata,ita din baqace ko ace wankan tarwada,zainab ta fita fari da tsahon gashi sosai,farin da a baya yaso ya zame.mata tarnaqi kuma kalmar da akaso ayita cusguna mata da ita. Bata taba mance lokacin auren zainab,zuciyarta ce kadai ta rage bata buga ba,amma hawan jini kashi kashi ta yishi. Hasken fata da tsahon gashi tayi imani kawai zainab ta fita,saidai ita kuma Allah sai ya qareta ta bangarorin da take da tabbas ta yiwa zainab rata me tarin yawan da bazata lissafu ba. A hannun kujerar da yake kai ta zauna tana duban fuskarsa "Habba amma ya kamata na sani ko?" Ta fadi a shagwabe tana tura baki gaba. Murmushi ya saki yana kauda idanunsa saboda ta fara tadoshi sosai "Am sorry" ya fada a taqaice saboda tsaiwar Zainab a wajen wadda kamar zata fashe "Alright,muje na qarasa wannan jinyar gaskiya,wannan amarci an cishi yadda ya dace,har ruwan dumi zan maka na gasaka da kyau,kaga nima sai naji dadin diban nawa tsumammen uwargidancin" ta qarasa maganar tana kashe masa ido daya hadi da cije lip's dinsa na qasa abinda ya sanya tsigar jikinsa zubawa. *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 07 "Ba inda zaije,bashi da lafiya,kuma har yanzu kwanana ne" a nutse ruqayya ta waiwaya ta dubeta sama da qasa,ta ganta wata harikicibayya cikin zanin wata atamfa da yayi musu waccan sallar,ta Zainab din ruwan madara ne,atamfar kudinta duk daya ta doshi dubu goma sha takwas amma cikin qasa da wata goma tata har ta doshi hanyar zama tsumma,ta rune daga milk ta koma brown brown da torches na dattin abubuwa mabanbanta,bakin zanin yayi leb'atu wani ya zarta wani yana lilo "Haba amarsu bakya laifi,baki lura bane azahar har ta gota?,ko kin manta ke kika tsara mana hakan dama?,kiyi haquri kwana biyu rak zan dawo miki dashi da kaina" ta fada mata tana murmushi dariyar daurin dankwalijta yake a jirkice yana kama ruqayya. Sau tari bata fiya jin kishin zainab cancan ba, saboda tasan bata da abinda zata kara da ita,saidai hali kawai irin na zuciya da kuma abinda takeso. Miqewa saleem din yayi yace "Minti daya" "A fito lafiya" ta amsa masa tana maida dubanta ga tv din dake aiki, wadda rabinta tayi baqi saboda yadda su haneefa suka ragargajeta duk girmanta kuwa,shi kuma yayi rantsuwar bazai canza mata wata ba,saboda bayan wadda ya siya musu ita da ruqayya ya sauya mata wata,wannan din shine karo na biyu kenan da yake sauya musun bayan ta farko. "Ba inda zashi,yana nan" zainab din ta fada tana juyawa tabi bayanshi dakin. Aikin da ya gagara bai gama jiya ba yake hada kan takardun nasa sai yaji motsinta,koda ya waiwayo ta fara zare t.shirt da zanin jikinta,ta fara takowa inda yake tana girgiza kafadunta "Mene hakan?" Ya fada a mamakance,take fuskarta ta sauya kamar yadda bata iya cinye bacin ranta ba "Ragowar haqqina nake buqata,kuma kaima aina lura bawai ka gama nutsuwa bane" Dariya ce ma taso kamashi,yadan kauda kai daga nan yana jiyo yadda smell na jikinta ya canza da alamu tana da buqatar tayi wanka amma ta kasa gane hakan. Abu na biyu kuma ya fahimci tana so ne tayi abinda zata batawa ruqayya lokaci,saidai kash bata iya durfafar miji da salon zai dauke masa hankalin ba tare dashi kansa yasan ya akayi hakan ta faru ba "Lokaci ya fice yanzun kema kin sani" "Eh amma hakkina ne ai a wuyanka ko?" Tsaiwa yayi yana kallonta kafin daga bisani ya girgiza kai yaci gaba da hada takardunsa. Maganganu ta shiga yi na bacin rai har ya gama,ya miqe tsaye yana zuba mata idanunsa abinda ya sanyata rage kaifi bakinta "Kiyi qoqari ki tabbatar ba wani abun kika zubamin jiya ba,don muddin na gano hakan kinsan sai na hukuntaki tabbas!" Ya qarashe maganar yana kewayeta ya fice,saboda yasha mata gargadi akan hakan,yayi dukkan abinda zaiyi ya koya mata hade haden vegetables din da ruqayya keyi masa da suke da matuqar amfani ga lafiyarsa da auratayyarsu,amma tsabar son jiki ta kasa tsaiwa ta dinga
Chapter 9 · 0% Book details