Sashe 19
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akan abun wasa,harda haneefa da ya kamata ace a shekarunta ba wannan abun yakeyi ba,ita ke kula ma da khaleel. Sanda suka farga da kallo suka bita baki sake saboda ba zasu iya cewa ga ranar qarshe data tako sashen nasu ba. Tunda ta shiga falon yanayin falon taji sam baiyi mata ba,haka ta dinga takawa cikin tsantsani don ko ina datti ne,bata tunanin jiya ya samu kyakkyawar shara,yau kuwa dama tunda tana sauri biki ya samu tayi imanin inda zata leqa kitchen dinta ko wanke wanke batayi ba. Kusan ginin nasu iri daya ne,wannan ya sanya bata sha wahalar gane inda bedroom dinta yake ba "Karki shigarwa ummanmu daki fa" haneefa ta fada tana kallon ruqayya. Sosai abun ya bawa ruqayya mamaki,ta juyo tana duban yarinyar. Har tasan wani kishiya kada ta shigarwa kishiya daki?, komai ma wai zama zainab takeyi da yaran ta gaya musu?. Hannu ruqayya ta saka ta yafitota tana murmushi "Zoki nunan kayan ummanki zan dauko mata zani da hijab,asibiti daddynku zai kaita" tsalle tayo ta sauko daga saman kujerar da sun jima da cin ubanta ta nufo ruqayyan ba tare da ta maida hankali ga batun zuwa asibiti ba "Zakisha wahala,dauko kayan ummanmu akwai wahala,don itama kullum saidai ta gaji ta dauko wanda ta gani ta mayar da sauran" bata cewa yarinyar komai ba tabi bayanta. Kusan idan ka ganta cikin dakin Zainab haihuwa tayi,rabonta da bedroom dinta tun haihuwar khalil. Tayi mamaki har fiye da zato na yadda ta zamu dakin nata a hargitse,hatta da shimfidar gadon a harmutse take,harda qasa qasa a kai,panties nata Brazier da cup harda spoon ma. Qasan dakin kuwa baja baja yake da karikice da bazata ma iya tsaiwa tantancesu ba. Dakin ba abinda yakeyi sai wani irin hamami hamami kamar warin dauda cakude da warin hammata. Bata sani ba amma qila tsabar tashi da jiki da hammatar Zainab din keyi da annakiyar da dakin yake da ita ne ya sanya a madadin qamshin turare... Nata turaren ya zama wadannan warika ne gud biyu. Bandaki shima na buso tashi gudunmawar qarni da zarnin ta qoofar bandakin dake a wangale. Gaba daya kayane jibge a rataye tun daga murfin sif din zuwa kan qofar bandakin,zannuwanta ne panties da riguna. Haneefa ce ta bude sif din hankalin ruqayya nakan wani tsadajjen turarensu data gani yashe a qasa an tattara kwalbar an shareta acan matse matsi mudubi,ta yiwu dazun da tana saurin zata fice ne ya fashe garin ta saka,ita kuma ba zata iya tsaiwa ba ta tattareshi gefe da zummar saita dawo,data dawo din kuma bata da lokacin bi ta kansa sai ranar da Allah yakai tsintsiyar shararta gurin. Zubowar kaya kawai ruqayya taji yiiiiiiffffff kamar an saki buhu. Gefe ta matsa da sauri adan tsorace,haneefa ta sheqe da dariya "Haka ummanmu takeyi kullum idan zata saka kaya,ki zabar mata saiki barsu a gurin saikin dawo,ko natayaki mu mayar" yarinyar ta fada hankalinta kwance cikin nishadi kamar me bada labarin abun arziqi. Tsaf ruqayya ta qarewa kayan kallo,tama kasa tantance meye da meye,don basu da maraba kwashen dilar kayan gwanjo "Ke da nace kaya aiba wanki za'a kai ba,ba kayan dauda ba wankakku asibiti zataje" baki ta saki tana kallon ruqayya "Ai sune wadannan,idan aka kawosu daga wanki watsasu mukeyi,idan muka cire kuma indai laundry basket dinmu ya cika sai mu ajjiye ciki idan an tashi kai wanki a kwaso,rannan ma daddy yace duka kayan ciki tsami sukeyi" ta fadi tana toshe hanci cikin son gwada yadda yayin a ranar tana dariya abinta don maganar har yau dariya take bata "Ya isa,ina hanaki fadin abu ko an tambayeki bare ba'a tambayeki ba,mu kwashe kayan mu mayar" tace da haneefan. Tana tilar kayan tana dauke numfashi da kau da kanta,haka ta dunga diba tana cusasu yadda ta gansu haneefa na tayata. Kafin su gama cikinta ya gama gurbata,da qyar ta iya gano zani da hijabi ta fito dasu a hannunta amma zuciyarta fal qyanqyami. A nan ta samesu,ta ajjiyewa zainab din kayan amma sai tayi talau alamun ba zata iya sakawa ba. Saleem dinne ya karba ya fara saka mata. Da ya gama saka matan ya riqeta suka fita farfajiyar gidan Zainab din tana layi kaman zata fadi. Kwanukan abincinta ta fara tattarawa tana daukesu a wajen kafin suma su fita a kanta. *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 15 https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39 *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* ____________________________ Tana kitchen taji ya sake shigowa "Ki dauko mayafi muje mu kaita" waiwayowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta kauda kai. Wani abune ke mata yawo a zuciya,ba zata taba manta wannan ranar ba,ranar da banda kiyayewar Allah babu abinda zai hana ta rasa ranta a abinda Zainab din tayi mata,bayan ta rasa ranta harma ta rasa ran abinda yake cikinta "Kuje kawai saikun dawo,zan zauna da yaran tunda dai ba za'a barsu haka gida ba kowa ba" ido ya zuba mata na wasu sakanni,har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice. Koda ta gama kintsa kitchen din alhassan ta aika ya kirayi su haneefa suka dawo sashenta,sannan ta saka alhassan din ya kulle sashen zainab din,don yafi haneefa nutsuwa da hankali,sau tari banda tsaho da ta fishi zaka dauka shine babban. Falon ta dawo ta zauna lokaci lokaci tana duba wayarta,yaran suna kallon carton,saidai bari bari da su haneefa din keta sanyata,ba'a samu sauqin abun ba sai da khalil yayi bacci. Dole ta saka ya qure ac dinsa saboda yanayin da jikinta ke bayarwa da ya soma dumame motar. Yawun takaici kawai yake hadiyewa,ya rasa me Zainab ke buqata a rayuwa da zai sanya ta canza halinta. Wasu lokuta yakanji kunyar ace ita din matarsa ce,abinda bai taba ji ba dangane da ruqayya duk da sunfi dadewa da ita nesa ba kusa ba akan zainab din. Wani kuka take kwazara mishi babu dadin amo bare dadin sauraro,ita a haka dole kukan da zai taba ransa yaja hankalinsa,abinda bata sani ba zallar takaici ne ya qumeshi. "Wallahi na sake yarda da gaske asiri yana tasiri a kanka,na rantse da Allah ko kaffara bazanyi ba inda ruqayya ke wannan kukan da tuni ka rasa inda zaka tsoma ranka,amma ba komai akwai Allah" "Ba zaki rusuna ba kenan ki saita kanki ba" "Me nayin da har zan rusuna?,saboda kawai idan ba'a sonka idan ka fada ruwa ma sai ace ka tayar da qura?,kuma ko meye ya sameni ai ta sanadinka ne,duk inayine don na gyara kaina na samawarwa kaina 'yanci kamar yadda ruqayya ke dashi,don bana son kaucewa hanya nabi malamai". "Anzo gurin" ya fada a ransa,cikin zuciyarsa yana fatan ace shiriyarta ce tazo,sai ya sassauta tuqinsa yana duban titi "Ai baki kama hanya ba sam zainab,ke din ba makauniya bace amma ta wani fannin kinfi makaho makanta,ta yaya kike tunanin zaki kamo ruqayya a haka?,bayan kinfi kowa sanin abubuwan da takeyi wadanda suka kaita matsayin da kike hange?,duk da ina iyakacin bakin qoqari na na yin adalci a tsakaninku?" Kamar ta banka masa ashariya haka taji,ita da yayi mata misali ko kwatance da ruqayya gwara ya sakata a daki ya lallasata tayi dumamen jikinta "Wanne abu takeyi banda zallar kissa da munafunci da bin malaman tsubbu duk don ta mallakeka?,idanunka ya rufe ka kasa ganin gaskiya?,ni da kullum nake fadi tashin gyara maka shimfidarka amma qoqarina a banza yake kullum". Kai ya girgiza "Zaki bawa Allah tabbaci ranar qiyama akan qazafin bin malamai zainab,ki kiyaye harshenki daga fadar abinda baki da yaqini akai" kuka ta fashe masa dashi "Ehnnn,an tabo shalelenka ba?,muddin kana irin wannan akan ruqayya wallahi zaman lafiya tsakanina da ita har abada" ko ya waiwaya ya kalleta bai sakeyi ba,ya sani Zainab tayi nisan da bazata taba jin kira ba sai wani ikon Allahn. Sun samu sunga likita,amma yawan gudawar da takeyi yasa likitan yace zata kwana anan a saka mata drip,gudun kada suje gida cikin dare abun yayi worsening. Sosai ta sharbe masa tana ci gaba da koke kokenta da babu abinda suke qarawa saleem sai takaici. Don tuni likita ya gaya masa ya dinga sakata tana kiyaye shan magani barkatai "Magungunan nan basu da wata qa'ida ko doka,duk maganin da za'a shashi ba bisa qa'ida ba dole yayi illa" tuni saleem din ya fahimci maganin meye,ba zata daina halinta ba kenan duk da tarin gargadin da yayi mata?. Bai iso dakin da suka batan ba sai daya kira hajiyayye qanwar mahaifiyarta akan tazo ta kwana da ita sannan ya wuce dakin. Tanajin sallamarsa ta sharbe magashiyyan. Baibi ta kanta ba tsabar takaici,yaja kujera ya zauna kawai yana danna wayarshi. Ba dadewa hajiyayye ta iso,ya miqe yana bata gurin zama "Da kayi zamanka abinka" hajiyayye tace "Ah dama ke nake jira,tafiya zanyi ni" ido zainab din ta bude da sauri,taci alwashin yau kwanan asibitin zaiyi,shine abinda zatayi kawai wanda zai quntata ran ruqayya. Yunqurin amai ta fara yi na qarya,shi da hajiyayyen dukka suka qaraso,saidai babu wani abu data fitar don tuni aman gasken ya fidda komai daga cikinta "Idan na fita zan tsaya na yiwa nurses din magana,ko alluran tsaida amai din suzo suyi mata" ya fadi yana matsawa gurin saman kanta "Sai da safe zan sake shigowa,banajima zamu kai azahar bamu koma gida ba,Allah ya sawwaqe " ya fada yana fiddo kudi daga aljihunsa ya ajjiye gefan kanta cikin qoqarin danne bacin ransa kada duniya ta fahimci halin da suke ciki "Yanzu ko tausayin halin da nake ciki bakayi tafiya zakayi?" Ta fada da qarfi don hajiyayye taji harda matso hawaye "Banda abinki zamansa a nan ai bazaiyiwu ba,kuma me zaiyi miki shi da bashi ke cire ciwo ba?,jeka abinka gida,Allah ya bamu alkhairi" "Sai da safe" ya fadi yana ficewa. Kaman jira takeyi ya fitan ta miqe ta zauna sosai har cannula din hannunta na qoqarin gocewa "Banso kikayi magana ba, wallahi hajiyayye na fara gajiya da rashin adalcinsa,qiri qiri mutumin nan kiga abinda