Sashe 13
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inno kakata ta gayamin,yadda muke samun qaruwa(yagewa) yayin haihuwa haka suma suna samu,amma saidai su basusan wani dinki ba,ana gyara mace ta koma fes da bagaruwa da sabulun salo ta hanyar tsarki da shiga ruwan bagaruwan. Na baku misali mana" "Muna jinki" suka fada a tare saboda yadda bayaninta ya fara musu dadi da tasiri "Zai yiwu ki siya mota ya zamana kullum kin hawa kina sabgoginki,ko engine generator kuna kunnashi kullum amma ba'a masa service?" Kai suka girgiza a tare alamun a'ah "Idan hakan ya kasance wataran ba za'a wayi gari ya tashi a aiki ko yana aikin dai amma lallabawa kawai akeyi ba baya bada abinda akeso?" "Tabbas" batulu ta fadi "To kamar haka yake a wajen mace,kiyi gyara saffa saffa da ingantattun itatuwa da abubuwa natural,karki tsaya a gyaran qasanki,ko ina na jikin mace yana buqatar kulawa da gyara,saidai kuma komai da zakiyi gyaran dashi ki tabbatar ingantacce ne. Shi kansa engine din idan aka yawaita yi masa service din da juyen mai haka ba gaira ba dalili ba tare da alamu sun nuna yana buqatar hakan ba me zai faru?" Kai batulu ta jijjiga "Gaskiya akwai matsala, za'a yita sakwarkwatashi ne ana raunata qarfinsa" "Wani notin ma idan aka kwance ba lallai a iya mayar dashi wajensa a daure,shikenan sai ya fara rawa,sanadin hakan sai wani gurin ya kuma saki" fatima ta qara dorawa "Yauwa,alhamdulillah,komai idan yayi yawa yana da illa ga jiki da lafiya,hatta natural ways din idan ka dauke 'ya'yan itatuwa da su basa yawa ga lafiya" "Gaskiya ne" batulu ta fada "Duk shan maganin matanki ko acan da ake hadawa saikin kiyaye wasu abubuwa sannan zasuyi tasiri,suma masu kyan ba daka ake shansu ba ai" "Kamar me da me?" Fatima ta fada tana komawa ta zauna "Yauwa,dole ki zama mai tsafta,babu ta yadda zaki tuttuli magani ki nemi kasancewa da me gida amma ko ina yakai hari sai a koroshi waje....." Bata qarasa ba suka sheqe da dariya su dukka biyun. D ido ta bisu tana son jin ba'asi,batulu ta yanke mata tunani "Kamar dai zainabunki?" "Banaso, ba'a gulmar 'yaruwata a gaba na" "Ita tayi taki ai,har ta taya a zageki" batulu ta fada tana tabe baki cikin jin takaicin sakarkarun halayen zainab. Murmushi ruqayya tayi "Taga zata iya ne" ta amsa a taqaice sannan ta dora "Abu na gaba ba yadda zakisha maganin mata baki da lafazin baki,ladabi biyayya haquri da juriyar zaman aure wanda sune jigon zaman ba wai maganin ba,shan magani kawai yana armasa auratayya ne da hanata ta gunduri abokin zama" "Gaskiya ne wannan,na yarda da haka" batulu ta fada tana jinjina kai "Sai kuma babban abun,mata ne ku ba kunyarku zanji ba........shan maganinki bazai taba miki amfani ba ba tare da kin iya sarrafa me gidanki a turaka ba,dole ki koyi salo da dabarun kasancewa da me gida sannan tasirin maganin zai fara aiki a jikinki,wannan dole ne,ba kuma kiyita gyara kanki shi bakya gyarashi ba indai akwai fahimtar juna da sauqin kai a tattare da shi" "Suma ana gyaransu kenan" fatima dake dan qunshe dariyar kunya ta fada "Eh,sosai ma" ruqayya ta fada tana kallonta "Kinga maggi?,kinga maggi?,yana bala'in taka muhimmiyar rawa wajen qarawa maza rauni,zaqi,maiqo,yawan yi musu ta'ammali da man gyada,shan sanyi,shan abubuwan da suke da sinadari caffeine da yawa a ciki,shan lemukan nan masu gas irin coca-cola da sauransu,ki yiwa miji natural drink kamar zobo,karkice zaki zuba tiara ko baby mix ko cola a ciki,ki dafashi natural da cocumber ginger cinnamon cardamom na'ana'a scent leave (daddoya) kanunfari da abarba,ki tace kisa masa sugar kadan yafi ki bashi wadan nan lemukan kaf dinsu,ku daina jibgawa mazanku magungunan qarfin maza,kashesu kawai kukeyi, za'a kai jallin da ba zasu iya tsinana komai ba muddin basusha wannan maganin ba,ke kanki idan kika ta'allaqa rayuwarki da shansu akwai matsala wataran zakiyi expire wallahi" dariya dukka ta basu,har itama suka saka ta dara(akwai hadin salad da na baku a last page,shima yana da matuqar muhimmanci wajen qarawa maza kuzari a turaka) "Eh mana,sanda kike da buqata kiyi service kiyi,service me ma'ana da hankali,ko meye na gyara zaki iya siyan kayayyakin a ganyensu ko asassaqensu guda ki dafawa kanki,idan ba zaki iya ba ki karba a gurin wadda kike da tabbaci a kanta hundred percent. ammafa kome zakisha indai ba zaki dinga ci kina qoshi ba akwai matsala, ba'a son ki dinga zama da yunwa,ko a abincinki ya zamana babu wani abu da zai qareki a lafiyar jikinki". "Amma matsi fa mata na sonshi Anty" murmushi ta kuma saki,mata da yawa sun halaka ta sanadiyyar matsi "Akwai natural ways shima" "A bamu anty" fatima ta fadi da sauri sai kuma kunya ta kamata. "Zaki samu sassaqen bagaruwa,kanunfari,bagaruwa sai magarya,ki tafasasu ki dinga shiga ciki idan ruwan ya huce,kunga duk a ciki meye me cutarwa?,meye wanda baku sanshi ba?" "Babu wallahi anty" fatima ta fada cikin gamsuwa "To kun gani,ku damu kanku da sabulun tsarki,bayan babu sabulun da yakai sabulun salo indai kin samu original din" "Gaskiya ne" batulu ta fadi "Allah yasa mu dace" ruqayya ta fada tana miqa batulu babyn "Zaki tashi muna qaruwa dake" murmushi ta saki "Muna gaisawa da hajiya na shigo banko zauna ba,kuma inason na leqa gidan umma binta,zan jira shukra zata kawomin su iftee zasu wuce gida dasu" "Anty kafin nayi arba'in zanzo gida na sameki don Allah a bani sauran sirrikan" "Saikinzo fatiti,kawai dafe dafen nama kala kala da zakiyiwa kanki,a baki da dadi a jiki da aiki ba wani sauran fargabar meye a ciki" cike da murna tace "Zanzo in sha Allah" "Qafarki qafata" batulu ta fada tana dariya "Duka sai kunzo" ruqayya ta fada tana murmushi. La'asar liqis ta baro gidan sunan tayi sallama dasu don ta qarasa gidan umma binta kamar yadda tace. Qanwace ga mahaifiyarta kuma a nan bayan layin gidansu fatiman take. Don haka cikin qasa da minti daya ma ta isa tunda a mota take. https://chat.whatsapp.com/EKyzZCUEGyRAEGGAnTHmGF *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 10 Hankali kwance cikin nutsuwar ta ta macen da tasan kanta ta tura kanta cikin gidan bakinta dauke da sallama. Sai da tayi sallama sau biyu kafin a amsa. Daga can cikin daya daga cikin dakunan dake hannun hagunka. "Da alama umma bata nan" ta fadi qasa qasa ta wucewa dakin da take jiyo ana amsa mata sallamar. Labulen ta dage tana sake jaddada sallamarta. Ido hudu sukayi da matashiyar dake zaune saman abun salla. Sanye take da hijab har qasa,baka ganin komai sai fuskarta da tayi wani haske dauuuu,irin hasken da kana masa kallon farko zaka san cewa ba natural haske bane. Hannunta da yanayin hasken fatarsa yasha banban da hasken fatar fuskarta na riqe da carbi tana ja daya bayan daya,bakinta yana motsawa mis mis da alamun wani abun take karantawa "Iskancin banza,ashe kina ciki kina jina naketa kwada sallama" ta fadi tana dan jifanta da harara hadi da zare takalminta ta shigo dakin gaba daya tana cewa "Yo wannan basai a shigo ayi muku sata bama?" Tayi maganar tana zama gefan kujerar guda daya dake dakin idonta akan matar. Hannunta ta dora saman bakinta alamar tayi shuru,sannan taci gaba da jan carbinta. Sasakai ruqayya tayi tana binta da kallo,sai kuma taja tsaki ta maida dubanta ga dakin. Kayan ado ne jere sama madubin,mayuka kala kala da turaruka,harda kwalabe da gwangwanayen supplement kala daban daban. Kan supplement din hankalinta yakai,ta miqa hannu daga inda take ta dauki wata zungureriyar kwalba dake dauke da syrup a ciki. Tun a rubutun farko ta fahimci maganin qara qiba ne,saita daga kai tana kallo fuskar matar dake zaune akan sallah. Tabbas,ta qara qiba qiba data jima tana mamakin ya akayi wasila siririya da ake tsokanarta da sunayen tsokana kala kala saboda rashin qiba lokaci guda tayi irin wanna qibar?. Mamaki ya hanata magana,saita mayar da kwalbar ta ajjiye dai dai sanda idonta ya gano mata wani tablet din dake nuna whitening yakeyi. Kai ta sake jinjinawa tana maido dubanta ga wasilar,dai dai nan ta shafa hannunta akan fuskarta da alama ta gama. "Ke kuwa me kika zauna yi har rana tana shirin faduwa bakiyi sallar la'asar ba?" "Haba ni da nake da tarin buqatu?,ta yaya zan bari sallar ta kufecemin? la'asar dinta liman yana sallamewa ina sallame tawa,wannan wani wuridi aka bani nakeyi" "Wuridi ko addu'a" "Duk daya ne ai" ta amsa mata tana ninke sallayarta "Addu'ar ce idan anayi ba'a amsa sallama?,nidai a iya sanina salla ce kawai ya haramta idan anayinta ayi magana" Ruqayya ta sake jifanta da tambayar "Ke wannan ba irin addu'ar da kika sani bace,wannan ta neman miji ce,yazo ayi aure nima na ganni a dakina na huta kamar kowacce mace" ta fadi tana zare hijabin jikinta t wurgar gefe,hakan ya sake bayyanawa ruqayya qibar da ta tsammata daga wasilar,saidai ashe hijabi ma ya rufe wani abun. Kasa shuru ruqayya tayi tana duban wasilan tace "Yanzu wasila wannan wacce irin qiba ce haka da uban fari da fuskarki tayi?,ga kunnenki duk kin bula kin cikashi da barima?" Gefen ruqayyan ta zauna tana daukar wayarta "Ba zaki gane bane,ke don kina dakinki asirinki a rufe,yanzun rayuwar sai da updating sai kina gyara,idon mazan a bude yake,saisu rainaka ko kiga wanda baikai ajinka ba yazo yace kai yakeso saboda rainin hankali" "Yanzu qibar da farinma kenan yayinsu akeyi" "Ke,qwarai kuwa,mace 'yar duma duma ai duniya ce,farar mace kuma itace alkyabbar mata,lantarkin gida,ajebo kalar hutu,sadakinsu ma daban yake,hakanan sunfi shiga" hangame baki tayi tana kallon yadda wasilan ke magana da confidence. Tare sukayi yammatanci da wasila,tunda can tana da surutu da rawar kai,amma yanxun kamar an qara mata da wasu sabbin halayen "Indai hakane kice mu da bamu samu mashinshini ba" "Da kenan,sanda kukayi aure ai duniya a kwance take,shekara bakwai zuwa takwas baya fa,kema ba yadda banyi ki goge baqar fatar nan ba kikaqi,ai gashinan kina zaune kina ji kina gani mijinki yaje ya dauko farar,wadda ma bata fiki komai ba" dariya wasilan ta bata yadda take nuna jin zafi da jin haushinta duk sanda akayi zancan zainab "Wai tsaya,kin manta bleaching haramunne?" "To ya za'a yi?,neman wanda zamu shige daga ciki kawai mukeyi?" "Tabdijan,wasila?,a haka?,kina abinda Allah bayaso amma ke kina neman ya dubeki?shaidanne fa yayi alqawari da kansa Allah ya fada mana cikin suratun nisa'i aya ta dari da sha tara,cikin alqawarin da yayi yace zan