Sashe 4
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya saba ajjiyeta,ya daidaita tsaiwarta sannan ya kashe motar yana furzar da iska daga bakinsa a mugun gajiye. Yau tunda ya fita bai zauna ba,ya gaji liqis yadda ya kamata,sunata zirga zirga tsakanin warehouse dinsu da shagunansa,ko abinci bai samu yaci ba,yunwa ce a kwance a cikinsa. Hannun rigarsa ya tattare yana duba lokaci,ana dab da kiran sallar magariba ne,duka duka bazai wuce mintuna goma sha biyar ba. Hannu ya sanya ya bude motar ya fito hannunsa dauke da ledoji,qarar rufe murfin motar yaja hankalin zainab dake kitchen,ta ajjiye ludayin miyarta da sassarfa ta fito daga kitchen din ta isa window din da yakw sadata da kowanne kallo da ya danganci harabar gidan. Kamar zuciyarta zata fado sanda yake nufar sashen ruqayya,abinda tafi tsana kenan a rayuwarta,duk kuwa da cewa ita dinma hakan yake musu,baya taba shallake sashenta idan ya shigo sai ya fara dubata sanann ya wuce wajen ruqayyan yadda al'adarsa take kenan duk sanda ya kasance kece da girki. A nutse ta sauke idanunta ga ledar hannunsa,tanaso tasan meye a ciki?,saidai duk iya qwaqwarta ta kasa tantancewa saboda ledar baqace me duhu babba da qarama. Sakin labulen tayi yana jan tsaki,ta waiwayo ga haneefa wadda suketa wasan guje guje,wasan guje gujen da ya qarasa hargitsa gyaran 'yar burum burum din da ta yiwa falon. Tsawa ta doka mata sannan ta narka mata ashar "Ga babanku can yayi sashensu alhassan,bishi ki ga me ya shigo da shi a baqar ledar hannunsa" yarinyar kamar ba zataje ba,sai kuma ta zumbura baki tayi gaba "Zakici ubanki da shegen rashin son aike" ta sake binta da zagin idanunta kamar zasu fado saboda harara,sai kuma taja qwafa ta wuce bandaki a gurguje tanason watsa ruwa kafin yakai ga shigowa. Wani sassanyan yanayi ne da parlor din wanda ko yaushe baya rabo da shi saboda tsaftar da ya kamashi. Komai na tsaftace ne akan tsari da sanin darajar muhalli. Sassauqar doguwar riga ce a jikinta ta wani yadi maras nauyi ruwan madara me haske sosai,kusan duk shigarta tana yinta ne bisa tsari da favourite colours na saleem din. Alhassan da alhussain na zaune daga qasan carfet saman qananun duddumansu,kowanne jallabiyya ne a jikinsa farare da qananun hulunan tashi ka fiya naci. Kyau yaran sukayi kuma duk wanda ya kallesu dole su bashi sha'awa. Sallamar uban ta sanyasu hankulansu yowa kansa,al_hussain shi ya fara yo gaba yana qoqarin karbar ledar hannunsa hadi da fadin "Abba sannu da zuwa" wadda suka furtata kusan lokaci daya da al_hussain dake daukema abban nasu pillow daga saman kujerar don ya samu wajen zama. A duk sanda ya sanya qafafunsa a sassanta yakan jishi tamkar cikin wani muhalli na daban yake ba'a cikin gidan ba. Sau tari yakan tambayi kansa da kansa "Me yasa ya qaro aure?" Wani lokaci zuciyarsa da kwanyarsa kanyi hadin gwiwar bashi amsar "Rabo". Kamar ko yaushe a yau ma amsar da ta bashi din kenan,wanda yayi dai dai da ajjiye kaskon turaren wutan dake hannunta,ta kuma sauko daga dining area din yana gyara zaman dankwalin kanta me sulbi tana fadin "Barka da warhaka" "Barka kadai" ya amsa mata yana bin su alhussain da kallo wadanda suka nade abun sallarsu suka wuce dakinsu. Hannun 3sitter din da yake kai zaune ta zauna itama,idonsa ya dawo dashi kanta lokacin da ta miqa hannu ta jawo gorar ruwa me matsakaicin sanyi ta zuba glass cup tana miqa masa. Sai da ya saki murmushi sannan ya miqa hannu ya karba,ya shanye tas sannan ya miqa mata cup din "Na rasa wacce irin baiwa ce dake da har kike gane yunwata da qishirwata ba tare da na furta ba" murmushin ta kuma sakar masa "Da kallo guda daya tak da zanwa idanunka na gama samun amsar komai" kai ya gyada cikin gamsuwa tare da jin matsayinta yana sake zarcewa wani madaukakin muhalli a zuciyarsa. Kullum wayewar gari sai ya godewa Allah da bai bawa shaidan galaba a kansa a shekarun baya ya ingizashin da zai zama sanadiyyar rasa ruqayya ba,inda hakan ta faru?,yanzu da a wanne gurbi yake a rayuwa?. "Amma,me yasa ba kowacce mace ke da wannan baiwar ba?" Idanunta ta dan janye daga kansa,jikinta ya bata inda maganarsa keson dosa,don haka tadan juya ido kadan "Ya danganta da yadd kika zabi ki fuskanci mijinki ko ki mu'amalanceshi,hakanan ya danganta da iya adadin lokacinki da kuma kulawar da kika bashi". "Sai yaushe zainab zata dinga fahimtar irin wadan nan abubuwan tayi koyi dake ta kuma canza?" Dauke kanta ta sakeyi a karo na biyu. Duk girman matsin da zaya shiga muddin akan zainab ne bata da sha'awar ta shiga lamarinsu,lamarin miji da mata sai Allah,duk yadda take gani a yanzun a wata ranar tana iya ganin sauyin hakan a tattare dashi,duk da cewa zuwa yanzu ta jima da mance wannan lamarin "Ba'a sassa na kake ba,kada maman haneefa taga ka jima da yawa" ta fada tana miqewa, miqewar da taja hankalinsa har ya gaza dauke dubansa daga kanta "Au korata ma kikeyi?" Ya jefa mata tambayar da kafin ta bashi amsa turo qofa da shigowar haneefa taja hankalinsu. Rarraba ido ta fara yi tsakanin fuskar abban nasu da ruqayyan. Har cikin ranta ruqayyan tana jin babu dadi. Yadda yanayin tarbiyya haneefa take a gidan,akwai sakaci na bala'i daga wajen mahaifiyar da bata cancanci zama uwa ba. Duk da haneefa ta girmewa su alhussain nesa ba kusa ba,amma akwai nisan tazara me yawa a tsakaninsu,tun daga hankalinta zuwa nutsuwarta. Tsuke fuska saleem yayi ransa na baci,a tsawace yayi mata magana *HUGUMA* https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 04 "Halan baki iya sallama ba bare gaisuwa haneefa?" Ta tsorata ainun,don duk yadda yake sakewa da iyalansa amma sun sani,muddin ya dauki zafi da kai ko fushi to zakaji babu dadi "Sannu da zuwa abba,ina wuni?" Ta fada tana hade maganganun duka guri daya "Koma kiyi sallama" ruqayya ta fada a sanyaye. Sakin labulen yarinyar tayi ta juya zuwa waje,haushin tsawar da akayi mata tana cikata,tana ji a ranta maamantata ce ta jawo mata. Irin yadda taga su alhussain din sukayi haka tayi,ya amsa yana dauke kai,saidai cikin ransa yaci alwashi bazai dauki wannan sakarce sakarcen da yayi imanin laifin na Zainab ne,dole ya zauna da ita ya kafa mata sharudda da qa'idojin da zata yawaita tunawa kanta bazai dauki irin wanann ba. Ledar hannunsa ya miqawa ruqayya babbar "Ga mutanen naki" murmushi ta saki cikin jin dadi,kamar yasan a daren tana da buqatarsu,duk da al'adarsa ce tunda kayan suka zama abebadan shanta "Na Gode qwarai qwarai,kaima Allah ya faranta maka ya qara budi da wadata" "Ameen ya hayyu ya qayyumu, your prayers are my strength" ya fada yana dan lumshe ido. Idanunta ta kada masa tana murmushi,ya zare nasa idon da sauri yana yin gaba "Inda zan zauna n qara awa daya tak zaki cikamin kunne da magiyar na tashi na tafi yanzun kuma kina yin abubuwan da sun saba doka da qa'ida irin ta yau" dariya ya bata sosai,sai ta rungume ledar ta juya zuwa cikin kitchen don ta wanke kayan ta kuma adanasu cikin fridge. Shigowar haneefa ya sanyata dungure man data dauko zata shafa ta waiwayo tana bada hankalinta ga yarinyar. Tun kafin ya gama shigowa ta kasa jumurin jira "Me ya shigar musu dashi?,ina ledar?" Baki haneefa din ta tura alamun dake nuna tsiwa ta zauna mata sosai a jikinta "Ina zamana kin saka anyimin fada harda tsawa" "Ba wannan na tambayeki ba leda nake tambaya" ta fadi tana zaro idanu cikin takaicinta tana duban haneefar "Ya bata" ta amsa mata a a taqaice "Ya bawa wa?" Zainab ta fada tana zaro idanu cikin jin bala'i da tashin hankali "Mommyn alhassan" "Lallai yau an taro fitina a gidan nan,wallahi bazan dauki irin wannan abun ba" ta fada tana jin kamar zata dora hannu a kai ta rusa kuka. Tako ina saleem cikin jawo abubuwan da zasu kawo rudani a zamansu yakeyi,rashin adalci tako ina yake gwadawa rayuwarta,duk qoqarin da ita din keyi na ganin sun zauna lafiya ita kuma ta faranta masa. Tana tsayen da daurin qirjinta hannunta riqe a qugu ya tura qofar dakin hadi da sallama ya shigo. Kamar me ciwon wuya haka ta waiwayo da qyar tana amsa sallamar,bakinta zaka dauka ya cusa lomar biredi ne data hanata yin magana da kyau. Tuna fadan da ya gama yi mata yanzu yanzu ya sanya haneefa juyawa ta fice a dakin. A nutse ya qara takowa ciki yana karantar yanayin dakin. Mutum ne shi me wani irin qaqqarfar halittar jiyo qamshi ko warin abu,don haka a yanzun ma kusan abinda hancinsa ke jiyo masa sam baiyi daidai da abinda zuciyarsa keso da muradi ji cikin gidan sa ba. Mayar da dubansa yayi gareta,tana tsaye qerere tana binsa da kallon da baisan daga ina ta samoshi ba. Cikin daurin qirji,gashin kanta me tsaho da laushi ya samu guri ya cure abinsa saman kanta,wanda hakan ke nufin akwai dauda da rashin tajewa da ya zama silar wanzuwarsa a haka. Kauda idanunsa yayi,don idan da sabo za'a iya cewa ya riga ya saba. Cikin ranakun mako guda bakwai zaiyi wahala zainab din ta tsallake kwana biyu ba tare da ya ganta da daurin qirjin ba,walau da safe ko da dare kamar haka,ko yanzunma yasan qilan dashi ta wuni,bayan tasan babu abinda yafi tsana irinsa _Note:Da yawan maza sun tsani wannan al'adar,domin bata da wani alfanu sai canzawa mace yanayi,musamman idan ta hadu da nau'i na qazanta irin ta zainab,akwai wasu lokuta da mace kanyi daurin qirjin don jan hankalin miji,in a stylish way,ta yadda zaki daure bakin zanin a tsakiyar qirjinki kamar kin qulle abu,ki koma sassauto da zanin zuwa rabin qirjinki wanda hakan zai bashi damar gano pant da wasu sashe na breast dinki,bawai daurin qirji irin wannan na gargajiya mara ma'ana ba da fallen zani me dauda_ "Sannu da zuwa" ta fada da qyar a hakanma tana tausar zuciyarta ne gudun kada daren yau din ta sake tafka asara kamar yadda tayi a jiya "Yauwa,ya gidan ya yaran" "Lafiya lau.....mu ina tamu ledar?" Ta tambayeshi kai tsaye tamkar ita ta aikeshi. Daga kai yayi ya dubeta yana maimaita tambayar da tayi masan,qasan ransa mamaki yana cin ran nasa. Ya akayi tasan ya shigo da leda?,har yanzu bata daina wannan dabi'ar tata ba kenan ta shegen sanya idanu a