← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 40

Sashe 23

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

DUNIYA NE (ba ina nufin duka 'yan iska bane a'ah,amma kowanne namiji yanason rayuwa yana son holewa duk taurin kansa duk miskilancinsa) kada kiga mijinki ustaz ne ko shuru shuru kice ai wane ba ruwansa wallahi KI GWADA KI GANI ZAKISHA MAMAKI MUSAMMAN A OTHER ROOM sanda al'amura suka fara tafiya(DON ALLAH KARKICE KIN TSUFA,KO MISKILI NE wallahi za'a yi babu ke,namiji baya tsufa shikam wallahil azeem,me yasa idan sun auro sa'annin jikokinsu sai kiga sun zama tabararru kuyita zaginsa? ,tana masa abinda ke kike ganin tsufa yazo ba zaki masa ba,bayan cikin bedroom dinnan daga ke saishi,ba'a taron assembly kuke ba....ku yafemin mommies ). Wanda bakinsu haya shuru kuma bance ki bawa kowa labari ba bayan kin gwada,kiyita blushing abinki idan assignment dinki ya samu nasara ,ki sake fidda wasu hanyoyin kuma a kanki,sai shawara da zaki iya baiwa ga kowacce mace ta tsaftataccen harshe ba tare da kin bankadawa kanki asiri ba. Allah ya dawwamar damu da mazajenmu,wadanda basu da aure ya basu ikon kame kansu ya hadasu da mazaje salihai nagartattu. *Ruwan wanka me kyau ta hada ta fara wanka farko. Ta sake hada wani zata sakeyi,har ta dauko sabulunta yau kadai taji qamshinsa baiyi mata ba,ya tsaya mata a hanci da qirji,saita maida ta buda shower gel dinta ta matsa ta fara wanke jikinta. Ita dinma hakanan taji kamar wari wari takeyi mata,amma sai ta kauda kai cikin hanzari taci gaba da wankan tana Allah Allah ta gama. *********Tana zaune saman gadon asibitin bayanta jingine da bango. Tun a daren jiya kawo yau idanunta da hanakalinta yana kan matar da suka kasance su biyu ne a dakin. Matar da qyar take takawa cikin takatsantsan duk sanda zata shiga bandaki,amma jikinta da bakinta sun nuna ras take,hakanan babu wani me jinyarta koda mutum daya ne,sai wasu nurses guda biyu dake shigowa suyi hira su fice. Yadda suke magana da nurses din yasa ta fahimci kamar qawayenta ne,kuma cikin maganar tasu ta fuskanci kamar dinki aka yiwa matar,saidai kuma dinki wanne iri?,shine abinda hankalinta yafi karkata akai kenan taketa da kwadayin jin dinkin meye akayi mata?. Bata tashi fahimta ba saida nurse din tazo duba dinkin. Mamaki sosai ya kamata,iya saninta masu haihuwa akewa dinki a wannan wajen,to amma ita wannan ai sam bataga alamun ciki ko haihuwa tattare da ita ba. Hasalima batayi mata kama da matan aure ba,tafi mata kama da irin matannan 'yan duniya. Bata gushe ba tana ci gaba bin qwwqwafin matar,sai ta lura manyan wayoyi ne a hannunta,hakanan manyan kudade take fiddawa tana kashewa ko a jikinta. Tuni zuciyarta tayi nisa gurin son sanin wace matar?,wanne sirrine a tattare da ita?,tayita Allah Allah hajiyayye ta fita,don ta shirya tunkarar matar qila ta samu wani haske daga gareta. Cikin sa'a hajiyayye kuwa ta fita dubiya can ward na yara,da sauri ta sauka a gadon tana daura dankwalinta ta zura slippers dinta ta tunkari gadon. Tana kashingide tana danna iphone14 dinta hankali kwance,sai ta daga kai tana amsa sallamar zainab din tana binta da wani kallo. "Sannu ya jiki?" "Da sauqi" ta amsa ciki ciki tana ci gaba danna wayarta "Ni sunana zainab,kuma nice nake jinya a dakinnan" ta fada tana murmushi "Ayyah sannu" ta sake fada ciki ciki *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 19 https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39 *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* ____________________________ Ta amsa ciki ciki tana maida hankalinta akan wayarta. "Tambaya ce dani idan bazaki damu ba" "Inajinki" ta fada ba tare data sake kallonta ba "Don Allah kiyimin taimako ki gayamin meye amfanin wannan dinkin da akayi miki bayan ba haihuwa kikayi ba?" Ta qarasa fada cikin d'ari d'ari tana dubanta. Wani kallon tara saura ta watsa mata,don itakam tunda ta zauna a gurin hamamin jikinta ya addabeta,batasan uwar da tasa ta kwaso jiki tazo zata dameta ba. Ta buda baki zatayi magana daya daga cikin qawayenta nurses suka shigo "Jimmy,ya dai?,baquwa kikayi?" Maida kallonta kan nurse din tayi "Ni bansan me yake damun mutane da shiga sha'anin da bai shafesu ba....." "Wallahi ba haka bane,ina cikin kaidin kishiya ne,mafita nake nema don Allah ki taimaka ki gayamin" ta fada gabanta yana faduwa,kada taqi mata bayani wannan damar ta subuce mata. "Malama me kikeso?" Nurse din ta fada cikin sakewar fuska "Dinkin da aka yiwa qawarki nakeso ayimin bayani" murmushi ta saka suka hada ido da jimmy din,sai ta jawo kujera ta zauna tana fuskantar zainab "Wannan dinki shine kankat a fannin matsi,babu wani magani da zaiyi miki abinda kikeso sama dashi,yanansake tsuke gaban mace ya maidata tamkar budurwa 'yar sha hudu" . Tuni jikin zainab ya dauki rawa,gaba daya hanakalinta ya daga,yanzun duk wayewarta a fannin matsi akwai wani abu da yayi saura wanda batasan da shi ba?,ashe duk wayewarta bata kai ba?,koda yake dai dama shi ilimi ance kogi ne. "Don Allah malama ki taimakeni,nima inason ayimin,wallahi akwai matsala,na rasa hanyar da zan mallaki hankalin mijina,duk wani abu da mace zata yiwa namiji don ta mallakeshi ta hanyar shimfida nayi amma a banza,komai kyan magani nayi amfani da shi bana ganewa,idan kinga ya nuna jin dadinsa to sanda ya fita hayyacinsa ne bazai iya mallakar kansa ba wajen nunan jin dadin. Ni nafiso koda ba ranar girkina bane hankalinsa ya zamana yana tare dani,yana d'okin dawomin,wasu matan naga har satar kwana akeyi a kansu,amma ni koda wasa bai taba yi ba,tunda muka cinye amarci shikenan. Mijina ya auroni yana sona,ya auroni kuma don ya samu 'ya'ya dani,ni na fara haifa masa yara,amma bayan haihuwata ina yayewa saiga matsiyaciyar da ciki,wai data tashi haihuwa saiga twince,ina sake haife na biyu saiga wani cikij still ta sake haihuwa itama,wallahi malama asiri ne,ko cikin data samu aita hanyar tsubbu ne, mace batasan gyaran HQ dinta ba,batasan komai ba......kunsan Allah na fita hasken fata nesa da kusa ba,ita ko irin dan man nan da ake gogawa a murtsike baqi bata sawa jikinta,ko gashi ma wallahi gashinta baifi rabin nawa ba...." Tana cewa gashi jimmy data saki baki tana kallon yadda take zuba ratata kamar an kunna famfo ta maida kallonta ga sumartata. Baki ta tabe,ko ita da take mace tsantsami ta bata ta yaya zata burge namiji?,aba a qudundune?. "Don Allah nurse ki gayan bakya tsuke guri baka damsasashi ta yaya miji zai soki?" "A'ah babu fa zee baby" nurse ta fada tana qarewa zainab kallo a fakaice dariya da takaici suna kamata "To kin gani.....yanzu yaushe za'a yimin dinkin?,kuma nawa ne?" Ido nurse din ta dan juya "Eh to,ke zaki zabi watanni,dinkin kuma na musamman ne ai,a qalla zaki ajjiye dubu tamanin haka,don idan akayi miki kuma shikenan keda neman maganin matsi har abada,shi kansa oga idan ya kawo ziyara kullum inajin saikin taimaka masa zai samu gurbi" Duk da kudin da nurse din ta cika mata yayi yawan da bata dasu amma kuma amfanin dinkin take dubawa. Fuskarta ta yalwata sosai da fara'a "To shikenan,yanzu dai bani da wannan kudin a hannuna,amma mai gidan zai tafi umra inajin nan da kwana goma ne ko sati biyu,yana tafiya da sati daya za'a yimin kafin nan na hada kudin,sannan ma zai kasance kafin ya dawo na warke,zansan yadda zanyi zan lissafa kwanakin yabar qasar nan cikin kwanakina,yadda idan ya dawo kwanana ne " "To shikenan,ba laifi " nurse din ta fada. Godiya sosai zainab ta dinga kwarara mata,tana ji a jikinta lokaci yayi na maganin matsalarta. Wannan karon indai ta samu yadda takeso hatta saleem sai ta garashi yadda takeso,ba kullum zai samu ba,don ta tabbatar muddin yaji yadda ta sake komawa sai abinda hali yayi. Bayan zainab ta wuce bandaki duban nurse din jimmy tayi "Amma dai talatu baki da imani,yanzu don Allah don Allah inake ina wani dinki bayan ke kanki kinsan ba'a nan akayi dinkinnan ba?,nazo ne kawai nan na warke saboda kawar da hankulan jama'a?" Gyara zamanta tayi tana dariya "Allah ne kawai ya kawomin rabona har gida, karba zanyi na kankareta na dinke abinda ya samu" "Amma dai da kin gaya mata gaskiya ina ganin da shi zaifi,taje ta fara gyara jikinta,baiiji irin samamin da take bugawa ba?" Dariya talatu ta kece da ita har sai data kama bakinta ta riqe gam bayan data tuna zainab din tana bandakin "ke ni Allah yasa ma na iya bankadata,don wallahi wannan da alama can wajen ma ba sauqi,danqari!" Ta sake fada tana dariya. Tabe baki jimmy tayi tana gyara zamanta "Kyaji dashi dai,ni mijinne ma nake ganin qoqarinsa da yake iya maaja din jikinsa da nata" "Ke qazaman matannan ai jarababbun maza ne,yo ita ai na tabbatar miki ko abinci ya hanata ba lallai ta damu ba akan ya hanata abinsa,shan HARKA MEDICINE ai yafi musu komai muhimmanci koda sallah bata fiya samun lokacinsu haka ba" baki ta sake tabewa "Lallai,irin wannan ba dole mu qadangarun bariki 'yan kwalta mu qwace musu maza ba,kiga mace kamar tsohuwar jaka a gidanta amma wai a haka take so ta mallaki miji?,wata macen ko ke bakya bata burgeki wallahi bare miji. Jikina talatu duk wata sai nayi masa gyara,gyaran fata kawai fa na dubu hamsin,a turarani,a qamsasa ni,to ta yaya maza ba zasu liqemin ba?,kazo nan kaji lumus,can qamshi can taushi,ka koma gida ka tarar da qamaya maya........Da anyi motsi mace take miki namiji bashi da adalci,namiji dan kunama ne,namiji bashi da mutunci,namiji batulu ne da sauransu,bayan ke kika siyawa kanki,habba.....muddin akwai mata irinsu zainab a duniya to kasuwar karuwai ba zata taba mutuwa ba" Dariya talatu ta saka "Yo yanzu wannan kika jera da ita ai cewa za'a yi 'yar aikinki ce" "Allah ya kiyaye,wallahi ko masu aikina basu isa su zauna da irin wannan qazantar ba" jimmy ta fada tana kyabe baki alamun mugun tsantsami ya kamata. Ranta fes ta koma gadonta,duk bayan mintuna biyu saita kalli jimmy ta sakar mata murmushi tare da yi mata sannu. Gaba daya jimmy ta gama tafiya da ita,jikinta ya bata tsabar yadda HQ
Chapter 23 · 0% Book details