Sashe 25
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciki,haba mana,ki barni naji da abinda yake damuna" "Kiji da abinda yake damunki nima zanji da nawa,don wallahi gida zan wuce,kuma ko ya tafi indai kinsan baki kwashe kayan qazantarki kafin nazo ba kada ki kirani" "Haba dan hajiyayye zo mana" zainab din ta fada tana sasaautowa,don tasan ba wanda tafiyarsu zatazo daya da ita sai hajiyayyen "Kiyi haquri raina ne a bace don Allah" "Sakeni" ta fada tana zare hannunta ta koma kitchen din tana qunqunin mita "Dadina dake shegiyar mita wallahi" zainab din ta sake fada tana jan tsaki hadi da hararar inda hajiyayye ta wuce,saita gyara zamanta tana ci gaba da qulla wadda take ganin zata fishsheta. Tunda ta zauna wajen ta gaza motsawa,gaba daya komai ji take ya dagule mata. Ba irin tunanin da bata saqa ba akan cikin ruqayya,har addu'a take cikin ranta "Ya Allah kasa zuwa gobe da safe ta hadu da mummunan tsautsayin da zai kawo sanadin zubewar cikin". Duk zaman da tayi a wajen ta rasa wanne zata kama?. Dagewa zatayi tayi ciki?,ko ta bawa banza ajiyar saleem din ta dage tayi ciki?,idan ta haihu sai a dinketa gaba daya?. Tafi gasgata wannan shawarar kuma tafi yarda da ita,don haka dab da magariba ta miqe daga wajen data jabe ba azahar ba la'asar,duk da yadda hajiyayye keta fama da ita ta miqe din,ta wuce bedroom dinta ta wawwatsa ruwa don sauri takeyi kafin ayi kiran sallah ya zamana ta fito kafin salim din ya shigo gurinta. A gurguje ta biya bashin sallarta,sannan ta bude locker dinta tayi hadin magunguna,tana ji a ranta zata sake dagewa da gyara,don ta shirya samun ciki a wannan dan tsukin,idan so samu ne ma kafin yakai ga wucewa umra. Wata rigar shadda ta saka,wadda wuyan da fadin yadanyi mata yawa saboda sanda akayi dinkin tana da ciki tayi qiba sosai,yanzun kuwa ta zazzage ta koma ainihin jikinta. Ko kadan bata fiya damuwa da sauyawar fadin rigar ba saima jinta sakayau da takeyi saboda wankan da take jin tayi,sannan kuma aka dace shaddar wankakkiya ce,duk da babu shaidar guga a jikinta ko na gamin gafara. Parlor ta fito ta samu hajiyayye tare da yaran tanata fama dasu wajen gyara musu yanayin cin abincinsu,yau sashen fes yake hakanan abincin yau da hankalinsa,saita hakimce saman kujera tana dakon shigowarsa,a hankali tana jin maganin yana mata aiki,cikin qasan ranta take fatan inama ace a wannan daren ta samu rabo itama?, tabbas a yanzu 'yan biyu sune burinta,kai idan da hali ma guda uku zata roqa,so take ruqayya ta tabbatar da cewa da gaske fa gida ya zama nata,qila hakanne kadai hanya guda daya da zata saka ta saduda. *Kuyi manage,mu hadu gobe in sha Allah,na gode da haqurin jirana* *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 21 Kusan tunda ya ajjiyesu ya fita yake fama da ciwon kai. A haka dai a daddafe ya zauna a kasuwar saboda lissafin shago sukeyi na qarshen sati,dole kuma akwai buqatar ya zauna din gudun rubuta kuskure. Sanda ya qaraso yaran suka baibayeshi suna masa sannu da zuwa. Bai taba shigowa gida bannu haka ba komai,duk qanqantar abu sai ya kawo musu tsaraban kasuwa(wannan halayya ce me kyau,tana qara danqon soyayya tsakanin iyaye da 'ya'yansu,iyayenmu na da zaiyi wahala kaga sun shigo gidansu haka,koda ma'aikata bare 'yan kasuwa). Kai tsaye ya kama hannun iftee suka wuce sashen ruqayya yana tambayarsu mamar tasu "Daddy tana kwance tun da safe,mommy kamar bata da lafiya" iftee ta fada cikin karyar da muryar "Batajin dadi amma zata warke very soon in sha Allah" ya fada yana murmushi. Sanda suka shigo ta gama alwalar sallar magariba dake gabatowa tana sanya hijabinta "Sarkin tsafta"ya fadi a ransa,duk da batajin dadi amma sashen fes yake kamar kullum. Fuskarta dauke da murmushin nan take dubansa "Sannu da zuwa" ta fada "Yauwa,ke za'a yiwa sannu maman wasu twince din in sha Allah" yaran tadan kalla ta gefan ido tana bude baki kadan "Daddy,bakaso na huta" "Hutun me?,me ya rage banda ki cikamin gida da yara,inaso na ganni da yara masu yawa Allah ma ya sani,sai gashi Allah ya qaddara zaki zama uwar 'ya'yana" "Uhmmm,yau kuma ni za'a baiwa wannan matsayin kenan" tayi maganar tana zura hannun hijabinta. Dan kallonta yayi sai ya basar,yasan gori takeson yi masa "Baki da mantuwa" ya fadi qasa qasa sanda yake zama hannun kujerar dake daura da ita,saita daga kanta,har zatace wani abu kuma sai ta fasa "Baka da lafiya" ta fada a hankali. Idonsa ya lumshe yana jin qaunarta har qasan ransa,ita daya ke da qarfin maganadisun iya karantar kowanne motsi nasa "Kaina" ya fada a taqaice "Subhanallah,daddy bakason shan magani,tsaya kasha magani don Allah" ta fada cikin nuna maqurar damuwa "Ki barshi idan na huta zan koma normal " kai ta girgiza cikin narkewa "Kada muyi haka da kai daddy,yanzun idan wanine yace hakan sai kayita fada,mu shikenan ba zamu kula da lafiyarka ba?,waye muke dashi mu da yaranmu sama da kai?" Idanunsa da ya zuba mata ya lumshe gami da sakin murmushi "Shikenan ranki ya dade" yadda ya kalletan taji kallon har cikin jikinta,idanunsa mada matuqar tasiri har yanzu ga zuciyarta. Ba jimawa ta dawo da maganin ta balla ta miqa masa hade da gorar ruwa,baikai ga sha ba saiga haneefa Ibrahim yana biye da ita suna raba ido. Koda basuce komai ba tasan turosu akayi suyi CID,don haka tana gama bashi maganin ta juya daki dasu,shi kuma ya waiwaya yana dubansu. Kallon shi kadai yasa suka gane laifinsu,suka koma da baya suna sallama,ya amsa yana miqewa,ruqayya ta qaraso da abun sallah "Na gode" yace yana yin waje "Wajibina ne" ta amsa masa tana shimfida abub sallar. Yana sallama da ita ya fara cin karo,sai cika takeyi tana batsewa hadi da kumbura. Yi yayi kaman bai ganta ba,yayi sallama yana saka kai falon. Hajiyayye ce ta amsa ta miqe tana masa sannu da zuwa,ya amsa yana zama cikin kujera,har zuwa sanda hajiyayye tabar musu gurin. "Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki kamar wadda aka yiwa dolen faden "Yauwa,ya jikin?" "Ka damu ka sani ne?,tunda tunda ka tafi baka ko kirani ba,ka dawo kuma kaje ka zauna a wajen wadda ba girkinta bane" ta fadi cikin hasala. Idanu ya zuba mata kafin ya janyesu "Wannan qorafin idan da sabo ya kamata bakinki ya gaji da fadinsu,kullum ke kenan cikin qorafi akan na shiga ganinsu?,bayan ita ko sau daya bata taba qorafi akan shigowata wajenki ba?" "Eh dama mana ai bazatayi ba tunda tasan tana cutata" ta fada tana gyara zamanta da alama da gaske ta shirya tayita zabgo qorafin. Ganin hakan sai ya miqe tsam kawai abinsa yana wucewa bedroom dinsa,cikin ransa yana mamakin yadda yau sashen yake fes. Amma yana shiga dakinsa ya tabbatar ba itace tayi gyaran gidan ba,don bedroom dinsa yadda ya tafi ya barshi ranar data fita a girki haka ya dawo ya sameshi. Da hannu ya tattara tarkacen ya zauna gefan gadon yana jira maganin ya ratsashi. Tsahon wasu mintuna zuwa sanda yaji an fara kiran sallah ya miqe ya wuce toilet ya daura alwala sannan ya fito don wucewa masallaci. A inda ya barta a nan ya sameta ita da hajiyayye,dama ita din tun da batasan wai tabi miji daki ko ta kebe dashi idan ya dawo daga aiki ko wani guri ba,saidai ya qaraci gararambarsa ya gaji "Ki shiga ki gyaramin dakin nan" daga kai tayi ta kalli hajiyayye "Don Allah qarasa ladanki mana 'yar hajiyayye" ta fada tana karyar da murya alamun lallashi. Kai hajiyayye ta daga suka hada ido da saleem saita sunkuyar da kai. Bai dauka haukan Zainab yakai har haka ba da zata aika masa bazawara gyaran dakinsa. Wani kallo ya jefeta da shi ya saka kai kawai ya fita a sashen. Karfe goma na dare ta shiga bedroom dinsa, idanunta a kanshi yana zaune daga gefan gadonsa yana dan duba waya sama sama,shigowarta sai ya kammala abinda yakeyi din ya ajjiye wayar. Idonsa yadan lumshe saboda yadda yakeji yana dan sara masa,a hakan maganin da ruqayyan ta bashi ya sassauta akan lokacin da ya shigo gidan,sai ya maida bayansa yadan jingina da gadon bayan ya zame kadan ya kwanta a rabin gadon bayansa. Lokaci lokaci yana karantarta sanda take shige da ficenta abunta,ko sau daya bata nuna ta fahimci wani rashin lafiya tattare da shi ba,duk da ko abinci ma kadan yaci don ruqayya yau bata samu zuwa cin abincin ba,to shi dinma bakinsa ba taste shi yasa bai samu ci da yawa ba,kota wannan bangaren a nasa ganin ya kamata ta fahimci akwai abinda yake faruwa amma hakan bai samu ba. Ita kawai sabgar gabanta take,sauyawar miji ta kowacce siga bata daukeshi wani abu da za'a bawa kulawa ba. Ta nata bangaren Idanunta a kansa jifa jifa tana satar kallonsa,ranta da zuciyarta ba abinda suke raya mata illa sauyawarsa na da nasaba da son bijire ma buqatarta,ita kuma taci alwashin ba zata lamunci a danne mata haqqi ba,ire iren wadan nan abubuwan ma qila suna daya daga cikin sanadin da ya sanya ruqayya ta rigata samun wani cikin. Gadon ta iso ta zauna daga bayansa,zuwa sannan yaja blanket ya rufe har kafadarsa saboda sanyi sanyi da yakeji na alamun ragowar zazzabin jikinsa bai tafi ba "Ina da buqata" ta fada sankankan kamar me bada labari. Ya dade da sabawa da wannan halayyar tata,sam bata da wani salon nunawa me gida buqata data wuce wannan "Banajin dadi yau,nasha magani ina buqatar na huta" wani abune yazo yayi mata tsaye a wuya. Ji take zuciyarta kamar zata fashe "Eh,ai dama na fuskanci take takenka,to ko baka da lafiya nidai haqqina nake da buqata" waiwayawa yayi kadan ya dubeta da kyau "Kizo ki qwata idan kina iyawa" ya fadi cikin matuqar maqurar jin haushi. Mutum kamar dabba,ace ko da yaushe shi kam baisan dai dai da ba dai dai ba,yana takaicin yadda sam zainab bata gane lafiyarsa da lalurarsa indai ba kwanciya yayi magashiyyan ba,koda yaushe tata buqatar ce s gaban tasa. Bai gama wannan tunanin ba sautin kukanta ya karade masa kunnuwa,cikin muryar kuka take cewa "Ai dama na sani,koda baka fadi haka ba komai ya fito a aikace,ni nasan dama da gayya ka yiwa ruqayya ciki ni baka yimin ba,to nima ciki nake da buqata haihuwa nakeso,banda ma rashin adalci ni da nake gyaran nan aini yafi