← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 40

Sashe 14

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanyasu su dinga canza halittar Allah,cikin canza halittar Allah wadan nan abubuwan suna daga cikinsu,kisha magani ki qara qiba,kisha magani don ki sirance bayan qibar ba matsala take kawowa ga lafiyarki ba,ki shafa mai kiyi haske ko ki shafa mai don kiyi baqi duk da mu an jarabci mutanenmu da son suyi haske ne kawai,duk da ana samu cikin turawa da yahudawa masu maida fatarsu baqaqe,duk me ya kaiki wannan wasila?" "Ina zuwa" ta fadi tana dagawa ruqayya hannu sakamakon kiran da ya shigo wayarta. Da kallo ruqayya ke binta da shi har ta gama amsa wayar tana gatsine gatsine hadi da amsa maganarsa da qyar. Wayar ta wulla gefe tana jan siririn tsaki "Sirikin namu ne?" Ta tambayeta tana ciro tata wayar daga jaka ta kirayi shukra taji yaushe zasu iso "Wa?,Allah ya kiyaye,sulaiman ne fa" tsayawa ruqayya tayi da abinda takeyi tana duban wasila cike da mamaki "Sulaiman dinne abun Allah ya kiyaye?,badai sulaiman wanda yazo duba umma sanda aka kwantar da ita a asibiti ba" "Shine,amma ke kinga mijin aure a nan?" Ta jefawa ruqayya tambayar tana kallonta "Ni kuwa naga mijin aure nagartacce ma,me sulaiman ya rasa?" Baki wasila ta tabe tana jawo carbinta ta saka a yatsarta ta fara ja tana cewa "Abubuwa da yawa mana,haba ruqayya kamar makauniya?,yana da rufin asirinsa yana da hali me kyau,amma gaskiya kamar bai qarasa irin mijin da nakeson aure ba" Mamaki ya qarasa kashe ruqayya "Amma yanzu bake na samu kina wasu wuridai ba duk akan Allah ya kawo miki miji kiyi aure ki huta ba?" "Eh amma mijin ai ba kowanne iri ba,irin sulaiman ina dasu sun kusa hudu,amma wanda yadanfi hakan rufin asiri nake nema,bance saimai shahararren kudi ba,amma ina laifin miji kamar naki saleem din,ke ba motar hawa gareki ba yanzu ke da kishiyarki?" Kasa cewa komai ruqayya tayi mamaki yana ci gaba da kamata "Kuma ma dazu dazu na dawo daga gurin wani bawan Allah,yayimin istihara ya gayamin aure na da isma'il babu alkhairi a cikinsa sam sam,mijina yana nan zuwa,dan kasuwa ne a kantin kwari,kinga kuwa ta yaya zan tsaya ina dagawa kaina hankali akan wanda nasan ba mijina bane" "Shi din Allah ne da har zai fadi abu ki yarda?" "Amma istihara ai ba qarya bace" "Wacce irin istihara yayi miki?" "Normal istihara da aka saba,carbi ya ajjiyemin yace na zabi daya,da na dauka na miqa masa ya karba na wasu mintuna sai yayi min bayani,babu qasa a wajen bare dai kice min duba ne" wasila ta fadi cikin gamsuwarta da abun. Cike da takaici ruqayya ke girgiza kai tana duban wasila "Wai duk yawon islamiyyar da muka dinga yi ina naki karatun yayi wasila?,dama haka annabi ya koyar da istihara?,suna fakewa da duba suna canza masa suna da istihara?,wallahi sai sunyi shari'a da annabi,ba wani wanda zai maka istikhara kai zakayi abarka da kanka,bayan kinyi sallar raka'a biyu zaki karanta *_Allahumma inni astakhiruka bi'ilmika,wa'astaqdiruka bi qudratika,wa'as'aluka min fadlil azeem,fa'innaka taqdiru wala'aqdir,wa ta'alam wala a'alam,wa'anta allamul guyub,Allahumma in kunta ta'alam anna hazal amra(saiki fadi buqatarki)kairul lee,fi diny wamu'ashy wa'aqibatu amry,fayassirhu ly summa barikhly ly fihi,wa'inkunta ta'alam anna hazal amra(saiki fadin abun),sharrully fi diny wamu'ashy wa'aqibatu amry fasrifhu anni,wasrifny anhu,waqduriliyal khairu haisu khana,summa ardini bihi) annabi yace ba wanda ya taba istikhara irin wannan bayan yaji ya gamsu da abun ya zartar da shi,daga baya kuma abun ya zame masa nadama,idan kayita kayi shawara da mutane nagartattu guda biyu akansa sannan ka zartar" . Kai wasila ta kawar tadan mele baki sannan ta dawo da dubanta ga ruqayya "Na gode da tunasarwa,amma na jima ina yin wannan ai,sannan shi kansa abinda ke faruwa jifana akayi,mutum kusan biyar suna gayamin asirin akayimin don kada na auru,ina da magauta da yawa da maqiya,duk wanda naje gurinsa cewa yakeyi a gaba aka sakoni" "Babu wanda yasan gaibu sai Allah,amma asiri gaskiya ne yana kuma iya kama mutum,saidai bisa amincewar Allah ne,ba wanda ya isa ya cutar dakai sai Allah yaga dama,akwai kuma ayoyi daga alqur'ani da tsafatattun hanyoyin warware sihiri da kuma kare kai daga sake kamuwa dashi,kamar cikin suratul a'araf......" "Duk fa inayinsu amma.....hmmmm" sarai ruqayya ta fahimci me takeson cewa,sai ta gyara zama "Eh bata karbu ba kikeson cewa?,ko kin dade kinayi ba nasara ko?,to bari kiji wani abu da baki sani ba,ita kanta addu'a tana da qa'idojin yinta da amsata.....indai zakiji a ranki addu'arki bata karbu ba to kin wargazata,indai zakiyi......" "Kinga rubutamin addu'o'in saina hada dasu" ta fada tana zaro biro da memo ta miqa mata,sannan ta miqe tana fidda kayan jikinta. "An kusa kiran sallah,akwai hayaqin da zanyi kada lokaci ya wuce,ina zuwa" ta fada tana daura zanin fallen atamfa tana fita a gaggauce daga dakin. Da kallo kawai ruqayya ta bita dashi,saita girgiza kanta takaici yana kamata,cikin qasa da minti biyu qaurin hayaqi ya risketa a nan inda ta barta a zaune. *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 11 https://www.mkdatasarvices.com.ng *MK DATA SERVICES* _ake magana_ *_INA MASU SARIN DATA,BIYAN BILL KO SUBSCRIPTION KO MASU SIYAN DATA DIN MA KADAI DON AMFANIN KANSU?_* *_TO KU MARMATSO KU BANKI ARON HANKULANKU DON KADA AYI BABU KU!!_* *_GA WANI SASSAUQAN WEBSITE DON SIYEN DATA CIKIN FARASHI ME SAUQI DA RANGWAME_* https://www.mkdatasarvices.com.ng _Ga me neman qarin bayani ko magana dasu kai tsaye sai ya tuntubesu ta wannan number wayar_ 08038258489 *ARAHA SAUQI DA RANGWAME KAMAR AN BAKA A KYAUTA* Tana saka kanta a tsakar gidan umma tayi sallama "A'ah,baqi mukayi?" Umman ta fada cikin fara'a. Tun asali ita din macace me kirki da qoqarin zumunci,saidai ubangiji ya jarabceta da dabi'ar son 'ya'ya. Irin matan nan ne da basa iya boye soyayyar yaransu,wannan ya sanya abubuwa da yawa da yaran zasu aikata ba kasafai suke iya tsawatar musu akai ko su hanasu ba. "Sannu da zuwa umma" ruqayya ta fada tana murmushi,a ranta tana jin dadi me yiwuwa umman yanzu data shigo ta taras da uban qauri hayaqin turaren ta yiwa wasila fada,iya zallar qaurin ta isa ta sanya ka samu matsala idan kana da cutar asma "Tun yaushe kika zo?,munyi sabani naje barka 'yar hannatu ce ta haihu" ruqayya na qaramar dariya taja kujerar 'yar tsugunno ta zauna kusa da umma da ita ta zauna saman kujerar bayan ta fidda mayafinta ta rataye jikin igiya "Ahhhh,umma hannatu ce yanzu da jika?,lallai rayuwa tana gudu" "Uhmm,kedai bari kawai,shi yasa yanzu gaba daya hankalina ha koma kan 'yar uwarku,ta samu itama tabar gidan nan,kada na mutu banga aurenta ba" umman ta fada cikin karyewar murya. Gyara zamanta ruqayya tayi "Umma kada ki damu,muddin kina mata addu'a akwai lokaci shi aure kaman haihuwa yake muddin yazo sai anyishi ba abinda zai canza,lokacinta ne kawai itama baiyi ba" baki umman tadan tabe kadan fuskarta fal alhini "Uhmmm,mutanene yanzu sun zama abinda suka zama,baka takawa mutum ba baka barar masa ba amma sai ya saka ka a gaba sai yaga bayanka,nidai tunda nake ban tana jifan dan wani da ko Allah wadai ba,amma ni tawa diyar ita kenam qwaya daya an hanata ta motsa" cira kai ruqayya tayi tana kallon umman,alamu dukka sun nuna itama ta yarda da cewa jifa aka yiwa wasila,itama nata idanun sun rufe da tarin kura kurai da dabi'u da ya kamata wasilan ta fara gyarawa saboda ta samu tsakaninta da ubangijinta yayi kyau ta yadda addu'arta zatafi shiga. Sau tari mune sila na rashin karbuwar addu'o'inmu,amma saimu danganta sanadin ga wani ko wata. "Don Allah umma kada ki saka wannan a ranki,hadisi ne guda daga ma'aiki cewa,idan da dukka mut anen duniya zasu taru don su cutar da kai,ba zasu iya cutar da kai ba sai abinda Allah ya rubuta a gareka,hakanan idan da dukkansu zasu taru don su amfanar da kai basu isa su amfanar da kai ba sai abinda Allah ya rubuta a gareka zai sameka" "Uhmm,kedai Allah ya rufa asiri kawai,ina kishiyar tawa da masu gidan nawa?" Kamar jira suke umman tayi tambayar sai ga sallamarsu,suna gaba yusra na bayansu. Da gudu suka qarasa shigowa kamar wadanda suka shekara basu ga mamar tasu ba. A jikinta suka zube iftee ta haye cinyarta "Ku dagani hakanan ku gaida umma" ruqayya ta fada bayan duk sun gama ifce ifcen. Daya bayan suka durqusa suka gaidata har ifteehal da take qarama. Umman ta amsa tana shafa kawunansu sannan tace "Allah ya nuna mana yaran wasila haka,da tuni itama nata yaran sunkai haka" "Lokaci dai umma" ruqayya ta fada tana wucewa bakin famfo don yin alwala. Tana fitowa ta ji umman na magana da waseelar,waseelan tana sake mata bayanin abinda malamin ya gaya mata "Wallahi umma da kin barni na tambayeshi,ya gayamin su waye da waye,na rantse da Allah duk randa aurena ya tashi kaf sai na tambayi sunansu,sai naci(ta dura ashar),kuma wallahi wallahi ba wanda zai moreni,ba wanda zaici arziqina,kada ma daga baya kice ai ya wuce na yiwa wance kaza na yiwa wance kaza,arziqin mijina nawa ne saike sai 'ya'yana da wanda naga dama" ta fada tana shanye ragowar rubutun dake cikin leda ta jefa ledar cikin kurfetunsu na girki "Ki barsu da mugun nufinsu,duk wanda yayi na gari kansa ai ko?". Sake cika da mamaki ruqayya tayi,gaba daya wasilan ta sake canzawa,duk wasu halaye da ruqayya tasan wasila dasu ta ninko wasu a kai wasu kima ta sauyasu gaba daya. Tana salla amma mamaki ya gaza barin kanta,ita wasila dake wannan zancan har ma tasan me kudi zata aura kenan da take zancan ba wanda zaici arziqinta. Kafin ta gama sallar wasila ta shigo dakin,ta nade saman katifarta tanata amsa waya,ko muryarta ma ba'a ji iya ji sosai saboda tsabar sanabe da langwashe murya. Waiwayawa kadan tayi ta kalleta sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da lazuminta tana sauraron kusur kusur din wasila saboda bata iya jin muryarta sosai. A gaban umma ta fara wayar,sai daga bisani ta tashi,tana mamakin yadda take iya zance tsaf da saurayi a waya a gaban umman ko yayyenta,ba tun yau ba ta saba hakan dabi'arta ce. Dai dai sanda ta shafa addu'a wasilan ta saki siririyar qara "Da gaske don Allah?.....wow......bari na shirya" ta fadi tana katse wayar gami da saukowa daga katifar "Ki tayani murna 'yar uwa, iphon 13promax yanzun nan za'a kawomin ita" wasila ta fadi tana bude wardrobe dinta tana zubo da kayan ciki qasa. "Toooo.......isma'il dinne?" Waiwayowa wasila tayi ta zabga mata
Chapter 14 · 0% Book details