Sashe 2
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki raba alaqar da Allaj ya hada ba,kuma a juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,dole wataran zai fashe" tana kaiwa nan ta juya a zafafe tana jin inama zai yiwu ta rufe ruqayyan da mummunan dukan da zai sanya a rasa gane ainihin halitattarta. Duk kuwa da tayi imanin babu wani kyau dake rudar saleem tattare da ruqayyan,face zallar tsafi da tsubbace tsubbace,tunda dai indai ana batu na kyan fuska da hasken farar fata,ko kusa ko alama ruqayya bata isa ta matso koda gefanta ba,wannan abun shi yake sake bata tabbaci a ko yaushe iyawa da gogewa a bun malamai da 'yan bori suke sanyawa ruqayyan ke shan gabanta a zuciyar saleem,wanda dukkan me dogon nazari da tsinkaye koda ba'a gaya masa hakan ba shi da kansa zai fahimta. Kasa ce mata komai ruqayya tayi face binta da kallo data ci gaba da yi har ta bacewa ganinta. Taja numfashi sosai sannan kuma ta sauke tana rausayar da kai. Koda sau daya bata taba tsaiwa ta biyewa shirmen zainab ba,amma a yau abun yayi ta'azzarar da har ta samu qwarin gwiwar shigo mata sashe?. Karamin tsaki taja ganin qananun tunane tunanen matsalolin Zainab da basu taba qarewa cikin gidan ba suna neman bata mata lokaci,saita juya zuwa kitchen zuciyarta na sake fadada da tunani da mamakin halayen Zainab din. Me yasa har yanzu IDON ZUCIYARTA ya kasa budewa?,ta gaza fahimtar abinda ke gabanta a bayyane?. Da irin wadannan tunane tunanen ta kammala dauraye plates da cups din da wanke kowanne kwano da aka bata da abinci ya zame mata jiki a duk sanda aka gama cin abincin,ta goge ko ina da kitchen towel ta sakayo qofar. Tsaftataccen killataccen bedroom dinta ta buda ta shiga,ta kalli agogo,sai ta bude wardrobe dinta ta ciro mayafinta daya dace da da A shape din atamfar dake jikinta a dan gaggauce ganin lokaci ya fara ja,tanason taje ta dawo da wuri kafin yaran su dawo daga makaranta,don ta dade da yiwa kanta alwashin muddin ba wani babban uzuri ba ta daina barwa zainab su saboda wani dalili. Ta dakin yaran ta biya ta dauki baby fatima dake barci ta sakata a kafada sannan ta maida lallausan mini blanket din yariyar ya lullubeta ta fito. *FREE BOOK NE,KU SAKI JIKI KUSHA KARATU* *_FOLLOW MY AREWABOOKS ACCOUNT_* *HUGUMA* *_KURMAN BA *H U G U M A* PAGE 02 Muhallin da ta tashi dazun a dakin shi ta koma ta zauna,har yanzu babu wani sassauci data samu ko qanqani,duk da cewa daga ruqayya har saleem ta barwa kowa a cikinsu saqo. Sam bata damu da tarin qazantar dake a sashen nata ba bare hankalinta ya dauku wajen ganin ta tsaftace shi,duk kuwa da cewa rana ta fara yi,kuma lokaci ne da ya kamata ace gurin ya kasance cikin kintsi da gyara. Ba abinda yafi damunta irin uban kudadenta data kashe,ta siya magunguna masu tarin yawa na mata,magungunan da aka bata tabbacin sunansu KAFI MALLAKA. Kuma muddin tayi amfani dasu ba saleem ba,duk wani wanda yake rayuwa da saleem ma zaya zama qarqashinta ikonta da zabinta ne. Sai gashi gaba daya daga kudin har maganin babu abinda ta amfana dashi,maganin da yake na kwana biyu ne,tayi asarar dare daya,saura dare daya ya rage mata,wanda bata da wani hope a kanshi,saboda bahaushe ma ya fadi juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Irin rabuwar da sukayi da saleem a yau bata tunanin zai nema wani abu daga wajenta a daren yau din,ita kuma batajin koda zatayi asarar kudin data zuba zata iya saukar da kanta ta nemeshi,muddin ba shine akayi katari ya saukar da kanshi ba. Koda bai bata haquri ba tana iya sallamawa,saboda kaf kudaden da ya basu ne saboda siyayyar sallah tasu data yara ta narka a ciki cike da yaqini da imanin zata maida mafiyinsu muddin tayi amfani da maganin. Kamar wadda aka tsunkula ta miqe da sauri,ta sanya hannu tana jawo locker din madubinta. Tarin ledoji ne da tarkacen da zakayi tsammanin qaramar bolar mahaukata ce dake cunkushe da karikice,wasu a leda,wasu a kwalaye,wasu a takarda,wasu ma saboda rashin gyara da kintsin gurin sun fashe sun barbade a cikin locker din. Da kallo tabi locker wani takaici yana sake ninkuwa a zuciyarta "Wai dame na gaza da har yau na kasa ture wannan baqar matar tasa?,dame ruqayya ta fini ne?" Ta tambayi kanta tana qarewa locker din kallo,tako ina bata wasa da gyaran HQ dinta,duk wami magani da zata gani ana tallatawa,ko taji labarin kyan ingancinsa da aikinsa a gurin qawaye saita tabbatar ta mallakeshi hankalinta yake kwanciya,amma har yanzu ta gaza samun nasarar da take hangowa kanta. Hannu ta saka ta dauko baqar ledar dake ajjiye daga gefe tana jan tsaki,kunceta tayi saman madubi,wasu qullukan garurruka ne da dunqulallun wasu abubuwa guda hudu. Daya brown daya baqi daya fari tas dayan kuma kore. Tsaki ta sake ja "Fiye da rabin ma da akace nayi inserting nasu ashe nayi,banajin wadan nan ragowar zasu samar min da abinda nakeso" ta qarashe maganar tana maida ledar ta qulle. Gwara ta samo wani abun da zai cikashe mata gibin da zata samu. Saman hautsinannen gadonta ta miqa hannunta,ta cusa shi qasan pillow dinta ta ciro wayarta. Kai tsaye data dinta ta kunna,sannan ta hau watsapp dinta. Tarin saqwanni ne suka shiga shigowa,duk da jiyan raba dare tayi tana chart kafin ta rufe tabi saleem din bedroom dinsa. Fitsarin da ya cika mata mara ya sanyata ajjiye wayar a gefan gadonta,sannan ta miqe da sauri ta tura qofar toilet dinta ta shige. Saman tiles din toilet din ta tsugunna ta kwata fitsarin. Sai ta dinga bin fitsarin da kallo saboda wasu launika da ya fito dasu da wani birtsi birtsi. Tsaki ta saki tana jin wani sabon bacin ran "Kalli yadda damshina da aikin maganin ke bi ta rariya a banza,haba,dole a yiwa saleem uzuri,akwai abinda ke shan kansa" ta fada a zuciyarta. Ko digewa fitsarin bata jirayi ya gama yi ta miqa hannu ta tari ruwan famfon dake kwarara ta yafawa wajen,ta sake miqa hannu ta tara ta yafawa gurin ba tare da ta sanya hannu ta wanke ba,ta miqe tana qoqarin maida pant dinta da uban danshin dake maqale a sumar dake mararta damqam,wadda a qalla kusan watanni biyu kenan cikin ta uku ba tare da ta samu aski ba. Sai a sannan ta lura da pant dinta da ya canza launi saboda kalolin magungunan matsi da taketa inserting tun yammacin jiya. Tsaki taja,ta fasa sakawa,sai ta zareshi ta jefa cikin bathtub dinta wanda ke dauke da kalolin pants da Braziers dinta da bata samu wankewa ba,ta tsartar da yawun bakinta dalilin rashin brush tana sakayo qofar toilet din cikin hanzari saboda kiran da taji ya shigo wayarta tana gudun kada ya tsinke bata daga ba. LIKITAR AURE sunan da ya fito kenan baro baro,wani mahaukacin tsaki da yafi dukka na baya ta saki "Ku******mar uba,aikin banza" ta fadi a fili takaicinta yana kasheta,sai tayi rejecting kiran ta shiga watsapp abinta. Shamsiyya ta fara lalubawa cikin jerin chats din dake dashboard dinta "Yauwa" ta fada da sauri tana gyara zamanta saman gadon ganin ta sameta a online cikin sa'a. Sallama ta danna mata,yana shiga yayi ticking blue "Ina kika shiga likita tana ta kiranki?" Saqon shamsiyya ya shigo. Ji zainab tayi ba zata iya jurewa typing ba,sai ta fara yi mata voice note "Yo me zanyi mata?,bayan asara tana dab da fadamin?,nayi amfani da komai da tace amma babu abinda ya faru tsakanina da saleem,hasalima tunda ya dawo daga kasuwa ya shiga dakinsa ya ajjiye jakarsa ya dawo parlor ya hau wasa da 'yan biyu,haka kawai naga kamar ya shigo ne da wani irin fushi,ana kiran sallahr magariba kuma tunda ya fita sallah bai dawo ba sai bayan isha'i,da na kawo abinci ma baici ba ya shige wanka abinsa,da ya fito kuma yace bayajin dadin jikinsa ne gaba daya,na juya yaqi cin komai,da na gaji nima sai na qyaleshi don ba wannan ne yafi damuna ba,kinsan wani rainin wayo?,na tafi naje na kwantar dasu hassana kafin na dawo sai zuwa nayi na tarar yayi bacci?,ya duqunqune a blanket,juyin duniya ya tashi ina da buqata wallahi ko juyowa baiyi ba". Zaman jiran shamsiyya ta gama ji ta bata amsa sai taga yayi mata tsaho,don haka ta fice daga inbox dinta ta fara duba charts. Saqon wani group dinsu da take masifar so mai suna MATAN NI'IMA shi yafi kowanne shigowa, group din yana matuqar sakata nishadi don tana qaruwa dashi sosai ta fannin magungunan mata,musamamman na turawa,wanda ita kanta ta sissiya wasu tayi amfani dasu,hakanan a boye ta siyawa saleem ta sassaka masa abun sha ba tare da ya sani ba. Tayi hakanne saboda sanin da tayi masa,baya qaunar ire iren wadan nan magungunan sam,duk abinda za'a ce masa magani ne na irin wannan fannin to baya ciki,ita kuma yadda matan keta comment a kansa ya sakata sha'awar gwada amfani dashi. Saqonnin ta fara bi a hankali,tun tana jin hirar na gundurarta kamar ta fice har ta soma daukan hankalinta _Maman mahbuba ya daren?,ya kikaji aikin maganin?_ _a fito mata a bamu feedback mana_ _hmmma ai abun ba'a magana,wadda bata gwada ba gaskiya an sha da ita_ Ire iren maganganun da suka sanyata zaquwa kenan,ta soma bin saqonnin da sauri sauri har ta gano bakin zaren hirar. Kai tsaye ta yiwa matar data fahimci a gurinta akaci kasuwar maganin magana ta private,sai taga ma jiranta ta karanta saqon bata lokaci ne,don haka ta sauka ta kirata direct call. Tana dagawa taji ta ambaci sunanta,abinda ya dad'ad'awa zainab rai. Wato tayi shaharar da sunanta ya tambara a group din kenan har ake iya kama sunanta kai tsaye?. Sama sama suka gaisa,zainab ta nema qari bayani akan magananin. Bayanin da matar tayi mata yasa taji ta gamsu d'ari bisa d'ari "Nawa ne kudinsa?,idan na turo kuma zan samu a yau?" "Eh akwai available,zaki samu,dubu ashirin da biyar,to amma tunda kece ansan saba da juna,ki tura ashirin,naki ne da na megidan duka zaku sha,na tabbatar saikin kawo wata ma". Nauyi taji kudin sunyi mata,saboda sosai tayi barnar kudin wajen likitar aure. Tun daga fallen zanin daurawa na magani data siya a wajenta da tarkacen kayan matsi a qalla ta barnatar da kusan dubu dari da talatin,abinda ya rage