← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 40

Sashe 20

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yakeyi,na rantse miki da Allah yau inda ruqayya ce zatayi kwanan asibiti bazai iya tafiya ya barta ba" kai kawai hajiyayye dake cire hijabinta ta daga ta kalli Zainab. Duk da tasan wasu abubuwan amma sai tayi kaman bata sani ba ta hanyar tambayarta "Saboda me?" "Saboda wani irin mahaukacin kula da yakeyi da ita da wani kulawa da na tabbatar ba ta domin Allah bace" "Ke ya akayi kikasan bata Allah bace zainab?" Hajiyayye ta fada tana jawo kujera dab da gadon Zainab din saboda su biyu ne a dakin,donma daya patient din tayi bacci abinta tuntuni,kuma abun mamakin ita kadaice babu dan jinya. Sake jan kujerar tayi baya kadan saboda yanayin da jikin zainab din ke bayarwa taci gaba da kallonta daga nesa nesa "Yo hajiyayye aiba irin wannan soyayyar a yanzu a wajen mazan wannan zamanin,kana gyara ma ya ka cika dasu bare baka gyara,nifa kullum cikin fuskantar matsala nakeyi da saleem,kyara gwasalewa,komai nayi banyi dai dai ba,komai nayi baya nuna wani jib dadi ko kuma wai na burgeshi,ni kuma a iya sanina macen da bata gyara HQ dinta ita ke fuskantar wannan matsalar,macen dake gyara take kulawa baji ba gani ai tafi qarfin ayi mata irin wannan tijarar,to ita ba wani gyara da takeyi matar nan,idan kuwa ba asiri ba banga ta yadda zata mallaki saleem ba" "A tunaninki?" Hajiyayye data gama sauraron soki burutsun zainab ta fadi tana dubanta "Hakane mana" zainab ta amsa mata kai tsaye "Sam sam" ta sake maida mata tana zama sosai idanunta cikin nata "Mun sani mafi rinjayen abinda ake kira da aure wannan abunne,to amma shi kansa baya tasiri baya kuma qayatarwa gami da jan hankalin d'a namiji saikin mallaki wasu abubuwan,tsafta,ladabi biyayya iya magana tattalin miji da tarairaya duka ina kika barosu?,ina kika baro iya girki?,ado da gayu?" "Duk basukai wannan muhimmanci ba hajiyayye,indai sune ke riqe maka miji me yasa saleem ya auroni idan ka cire matsalar haihuwa?,ita kanta haihuwar ba damun wani namijin tayi ba indai zai samu wannan gurin da kyau" ta fada tana qoqarin maida kanta ta kwanta,don kwata kwata maganganun hajiyayye basu samu matsugunni a ranta ba. Ta dade da sanin Zainab da kafiya da kafirin taurin kai,musu kuwa ba abinda yafi mata shi sauqi,tunda har bata da intention na ta fahimcetan to ba fahimtarta zatayi ba,zata batawa kanta baki ne,don haka tace "Gaskiya ne,hakane,amma akwai gaskiya daya da zan gaya miki,don Allah ki dinga qoqarin amfani da turare,sannan kodon zirga zirgar da kake wuni kanayi wankanki ki maidashi sau biyu" "Ke hajiyayye kin ganni nan,saleem bai taba cewa wani abu ba,turare kuwa mu ko munsa ko bamu saka ba mun wanku fes daga gurin kakanninmu,jikinmu baya komai in gaya miki,ki qyaleni na huta" "Hakka" tace da ita kawai tana tura kujerarta baya,ta dauki wayarta ta soma chart abinda.(hajiyayyen bazawara ce, mijinta ne ya rasu ya barta bata taba haihuwa ba,shekarunta kuma duka duka basu wuce arba'in da biyu ba). Idanunta ta rufe saidai maimakon tayi nazarin maganganun hajiyayye a'ah,asarar da zata tafka ta maganinta take qiyastawa indai shegen likitan nan ya riqeta bai sallameta ba a gobe "Aikuwa koda tsiya koda tsiya tsiya dai an sallameni gobe" ta fada tana muskutawa hadi da gyara kwanciyarta. "Me kika ce?" Hajiyayye ta daga kanta tana tambayarta "Ba dake nake ba" ta amsa mata don bata taba zaton zancan zucin da takeyi ya fito fili ba. Itama bata sake tambayarta ba ta maida kanta ga abinda takeyi. ********Dogon tsaki taja tana gallawa wayar ta data dauki ruri a karo na babu adadi harara "Kinsan fa ni banason irin wannan abun,waye yake kiranki da baki daga ba bare ki kawo masa uzuri?" Umma dake zaune a gefanta tana cin tuwon dare ta fada "Isma'il ne umma" "To ki daga mana?" "Haba umma,dame zanji don Allah?,da takaicin shegen yaron nan da na aika ya siyomin indomie yaje ya zauna koda nacin kiran wayarsa?" Side hannunta data gama cin tuwon umma ta farayi tana cewa "Duk dai ke kika jawowa kanki,inda tuwonki kikaci da ba yanzu bakinki alaikum ba,ba wanda yaji bare ya gani" "Allah ya sawwaqe,tuwon masara aisaidai a bawa gawata" ta fada tana kyabe baki tare da gyara zamanta tana ci gaba da hada sabbin syrup da supplements din gyaran jiki dana qiba data siyo jiya. Gefe kuma ga mayukan saka hasken fata suma data yiwa roba guda. Dai dai nan yaron ya kwado sallama ya shigo hannunsa da baqar leda "Kaci uwarka surajo,inda kasan dadewa zakayi uban me yasa ka karbarmin aike?" "Banason lamarin zagin iyaye na gaya miki malama" umma ta fada tana kwada mata harara "Layine a wajne wallahi da qyar akazo kaina" "To kinji ma" umman ta fada ta yunqura tana miqewa da kwanonta ta nufi kitchen. Jakar umma ta jawo ta zuge,daga can umman ta jiyo qarar zuge jakar "A'ah fa,ni ba zaki talautani a daren nan ba,na baki kudin indomie me kuma kike nema?" "Pepsi zai siyomin don Allah,sai kuma ashirin din dana masa alqawari,zan biyaki bashi na ansa" ta fada tana ciro kudin da sauri ta miqawa surajo din tana masa inkiyar yayi sauri ya fita. *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 16 *_RUK'AYYAT GRAPHICS_* *_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_* *_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_* *_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_* LOGO INVITATION CARDS BANK STICKERS BUSINESS LOGO SAVE THE DATE P.O.S BANNERS BIRTHDAY CARD BOOK COVER DATA FLAYER BIRTHDAY VIDEOS VIDEO INVITATION AI PICTURES _KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_ *_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_* *RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku _KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_ https://wa.me/+2347084515410 _ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_ _____________________________ Da gudu surajo ya cilla ya fice daga gidan,saboda yasan indai umman ta fito ta karbi kudinta to ya shiga uku gurin wasila. Hakanan 'yar naira ashirin dinsa shima ta shiga rububi. Umma na daga kitchen tana mitar halin wasilan na zabe zaben abinci "To wai umma idan bakiyimin ba waye zaimin?,kuma ai ansan banason tuwon aka tashi akayi mana,kinga kuwa bazan kwana da yunwa ba". Suna tsaka da wannan taqaddamar Surajon ya dawo. Tasa hannu ta karba tana cewa "Surajo me abun arziqi da na tsiya,yanzu dai sai gaka sharp sharp,to ga kudinka" ta miqa masa ashrin din. Hannu yasa ya karba yana cewa "Ana sallama ma sake a waje" fuska tadan bata "Waye?" "Isma'il ne" ya bata amsa dai dai sanda umma ke fitowa daga kitchen "Bawan Allah dan albarka,je kace tana zuwa kaji" juyawa yayi ya fice abinsa,yayin da fuskar wasila ta canza ta jawo ledarta tana budewa. Kallonta umma tayi "Nayi tsammanin zakije ki fara saurararsa kada abar mutum haka a tsaye?" "Ni yunwa nakeji wallahi umma,sai naci abinci tukunna,idan bazai iya jira ba ya tafi" "A'ah,kedai kiyi da jiki ki gama" umman ta fada tana kade gefan tabarmar da suke kai din ta sanya hijabinta ta tayar da sallar isha'i. Da gayya ta dinga laqai laqai harta gama,siririn mayafi kawai ta yafa saman doguwar rigar jikinta tadan sake shafa turare tayi hanyar soron. Haushin isma'il takeji,wannan shige matan da yakeyi,sai taga kamar yana nesanta ta ne da irin mazan da take sa muradi,yaqi ya gane yaqiyin zuciya kuma ya barta. Kansa a qasa yana danne danne a wayarsa,jin takunta ya sanyashi daga kai daga abinda yakeyi yana dubanta,sai ya saki qaramin murmushi yana fadin "Barkanki da fitowa ranki ya dade" "Yauwa,barka" ta fadi kadaran kadaham. Ita kanta tasan isma'il bashi da wata matsala ko makusa,amma an riga an gaya mata ba shine alkhairi a tattare da ita ba,kuma itama ta gamsu da hakan,tunda baikai arziqin da takeson mijinta ace yana da shi ba,yadda take da tarin magauta din nan,tanason ta auri mijin da idan ta shiga gidansa za'a san yes!,ta auri me arziqi,mijin da first night dinta zai bata kyautar mota,mijin da zata dinga zuwa umra da aikin hajji har sai ta gaji,mijin da zai dinga sauya mata kalar motocin da zata ji dadin takota ta shigo unguwarsu tana fankama da hura hanci,ta bule maqiya da mahassada da qura,ana kiran hajiya wasila tana kyautar sabbin kudi,dukka tasan isma'il bazai iya affording wannan ba,duk kuwa da tasan ci sha sutura da wirin zama duk ba zata raza ba,don bai rasa komai din ba,hasalima Lagos yake zuwa yayi sari na shagonsa me yawa. Ya siya fili kuma gini yakeyi me kyau,amma yace mata idan bai samu kammalawa ba har lokacin aurensu zai kama musu haya kafin ya kammala daga bisani sai su tare. Itakam babban abun kunya ne a gareta ace wai yau ita wasila.......wasila guda tana a gidan haya,me yafi wannan abun kunya?,duk wadanda duka sanya ido suga ya zaka qare suyi maka dariya suyi shewa son ransu kenan,Allah sitru buqui inji kishiyar me doro. Shi ya karba daddumar da ta fito da ita ya shimfida sannan suka zauna akai. Kusan fiye da rabin hirar shi yakeyi,har zuwa wani lokaci da yaga ta fara hamma da lumshe idanu duk kuwa da cewa duka duka baifi minti arba'in da zuwa ba "Yadai?" Ya tambayeta cikin kulawa. Fuska ta yatsina ta danja tsaki "Bacci nakeji,kuma ma dai yunwa ma nakeji,haka kawai umma tayi mana tuwo yau" "Subhanallahi" ya fada cikin dan gajeran nazari. Bayan dan shuru da ya biyo baya na sakanni sai kuma yace "Ai bai kamata ki kwana da yunwa ba seela ta" ya fada yana fiddo wayarsa a aljihu. Bugu biyu aka daga suka gaisa "Ina layin nan dake kallon gurinku........eh takeaway nakeso a hadamin me kyau.......yauwa komai da komao,ya miqo layin sosai sai yazo gaban wani gida me farin fenti ina daga ciki...... alright na gode" daga haka ya cire wayar a kunnensa ya maida aljihunsa "Ai da ka barshi wallahi" Ta fada kawai don jin baki "A'ah,ba za'a yi haka ba ai,so kike nima na kasa bacci?" Murmushi ta saki tana jin dadi a ranta "Yauwa ni da albishir mafa nazo miki,ga yunwa kuma kina ji,anya albishir din nan zai fadu?" Wata zaquwa ce ta kamata, zuciyarta na hasaso mata waya zai sauya mata "Fadi kanka tsaye yallabai,ai dukka kunnuwana suna tare da kai" "To shikenan yallabiya" ya furta cikin dan
Chapter 20 · 0% Book details