Sashe 15
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
harara "A'ah sulaiman ba isma'il ba,kina da abun haushi wallahi.....wannan wani guy ne irin type dina wallahi" ajjiye carbin hannunta ruqayya tayi ta tallafe habarta "A'ah,amma yanzu kk ce baki samu wanda kikeso ba ko saboda jifanki akeyi" rigar atamfar ta zaro ta dawo gefan gadon ta zauna tana kallon ruqayya "Inason mutumin nan ruqayya,amma na masa maganar ya fito yakai sau goma har yanzu shuru,malamai biyu sun gayamin jifan da akeyimin ne yake hanashi turowa,shima yana shafarsa" kai tadan gyada "Kuma kin tabbatar yana sonki kema?" "Sosai,ke kinga hidimar da yakeyimin ne?,kuma inda baya sona ai da tuni ya tafi,wata nawa muna tare,munfi shekara fa". Shuru ta sakeyi tana nazari,duk da ita da wasilan tamkar ciki daya suka fito haka suka tashi,kuma ko yanzun dukansu suna iya yiwa juna katsalandan akan abinda ya shafi rayuwar daya,saidai zuciya da kuma shaidan batasan ta fiya challenging wasilan. "Au,bari na gayawa umma ta tura wani yaron ma ya siyo masa lemo" wasila ta fadi tana fita da sauri a dakin. Minti daya kacal ta soma jin muryar umman tana magana "Bazaiyiwu ba,tunda kinsan ko kin karba Bashir sai ya saka an maida masa,bayan uban fadan dazai hada ni dake yayi mana" "Don Allah umma ki manta da yaa Bashir,shi wallahi ya fiya tsanani,waini qaramar yarinya ce da zatayi abinda bai kamata ba?,nasan fa abinda nakeyi da hankalina,waya me tsada kamar wannan ina gani umma kice kada a kawo?, gaskiya kiyi haquri umma,yaa bashir dai tunda ba'a gidan nan yake ba sai naso ma zaisan wacce irin wayace a hannu na". "Nidai ba ruwana na gaya miki" "Haba umma,haba umma" wasila ta fadi tana buga qafarta,sannan kuma rai a bace ta dawo dakin. "Wasila" ruqayya ta kira sunanta "Inajinki" ta amsa mata tana zama gefan gadon "Abinda ya bashir fa yayi dai dai ne,sannan dadewa da saurayi da kuma yi miki hidima ba shine tabbacin ingancin halaye da dabu'unsa ba,hakanan ba shine tabbacin yana sonki ba,babu soyayyar data wuce mutum ya aiko gidanku ayi maganar aure tsakaninki da shi" "To amma meye hadin waccar matsalar da wannan,kawai sai ace kyautar wayar ma ba za'a karba ba,komai an maka izini kamar dan qaramin yaro?" "Kudin iphone 13ya isa fa ya kawo kudin aurenki harda sadaki fa wasila,mutuncinki suke kare miki" juyawa tayi kawai ta kwanta rub da ciki ba tare data sake cewa da ruqayya komai ba,sai qananun gunaguni data ci gaba da yi,kana ta jawo wayarta tahau yin waya. Tata wayarce itama tahau tsuwwa,koda ta duba sai taga saleem ne. A nutse ta daga tana daidaita muryarta tamkar budurwar da zatayi magana da saurayinta da suke sharafin ganiyar soyayya "Habibee,hala munyi dare ko?,ayi mana afuwa umma dince ban samu ba sai dana jirata" "Kada ki dami habibtee,nima ina komawa na fito,zan qaraso saimu dawo tare,da motarki kika fita?" "Eh da ita ne" "To sai na qaraso" "Allah ya kawomin kai lafiya" "Ameen habibtee" ya amsa mata. Ajiye wayar tayi tana fita gurin umma,ta sameta tsakiyar su iftee ta sakasu a gaba suna cin alkubus da miyar ganye,sunata zuba mata surutu tana biye musu. Sake gaisawa sukayi a nutse sannan suka shiga hirar duniya wadda kusan duka ta zumunci ne. Akwai zumunci sosai tsakanin mahaifiyar ruqayya da umman data kasance qanwa ga mahaifiyar ruqayya. Suna tsaka da hira kiran saleem din ya shigo wayarta, saita duba tana cewa da alhassan "Duba ko abbanku ne a waje,yace zai qaraso mu wuce gida tare" "Asshsha,kya barshi a waje,jeki shigo dashi mana"umman ta fadi,sai ruqayyan ta miqe ta fice. Tare suka shigo tana zolayarsa,yayi kyau cikin yadin voyel fari qal yana zuba qamshi "Kodai kodai anya kuwa?" Murmushi ne ma ya qwace mishi,ita ta tafi dashi saboda daurin data lanqwasa kanta,fararen idanunta kuma sun fito tarwai a hasken qwan lantarkin da ya haske gidan gaba daya amma ita tsokanarsa take qoqarin yi "Kodai me?" "Zance kaje ka biyo ta nan" ta fadi tana qaramar dariya me jan hankali saboda sautin da take bayarwa ma daban yake. Hakanan ita kanta ta saba,idan tana tare da saleem komai nata yakan canza,takan rikide daga ainihin ruqayyanta zuwa habibtee dinsa. Sosai umma ta tarbeshi,don kafin su iso ma ta masa shimfidar dadduma. Hira sukayi kadaran kadaham,don yafi sakewa da ita ma akan maama mahaifiyar ruqayya. Wasila ta saka ta zubo masa alkubus,amna kuma baici ba yace ya qoshi,don ba kasafai yakecin abinci a wani guri ba muddin girkin ruqayya ne. Ko kadan bayason yayi missing girkinta,gurin hajiya mahaifiyarsa kawai yake iya karbar abinci yaci indai tayi masa tayi ranar girkin ruqayyan. Koda zasu tafi umman ta juye masa abincin "Ku tafi dashi ruqaiya" umman ta fadi. A gurguje ruqayya ta leqa don yiwa wasila da bata sake ganin gilmawarta ba sallama,saidai bata cikin dakin,bata kawo komai ranta ba ta fita suka wuce.