← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 40

Sashe 29

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bacin rai,hakan ta fada qibar ta dan janye kadan. Cikin wannan lokacin yara suka kammala exams, za'a yi musu hutu,hakanan an gayyaci dukkan iyayen yara don su halarci makarantar za'a yi taron tafiya hutu da bada kyaututuka ga haziqan dalibai. Farko ruqayya cewa tayi ba zataje ba,tunda duka makarantar yaran nasu daya ne Zainab din ta wakilceta kawai. Saleem ne yace a'ah,dukkansu suje kawai,bataso zuwa din ba don cikin yazo mata da zaman daki zuwa falo,batason leqawa ko ina,amma hakanan dai tunda yace aje din ta kira wasila tace tazo suje tare tayi mata rakiya. Kowa a motarsa zashi,don haka koda ta tashi tafiya bata cewa Zainab din komai ba. Tunda ta lura ta dauki wata gagarumar gaba da ita tun daga ranar da tace zata bita suyi yaji tare,sai itama ta sake kama kanta fiye da baya,don a nata ganin meye nata a ciki?,fadanta dama tsakaninta da mijinta ne,abinda ya sanya harta sanya baki ma shine ganin za'a bar mata wahalar yara,wanda ba ita ta fara tarbiyyarsu ba,so batasan ta ina zata dauko gyara ba. *_ZAZZAFAN ALBISHIR GAREKU MASU KARATU_* *NACE BA* *ZAFAFA BIYAR FA!* *SABUWAR SHEKARA CE!!!*2024 *Abun ba'a magana* *_KUSAN WADANNE ZAFAFAN LABARAN SUKA DAUKO MUKU?_* AMEENATU mamuhghee KWANKWASON JIMINA Miss xoxo TSUTSAR NAMA Billynabdul GUDUN K'ADDARA Huguma *_kedai ki shirya kawai hajiyata,abun ba'a cewa komai_* *_akwai zazzafar tattaunawa da zazzafar muhawara_* *HUGUMA* *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 24 *_Asalamu alaikum warahmatullah,barkanmu da warhaka_* *_Har yanzu dai ina nan ina ci gaba da sauke muku kabakin kaya masu tsananin kyau quality da kuma saukin kudi kamar a kyauta a HUGUMA CLOSET_* *_SARI KIKEYI KI SIYAR KEMA?,KO NA SANYAWARKU NE A JIKI?_* *_TO TABBAS BA GROUP DIN DA YAFI DACEWA DAKE SAISHI *_ki siya kayanki cikin farashi me sauqi,kaya masu quality kuma unique one,suzo su sameki fiye da yadda kike zato hankalinki kwance cikin aminci_* *GANI ANCE YA KORI JI* Iftee na riqe hannun wasila suka fito daga sashen ruqayyan. Tayi kyau sosai cikin doguwar rigar wani material wadda take zuwa hade da mayafinta,yaron cikin jikinta ya qara mata kyan fuska da na fata gaba daya. Fes da ita qamshin sassanyan turarenta kawai takeyi. Hira Suke ita da wasilan,wasilan na qorafin kan case dinta da faisal "Nidai bansan lokacin da idanunki zasu bude ba wasila,bansan sanda zaki gane abinda ke gabanki ba,ai alamun qarfi yana ga me qiba,hakanan duk juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta,ya kamata ki bude idanunki da kyau wasila" baki tadan tabe,har yanzu tana jin ciwon abinda faisal yayi mata "Shi kuma isma'il gaba daya yama daina kirana" "To zaizauna ne kina wulaqantashi son ranki?, bazaiyiwu ba ai,Allah ya hada kowa da rabonsa,tunda dai ya baki dukkan dama" "A yadda ma naji wai yakai kudin aure" ta fada tana jin dacin abun har cikin ranta "Ato,kinga ya sawwaqa miki wahala ko?" Maimakon wasilan ta amsa sai sautin dariyarta da ya isa kunnen ruqayya dake qoqarin zura key ta bude motarta. Daga kai tayi tana duban wasilan "Ke kuma lafiyarki?,muna magana me ciwo da kuma muhimmanci kina kuma dariya?" "Qanwarki za'a tambaya lafiyarta daya?,don muhammadur rasulillahi da gaske haka zata je makarantar 'ya'yan nata?" Duk yadda ruqayya taso ta dauke kai kada ta kalli zainab amma saita kasa,yadda wasila ke sheqa dariya abinta ta tabbatar ba qaramin abu bane. "Subhanallahi" ta fadi tana dauke kanta da sauri kada zainab ta fahimci suna maganarta ne. Wata irin hautsinanniyar shiga tayi kamar wadda ke shirin fara aikatau din abincin biki. Sai data tausa kanta da kyau sannan ya hadiye dariyarta,ta jefi wasila da harara "Gulma ajali,to ina ruwanki?" "Ki barni Allah yau daya na bata shawara kada taje a haka ta zubdawa 'ya'yanta aji" caraf ruqayya ta kamo hannun wasila,domin kuwa tasan halinta sarai,'yar takife ce,tsaf zata iya tarar zainab din,tayi imani kuma abun bazai qare da kyau ba,wasilar 'yar rigima ce ta gaske,zainab kuma ba haquri ta tabbatar ba zata dagawa wasila qafa ba. "Ba ruwanki don Allah, shige mu tafi" ta fada tana turata gaba. Duk da haka bata fasa tiqa dariyarta ba har zuwa sanda zainab din tazo giftasu. Suna Hada ido da ruqayya ta saki wani mugun tsaki sannan ta barke da waqa tanayin gaba "Kanbalasti,don girman Allah ki barni na yagawa jakarnan dawa,wai ita a nan haka macace?" Wasila daketa dariyarta kamar ba gobe ta fada. "Nace miki dai ba ruwanki bakinta ne tayita yi" "Su kishi manya,ni da gwaigwai" wasilan ta sake fadi tana kallon qafafun zainab data rabasu tana niyyar shigewa mota "Nikam wannan matar ko primary ta gama kuwa?" "Bansani ba nidai" ruqayya ta fada tana tayar da motarta tare da qoqarin danne dariyar da wasila ke qoqarin sakata yi qarfi da yaji. Ta daidaita motar suna shirin fita dab da motar zainab din wasila ta sauke glass "Mata suna muka tara,a cikinmu wace zara tauraruwa acan a sama......" Daga haka ta fuske ta maida dubanta wani sashen na daban. Sarai zainab taji maganganun wasilan,kuma ta tabbatar da ita take,ba tun yau ba tasan halinta,wannan ya sanya sam basa shiri da ita,muddin tazo gidan ba kasafai ta fiya tafiya salamun qaulin wani abun bai hadasu ba. Mita ruqayya ta shiga yiwa wasila bayan sun fita a gidan "Ke kike jin tsoronta,ni so nayi ma ta kulani na wanke qazama,yo koni da nake ba wanda ya ajjiyeni tsigau nake ta yaya zan zauna a haka bare ina da miji?" "Amma kinfi kowa sanin halina,ta yaya zanji tsoronta?,tashin hankali ne kawai ni banaso,zaman lafiya kuma yafi komai dadi" "A wajen wanda yake sonshi ba" ba wani jin dadin jikinta sosai takeji ba,don haka taja bakinta ta kulle ta qyale wasila,saboda tasan ko meye zata fada ba lallai ta yarda ta dauka ba. Sanda suka isa makarantar harabar gidan ta fara cika da mutane. Tsaida motar ruqayya tayi tana cewa "Banajin qwarin jikina sosai,ba jimawa zamuyi ba zamu koma gida gaskiya" "Ba damuwa,nima din yau zanyi baqo" dan dubanta ruqayya tayi "Really?,Allah yasa shine mijin" dan tabe baki kadan wasila tayi "Toh.....gashinan dai,yaa bashir ne ya hadamu" ta fadi tana bude murfin motar. Da kallo ruqayya ta bita,itakam wani lokaci al'amarin wasila kamar wata me almutsutsai,duk wanda yazo yakai mijin aure a idon kowa amma banda a idanun wasilan,ko meye yake damunta oho?. Tunda yaran suka hangi ruqayyan suka fara murnar ganin ummansu,haneefa na zaune daga gefansu tana raba ido. Duk da ba wanu shekaru bane da ita ba can amma shigar zainab ta sanyaya mata jiki. Kowa cikin yaran yanata nuna ummansa da azamarsa da karsashinsa amma banda haneefa da ta sake noqewa,kwata kwata shigar ummantata batayi mata ba. Cikin lokaci qalilan aka fara gudanar da taro gadan Gadan,har zuwa sanda aka fara raba kyaututtuka. 'yan biyu makaranta wato alhassan da alhussain sun samu kyaututuka kala daban daban har kusan kashi hudu. Zainab na daga gefe amma tana bibiye da komai,kusan fiye da rabin hankalinta yana kan yadda komai yake gudana. Ta kasa kunne ta jirayi jin an kira koda Khalil da ta saka buri me yawa a kansa,har wani lokaci takan kirashi da doctor,amma har akayi aka gama shuru maqatau kakeji "Shegun yara,an koya musu shegen sanabe da iyayin masifa da iya mallaka" zainab dake zaune akan kujera ta fada tan binsu alhassan da harara. Da daya da daya yawancin yaran suke gabatar da abokansu ga iyayensu,tun zainab bata ankara ba har idanunta sukakai ga su haneefa. Zugar yuyar qawayenta ne ta jasu zuwa wajen ruqayya dake zaune tana magana da abokansu alhassan,duk da cewa kusan fiye da rabinsu ta sansu dama,don bata wasa da zabarwa 'ya'yanta abokai,hatta kuwa da iftee da take qanqanuwa a cikinsu (mu kula da kyau iyaye,mu kula,mu sanya idanu,tabbas abokai na daya daga cikin mutanen dake taka muhimmiyar rawa ga rayuwar yaranmu,kada kace ba komai don abokin yarona baya zuwa makaranta tunda yarona yana zuwa,kada kace ba wani abu bane don abokin yarona ya kwana ko ya yini da yunwa tunda dai nawa dan yaci abinci hakan bazaiyi affecting dinsa ba,kada kace ba komai don abokin yarona yana zagi ko gidansu ba tarbiyya ai basa haduwa ko yaushe bazaiyi affecting nasa ba,a'ah......sam wallahi,kiyi iya bakin qoqarinki tuquru,yadda kikasan danki bai rasa komai ba kuma yana kan turba ki tabbatar abokan 'ya'yanki ma haka,daga yaranki suka fara samawa rayuwarsu abokai to aikin tarbiyyar dake wuyanki ya linku, tarbiyyar ta zame miki double muddin kinason kiga daidai,kiyi naki kiyi na abokan yaranki,duk yaran da iyayensa zasuyi fushi donkin hukunta dansu ko kin masa gyara ko tsawatarwa ko tabbas ki nesanta yaranki da wannan yaron,Allah ya dafa mana yayi riqo da hannayenmu wajen basu kyakkyawar tarbiyya ameen summa ameen). Washe baki sosai haneefa keyi tana cewa "Ga mommy na nima,ku gaisheta" da murmushi ruqayya ke bin qawayen haneefan da kallo,saidai babu wanda yakai ga furta komai suka tsinci bankowar zainab tsakiyarsu. "Mommyn uwarki mommyn ubanki?,ina tasan ciwonki don******ubanki,annamimiya kema an koya miki annamimanci ne koko yaya aka soma?,ko sihirin ya fara biyomin ta kanku?" Zainab ke fada a tsawace tana kallon fuskar haneefa data ruqayya. Har wasila zatayi magana ruqayya ta damqi hannunta,ta jata suka miqe tsam tace dasu alhassan "Ku wuce muje hakanan,taro ya tashi alhamdulillah,'yan yara sai watarana,ku dage kuyi karatu ku yaqi jahilci kunji?,domin shi jahilci babban ciwo ne da yafi na hauka". Daga wannan bata qara ba tayi gaba bayan ta sanya su alhassan a gaba. Daga inda motarta take take tsaye tana qoqarin bude musu amma tana iya jiyo ashariyar da zainab din ta lailaya sannan ta fara tunkaro inda suke "Don annabi kada ki tashi motarman,ki bari na nunawa matarnan qaramar qwaruwa ce ita tunda ke ta shanyeki" "Ba zamu raba hauka a nan wajen ba,indai mukayi haka damu da ita din dukka daya muke kenan,ki barta idan ta haifu ta sameni cikin gida" daga haka ta tayar da motar tun zainab bata qaraso ba,wanda hakan ya sake qona ran zainab din taja burki a wajen tana huci,saidai kuma zuciyarta na gaya mata tsoro ruqayyan taji ta gudu "Aiko baki tsira ba,yau sai na fanshe haushinki billahillazi,sai nayi sanadiyyar wannan matsiyacin cikin da ake feleqe a kansa" tana gama fadin haka cikin zuciyarta ta durfafi motarta,haneefa dake binta a baya idonta da ruwan hawayen takaici saboda yadda taga qawayenta da wasu mutane da sukayi saura a wajen na kallonta tabi bayanta
Chapter 29 · 0% Book details