← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 40

Sashe 26

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cancanta ace kafi maqalewa,ni ya dace ace ina da ciki,amna saboda anqi Allah anqi ma'aiki sai gashi me ciwo daban me shan magani daban,Allah zai saka min" tana kaiwa qarshe tana sauka daga gadon. Wani dadi yaji yana ratsashi bayan tayi zuciya ta fita a dakin,ko banza zai samu yayi bacci cikin salama,don haka ya sauko a nutse ya murza key ya rufe dakin ya dawo gadonsa yayi kwanciyarsa,idanunsa a rufe amma cikin zuciyarsa yana wassafa irin kulawar da zai samu inda ace kwanan ruqayya ne. *******A harzuqe ta tashi washegari,don ko dakin bata leqa ba bare ta gaidashi. Abunda ya sake dugunzumata kayan da tayi order tace tanaso da sunan kayan sallan yara da nata sun iso,saidai kuma babu kudin da zata biya ta karba don duk sun tafi. Ita daya ta dinga qullawa tana kwancewa,tasan tabbas dole kafin saleem din ya wuce umra zai nema ganin kayan kowa,ita kuwa abun kunya ne ruqayya ta fiddo nasu ita ace ba abinda ta da nata sunbi ruwa. Sai wajejen sha biyun rana ta shiga a tsaitsaye ta gaidashi,ta samu ya fito a wanka ma yana shiryawa,gefe guda kwanukan abincin data aika haneefa takai masa ne na safe,da alama ko tabasu baiyi ba bare yaci abinda yake ciki. Zuwa azahar ya fito da shirin fita ya ajjiye mata kudin cefane ya wuce. Qaramin tsaki taja sanda yake ficewa,ta dauki kudin tana juyasu sannan ta ajjiye. Daidai sannan kira ya shigo wayarta. Kiran raliya ne,abinda ya sanyata nutsuwa kenan ta kuma amsa kiran ba bata lokaci. Qasa qasa takejin muryar raliyar,don sallamarta ma kaman a jigace take "Me ya sameki ne raliya?,bana jinki sosai" "Hala bakisha magungunan gurin basira ba?" Raliyan ta tambayeta tana numfarfashi "Niko nasha don jiya ma kwanan asibiti nayi maimakon kwanan turaka" "Madalla,mun samu qarin shaida,ashe matar nan bugaggiyar macuciya ce?,kin ganmu yanzu haka gidanta muka nufa, billahillazi saita fito mana da kudadenmu,ashe ita ke hada abinta a gida da duk abinda taga dama" "Kan uba,lallai biri yayi kama da mutum,jiya da qyar na qwaci kaina raliya....." "Ai ba'a bori da sanyin jiki,ki fito kawai mu hadu mu wuce gidanta,saita fito mana da kudinmu" "Yanzu kuwa,mu zata gwadawa shegantaka?" Ta fada tana katse wayar. Tsam ta miqe,ta danyi tunanin wacce qarya zata yiwa saleem ya aminta da fitarta?,don tasan ko giyar wake tasha bata isa ta cewa saleem wai kudi maganin kayan matanta zata amso ba. Lokaci ta duba,wata zuciyar ta gaya mata har taje ta dawo ba lallai saleem ya dawo ba,tunda idan ya fita bai dawowa sai magarib,ita kuwa me zata zauna ma tayi har magariba. Idan tayi wuta takai yamma,don ruwa ruwa zata zubawa basira rashin mutunci ta bata kudinta ta wuce,ta samu ta sissiya wasu kayan da zata nunawa saleem. "Umma ina zaki?" Haneefa da tayi tsaye a gabanta ta zuba mata ido tana kallonta sanda take gyara zaman hijabin wuyanta ta fada "Ku zauna keda.khalil,ko farfajiyar gidannan bance ku fita ba,yanzu zanje na dawo" tura baki gaba yarinyar ta fara yi tana qunquni har uwar ta fice daga gidan. Bata ma iya isa gidan raliya ba ta tsaya daga titi yayi mata waya,ba jimawa sai ga raliyan tana tafiya iska na kadata,ta zabge lokaci daya da alama taji jiki itama yadda ya kamata. Ba wanda ya iya magana a cikinsu don kowa idonsa ya gane masa,sai me napep kawai da raliya ta tsare musu, raliyan ce ta bashi kwatance sannan suka hau tana daukan wayarta tayi kira ta kara a kunne "Rabi gamu nan akan hanya.....uhummm" ta fada tana yanke kiran. *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 22 Kusan dukansu a galabaice suke daga ita har raliyan,saboda ba wanda baiji jiki a cikinsu,wannan ya sanya ko hirarma sama sama suke tabata,har zuwa sanda me napep din ya ajjiyesu a qofar gidan. Zainab ce me qwari qwari a jikinsu,ita ta zaro kudin ta miqa masa yayi gaba. A qofar gidan suka samu rabi ita da wata,su dinma kana kallonsu kasan anji jiki "Mu shiga kawai,mu shiga" Zainab da takeji kudinta kamar sunfi na kowa yawa ta fada,ko banza tana saka ran samun koda rabin kudinne idan ma duka basu samu ba. Tun daga soron gidan zakasan cewa tsafta ta tattara kayanta tayi gabas da gidan,tako ina sunyi hannun riga basa hada hanya ba. Hatta da Zainab yau d'ari d'ari takeyi kada ta taka kashin kajin dake karakaina abinsu cikin soron. Sanda suka amsa sallama kuwa basira data karkace a gefen kwatar data raba gidan biyu tana dahuwar kaza sam bata jiyosu ba. Hasalima waqe waqe take abinta cikin nishadi gami da jin dadi,gefe guda kuma tana jin zuciyarta tayi fess,saboda dawa tayi nama,domin kuwa dubu sha biyar ta karba a dahuwar kazar da duka dukanta naira dubu daya ce,sai tarin tarkacen magungunanta da suke amfani dashi ita da yara da ta yiwa gamje gamje ta zuba suka bada taste mara dadi,wanda shi makamin da zata bada hujjar cewa kazarta tasha hadin maganin mata me inganci. Cikin rawar jiki da washe baki ta miqe tana musu sannu da zuwa,cikin ranta tana jin yau farar rana ce a tare da ita,don dukkansu ba wanda bata samu kudi dashi ba "Sannunku da zuwa customer,eh lallai magunguna sunyi aiki, emergency ya kawo wuta yadda ya kamata,sabon hadi kuka zo ayi muku kenan......ahayyeeeeee cassss,saini basira me gyaran turaka......" "Ke da'alla malama ki yiwa mutane shuru ko na zazzabgeki da mari,macuciya azzaluma,ke kisa kikeyi ma inajin,kin bamu abinda kadan ya rage kwananmu ya qare" baya basira tayi baki galala tana qarewa zainab kallo "Ban fahimceki ba me kike nufi ne baiwar Allah?" "Koma meye ki shiga ciki ki lalubo mana kudadenmu da dukiyoyinmu da kika karba billahillazi ko na lahira ya fiki jin dadi" "Ahto,don ba zamu dauki asara goma da ashirin ba,ba wan ba qanin?" Raliya da qafarta ke rawa saboda rashin qarfin jiki ta fada rai a bace ta biyo bayan abinda zainab ta fada tana kada hannu. Guda basira ta saki tana yarfa hannu gefe guda "Ni zaki shigowa gida ki yiwa barazana?,to anqi a baki dukiyar taku....nace anqi a baku din duk abinda zakuyi kuyi" bacin rai da kuma ganin samu da rashi duka lokaci daya yasa idanun zainab suka rufe,ta tunzura da maganganun izgilanci da rainin wayon da basira ta fara kwararo musu,sai kawai ta kaiwa basira duka. Cikin tsananin sa'a kuwa ta sameta a fuska,ji kake qummmm...... Wani razanannen ihu basira ta saki tana dafe da fuskarta "Da kin dauka da wasa mukeyi miki 'yar rainin hankali,maza wuce ki dauko mana kudadenmu tun ban canza miki kamanni ba" "Ni kika yiwa wannan dukan?" "Nayi miki kuma na daki banza" "Wallahi wallahi sai kinsan ba kowa ake tabawa a kwana lafiya ba" basira ta fada tana juyawa afujajan zuwa dakinta "Duk abinda Zakiya kiyi,ina nan ina dakonki,karki fito saida kudina" zainab din ta fada tana huci gami da jan kujerar tsugunno da basira ta tashi a kai tana ci gaba da hayagaga da kumfar baki. Har kusan minti biyar shuru babu batun basira suna tsaye carko carko suna maida magana a tsakaninsu. Rabi ce ta dubesu cikin qosawa "Ko zuwa zamuyi mu tafi matar nan ba ita ba dalilinta fa,kada muje ta shirya mana sharri" "Wallahi indai ba batan dabo tayi tabar gidan nan ba inda zan motsa sai kudina sun fito,ta gama zamanta ta fito ta sallameni koda kuwa ku tafiya zakuyi,ni na fita bariki wallahi" zainab ta fada tana tafa cinya,tana jin kamar ta jawo basira ta bata kudadenta. Ko minti biyar bata rufa da rufe bakinta aka bubbuga qofar gidan da qarfi,ta bude baki zatayi magana cikin fusata sallamar wata mace me gurbatacciuar hausa ta sauka a kunnensu. Gajeriyar macace sanye da kaki na 'yan sanda(uniform),baqa me fadi da qiba,tana takowa tinqis tinqis "Hajaju........hajaju woooo" ta fada tana leqe leqe cikin gidan "Madam,ganinan,bazan iya fitowa ba,ko tashi bazan iya ba,haduwa sukayi suka yimin dukan tsiya,kin ganni a yashe a daki" maganar ta basira dake kwance a daki ta sanyasu kallon kallo a tsakaninsu,suka kasa cewa komai,saidai kowa zuciyarsa ta cika da tsoro "Aeaeaeae........sune wadacan mata na sakar geda ko?" "Sune madam,sune" basira ta fada tana nishin qarya "Angama" macen dan sandan ta fada tana fitowa. Da daya da daya ta qare musu kallo tana muzurai idanunta a kansu "Ku wuce mu tafi lafiya Allah ko na saka muku karfi" tace dasu "Ina zaki kaimu madam?,me kuka mukayi?" Zainab tayi qarfin halin tambaya "Tambaya na ma kikeyi?,to wa yabaki izinin shigowa gida ku dadaki matar gida kuma ku zauna a ciki ba izininta?" "Mu bamu daketa ba,kuma hakkinmu mukazo karba" zainab ta amsawa matar "Hey shut up stupid,naga alama kin fisu kwarin ido......hey. ... Samuel shigo ciki" matar ta fada cikin dan daga murya,nan take saiga matashin dan sandan ya sako kai,ya kuma taimaka mata suka tasa qeyarsu zainab sai police station. ****Tunda yace mata zaizo ta kasa zaune ta kasa.tsugunne,kusan ta manta rabon da faisal yace mata zaizo gidansu,ko yanzun ma tafi gasgata cewa aikin malam ne ya ciyoshi,don kuwa tayi dahuwar borkono tsidugu da rubutu,ta saka wuqa a garwashin wuta me dauke da sunansa,hakanan tasa anyi hatimi wanda aka buda aka rubuta sunansa a tsakiya dukka dai gaba daya domin azalzalo zuciyarsa,sai gashi cikin nasara da bakinsa ya furta zaizo din,bayan yazo din kuma yace akwai maganar da zasuyi wadda jikinta da zuciyarta sunfi gasgata mata cewa magana ce ta aure. Cikin wancan satin data shaidawa isma'il bata aurenshi yayi haquri yace ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa sai jikinta dukka yayi sanyi daga baya,har ta dinga ji cewa kamar tayi gwari,kamar bata kyauta ba,kamar tayi wata asara,amma yanzu faisal ya wanke mata zuciyarta fesss da zancan zuwansa. Kwalliya ta zauna ta dandasa 'yar ubansu,itama umma bata zauna ba,tana ta aike siyo drinks da sauransu. Ta tatse jakarta yau tas,don hatta kudin da yaa bashir ya bata dazun duka sun narke. Turaren da malam ya bata hadi da kwalli duka ta dauka tayi amfani dasu,da taga akwai sauran lokaci sai ta dauko carbinta ta zauna tana fuskantar gabas ta soma qarasawa don jiya bata samu kammalawa ba. Ba dadewa suraja ya shigo yace ana sallama da ita. Kafin umma ta amsa ita ta rigata,ta ajjiye carbinta ta dauki mayafinta da duka duka bai wuce ayi dankwali dashi ba ta yafa ta
Chapter 26 · 0% Book details