Sashe 21
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
salon tsokana,yaza hannu ya tura hularsa baya sannan yace "Zuwa yanzu wasila ina gani lokaci yayi da zamu maida alaqarmu ta ainihin gaske,tunda iya fahimtar juna mun yishi tsahon shekarun da muke tare,ina so ki shaidawa umma,ta yiwa su kawu magana in sha Allah qarshen watan nan zan aiko da kudin aurenmu hade da kudin sa rana,kuma banason duka a wuce wata hudu in sha Allah ba'a yi bikin ba" tunda ya fara zancan ta zuba masa ido gabanta yana faduwa. Bata shirya auren isma'il ba bata kuma son ta rasashi tun yanzu,tafison koda zai tafi sai idan FAISAL ko wani kaman faisal din ya kawo mata kudin aurenta tasan ta kama dahir "Kudin aure kuma isma'il ka gama ginin ne?" Ta fada tana dubansa. Dan nazarinta yayi kadan "A'ah,yanzu ba magana ake ta gama gini ba,gini na yana da buqatar a zuba masa kudade da yawa,inason nayi abu me kyau me tsari,wanda duk wanda ya kalla zai san na mori nemana" Fuska tadan bata tana girgiza kai "Gaskiya nidai nafi buqatar ka kammala tukunna" "Wasila" ya kira sunanta kai tsaye a maimakon seela da yakan kirata da shi,abinda yasa itama tayi hanzarin daga kai tana dubansa "Ni na shirya aure magana ta gaskiya,sanann hajiya kanta kullum maganarta kenan nayi aure taga 'ya'yana kafin ta Allah ta kasance a kanta tunda ban rasa komai ba,hankalina nima yanzu ya karkata ga hakan,in sha Allah bazan wuce wannan lokacin ba tare da nayi aure ba,idan kin shirya nima na shirya" "Idan ban shirya ba fa?" Ta fadi a qasan ranta tana dan satar kallonsa gabanta yana sake tsananta faduwa. Isma'il shine saurayi kusan na biyar da haka ta taba faruwa a tsakaninsu. Abdullahi,abubakar,nasir da sagir ga kuma isma'il. Dukkansu sun tafi ne saboda samun masu kudin da take muradi a irin wannan lokacin,kamar hadin baki dukkansu sai zance ya fara nisa a tsakaninsu sai masu kudin da take buri su bayyana saisu rushe gwamnatinsu,sai bayan ta sallamesu ne saboda ganin wadan nan sai suma daga baya su fece su barta ba wan ba qanin. Tayi qunan rai a sannan ba dan kadan ba,tun daga lokacin ta yanke hukuncin ta daina sallamar standby din har sai ta tabbatar ta kama wadancan din,yanxu gashi ana neman kwatawa (Yan mata!,yan mata!,wallahi wallahi wallahi kuyi hankali,ku yiwa kanku karatun ta nutsu,a irin wannan yanayin da ake ciki babban arziqi ne ma ki samu wanda zaice yau so nake muyi aure,da yawansu ba aure bane a ransu,saidai suzo su hole da ke kamar uwa su ta haifa musu ke,da yawan 'yammata ba mijin aure suka rasa ba, a'ah.......MIJIN BURI MIJIN MAFARKI suke jira ko ince suke nema,kibar wahalar da kanki kina namena lallai saikin auri me kudi,wallahi wannan din da kika raina qila shine me kudin da kike burin amma kika wulaqantashi,Allah ya rubuta sai ya aureki zakuyi arziqin tare amma kika bijire saboda idanunki sun kulle, ba'a ce ki auri namijin da bazai iya kula dake ba,namijin d a baikai ajinki ba,tunda ko a musulunci akwai KAFAA'A wato dacewa da juna,amma ta yaya a gidanku ana kulawa dake da kwatankwacin kudin da sukakai dubu dari kice ke wanda zai kula dake da million d'ari kike nema?wanne irin buri ne wannan?. A qa'ida dai ba'a son ana kula dake a dubu dari ki auri wanda saidai ya kula dake da dubu goma,ko ina anason aga mace gidan mijinta yafi gidansu ci gaba,AMMA FA ba tarin dukiya ba. Albishirinku!!!!,akwai tarin dimbin matan da zaki gani cikin leshi na kece alfarma,motar hawa ta isa da qasaita,gold kowanne corners na jikinta bodyguard da sauransu,amma billahillazi la'ilaha illa huwa da zata bude miki cikinta saikin kwana kina sallah kina godewa Allah da ya barki a inda kike,shi aure bawai mutum me DUKIYA kadai ake nema ba,Inaaaaaa........'yar uwa nemi MAI ZUCIYA wanda ko matar da take Jin mijinta wani ne idan kuka jera da ita zatasan lallai kinfi qarfin raini,nemi mijin dake KISHINKI wanda bai yarda matarsa ta rasa komai ba,wanda bai yarda a raina matarsa ba,wanda zai maidake SHALELE kifi qarfin rainin kowacce mace,mijin da zai kula da lafiyarki sai inda qarfinsa ya qare,wanda ya damu da damuwarki me tsare miki mutuncinki da dukkan qarfi da iyawarsa,wanda zai dauki iyayenki tamkar nasa ya basu girma na musamman.ba mai tarin dukiyar da baki da tabbas din zaki cita cikin kwanciyar hankali ma kuwa?. Da yawan 'yammata basu shiga gidan aure sunsan meye ainihin ma'anar miji ME DUKIYA ba dame ZUCIYA wannan shike rudarsu. Akwai wani jin dadin da duk girmansa kome miji yake baki koda kullum million hamsin ce wallahil azeem idan yana miki wasu halayen ba zaki taba jin dandanonsu ba,saikin gwammace naira dubu goma yake baki yake mua"amalantarki cikin nuna qauna tausayi da girmamawa,don Allah qannena yayyena da sa'annina YAMMATA ku farka,KU FARKA,KU DAINA KORE MAZAJEN AURENKU SABODA HANGE DA NEMAN WANDA YA FISHI,Allah ya shiga lamuran rayuwarmu gaba daya *HUGUMA* *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 17 Tana tsaka da wannan nazarin akayi sallama qofar soron,isma'il ya miqe a nutse ya karbo saqon ya dawo ya zauna yana ajjiyewa gabanta "Kada ki damu,amma kije kiyi nazari,saidai am sorry to say....koda baki shirya aure ba in sha Allah zanyi aure a wannan lokacin,don haka kiyi tunani a hankali kina da sati daya cif,duk abinda kikaji zuciyarki bata kwanta da shi ba kada ki yanke shi,ki zabi abinda kikaji kinfi aminta dashi,zaman aure zamuyi wanda muke saka ran mutu ka raba,bawai aje a dawo ba" da wadan nan maganganun yayi mata sallama ta dauki ledar takeaway dinta ta wuce gida. Da farko jikinta yayi sanyi sosai,har ma ta dinga juya lamarin,wata salihar zuciya daga qirjinta tana gaya mata "Me zaki jira?,kin cika shekara talatin fa kenan wasila,ki yarda da isma'il kiyi aurenki ki huta,tunda bazai barki da yunwa ko a wulaqance ba" zuciyar dake da gamayya da shedan na tuna mata "Shi kuma faisal ya zakiyi dashi?,idan kika amincewa isma'il shi kuma faisal yana da niyyar aikowa kinga kin yiwa kanki asara,yanasonki Faisal yanason kuyi aure,akwai jifan da ake miki ne ansan da arziqi a jikinsa ba'a so ki shiga gidan hutu shi yasa,amma da tuni kin jima da zama matarsa" kai ta jinjina tafi yarda da shawara ta biyu. Su masu jifan nata qila an duba musu sunga wahala zatasha a gidan isma'il shi yasa basu maida hankali su rabasu ba,sun hango arziqi jikin faisal wannan dalilinne yasa sukafi maida hankali a kansa. "Bari kiga" ta fada ita kadai tana janyo wayarta,wata number dake dauke da sunan MALAM ta lalubo ta dannan masa kira. Sai data kusa katsewa ya daga,suka gaisa da kakkaurar muryarsa sannan ta fara masa bayani "Isma'il ya matsa malam,yanzu haka zancen turowa yakeyi,ni kuma tun kafin ma ka shaidamin babu alkhairi tsakanina da shi nafison faisal gaskiya,don Allah malam a taimaka asa faisal ya turo ko yayi maganar kafin isma'il ya dawo" kai ya jinjina,yanzun haka a buqace yake da kudi "To ai shi kansa faisal din ba maganar aure a ransa kwata kwata,saidai zamu bullo masa ta bayan gida,bazai wuce wata guda ba tare da ya aiko din ba" "To na gode sosai malam Allah ya saka maka da alkhairi" "Ameen........yanzuuuu ......akwai turare da zamu siya,daga Syria ake kawo wannan turaren,sai wasu duwatsu daga misra a cikin ruwa ake samo ire irensu" "Kamar nawa kenan ane buqata malam?" Dan shuru yayi sannan yace "To,ai wasila ke abar tausayi ce,dole me imani ya tausaya miki saboda irin jifa dake jikinki Allah yayi yawa dashi,ki bayar da dubu ashirin,abinda bai cika ba na cika miki cikin aljihu na" Taji dadi sosai,godiya ta dinga yi masa kamar ta durqusa,sukayi sallama ta kashe wayar. Ranta fes ta soma cin takeaway dinta,a yanzu tunaninta inda zata hada kudinne kawai,don ba komai takeson gayawa umma ba,wani abun sai ta doje akai,tafison kome zatayi tayi abinta kai tsaye ba'a kawo mata cikas ba. Wayarta ta jawo sai tayi tunanin tayi kiran faisal(sau tari dama wasu 'yammatan suna qarewa ne da kiransu,kafin ya kirasu sau daya sun kira biyar). Duka yau basuyi waya da shi ba,amma takan bashi uzurin cewa harkokinsa ne sukayi masa yawa. Har ta katse bai daga ba,sai data qara kira bugu biyu ya dauka. Ranta fes ta shagwabe masa,shima ya biye mata suka bata kusan awa biyu suna waya,don leqowar umma biyu amma bata gama wayar ba. Suna tsaka da wayar dai dai lokacin da tasan yafison hira da ita ta katse wayar,sai bayan minti kusan biyu ta kunna ta kirashi "Nayita trying kuma naji a kashe" "Uhmmm wallahi,qawata ce ta shigo,bikinta ya kusa,ta kawomin anko amma nikam gaskiya na gaji da yin ankonnan,nima burina yanzu ace yau nice na fitar da nawa ankon kamar kowa?" "Nawa ne kudin ankon?" Ya fada yana share maganarta ta biyu "Dawainiya baby?" "No,kada ki damu abinda kakeso kake wahaltawa ai ko" "Gaskiya ne" ta fada da wata siriryar shu'umar muryarta cikin son sake shigar da kanta zuciyarsa "Lace ne 20k,sai atamfa 10k" "Alright,to ba damuwa,zan saka miki 40k harda kudin dinki" "Wow.....Allah ya biya, godiya nake" a cikin ranta tana jin ta samu kudin da zata biya malam harda riba. Wannan abun da ya faru a ranta sai ta sake jin me zatayi da isma'il?,mutumin da qarshen kyautar bajintar da zaiyi mata itace 10k,itama sai bisa abu me amfani tare kuma da qwaqwqwaran dalili. Tun a daren ta yankewa kanta shawarar sallamar isma'il,indai aikin malam yayi kyau Faisal yana magana zatace a saka wata biyu ma,tasan daga umma har yayunta duk a shirye suke mijin dama kawai ake jira. ********Tun da tayi sallar asuba bata koma ba ta wuce kitchen don hada abincin yara da nasu da wanda za'a kaiwa zainab asibiti. Shima saleem din da ya dawo daga masallaci zama yayi saman abun sallah yayi lazumi da karatu kamar yadda ya saba,bayan ya kammala bacci yadan daukeshi. Koda zai farka ta kusa gama sallamarsu,don uniform kawai suke sakawa,ya shiga dakin ya iskesu kowa yana saka uniform dinsa. Alhassan ya gama iftee yake sakawa socks. Su alhassan suka fara gaidashi,ganin haka kuma sun hada ido da haneefa sai itama ta matso tana gaidashi. Gefe ya koma yana karantar kowa. Tare ya canza musu uniform da komai na makaranta,amma idan kaga nasu haneefan zakayi tunanin sai da suka shekara biyu sannan aka dinka nasu alhassan,a