Sashe 37
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****Qarfe takwas na daren jajibirin sallah jirginsu saleem ya sauka. Dai dai lokacin da ruqayya ke kai kawo tsakanin falo da dakunan baccinsu don ganin ta wadata gurin da turaren wuta. Idan ka kalleta saita burgeka,saboda tayi kyau cikin dinkin wata lallausar atamfa da aka zuba mata doguwar riga. Daurin kanta ya zauna das,lallen dake hannu da qafafunta sun yiwa hannuwanta da suka qara taushi da haske kyau saboda cikin dake jikinta wanda ya fara turowa gaba. Duka yaran suna wajen wasila a daki anata faman fidda kayan da za'a saka a gobe idi. Yaran shadda tayi musu fara qal harda babbar riga iri daya da saleem data sanya aka zuba masa shima aiki a babbar rigar zatayi masa ba zata da ita a matsayin gift dinta na dawowarsa. Suna jin qarar tsauwar motar suka diba da gudu kowa na rige rigen isa farfajiyar gidan,dama kuma kunnuwansu dama suna farfajiyar gidan tunda sukaji an tafi dauko baban nasu. Garin wannan saurin suka yarda iftee,ta tsala kuka kuwa abinda ya dakatar dasu ya kuma ja hankalin ruqayya ta iso wajen. Harara daya tayi musu kaman yadda ta saba kowannensu ya shiga taitayinsa "Ku koma ku zauna" ta fada a dake,tilas kowa ya koma saman kujera ya zauna idanunsa a bakin qofa suna daukin ganin abban nasu. Godiya yayi ga Allah sanda ya shaqi iskar gidan,saidai kuma ya cika da mamakin abinda ya hana yaran fitowa musamman su iftee da ba kasafai koda yana gari suke missing zuwa tarbarsa ba. Kayansa ya bawa yahaya qaninsa yace ya wuce dasu sashen ruqayya shi kuma ya saka kai sashen zainab tunda yasan a sashen ruqayya zai sauka,abinda ke dada faranta ransa kenan tun a jidda kafin su taso,yasan zai sauke dukka wata gajiya tasa,zai kuma huta da kyau qwarai fiye da yadda yakeso. Yana sallama Khalil da haneefa suka yo kansa da gudu ya hadasu ya rungume yana amsa oyoyo dinsu. A sanyaye zainab dake zaune dafaan a wajen saboda jinin da ya fara bata zaninta bata samu ta tashi ba saboda wayar da sukeyi da raliya akan maganin da za'a amso mata na tsaida jinin data laqabawa suna jinin jifa,ta sauke wayar gabanta yana faduwa,saboda duka a lissafinta sai washegarin sallah zai dawo,kafin sannan suka ta samu ta saita komai,don taci alwashin ko na minti daya ba zata barwa ruqayya shi ba wai don tana cikin jini,sam ba zata bari ba,idan ma tayi ne don ta shawo kanta ita daya,kuma idan kwana biyun nan taci bulus,wani girkin da zata karba zata fara shine ta kuma qareshi cikin ciwo da tashin hankali hadi da jinin bari in sha Allahu,don ta qwaqule duk abinda yayi mata saura ta bayar ayi mata aiki akan ruqayyan. "Lafiya kike?ko azuminne?" Ya tambayeta yana kallonta saboda yadda ta koma wata iri gaba daya. Yaqe tadan sake masa kadan tanason kauda hankalinsa daga kanta "Azuminne na bana ya bada wahala" "To ya za'a yi?,ita dama aljanna ai ba'a samunta da sauqi kana daga kwance" ya fada yana zama saman kujerar yana mamakin yadda yaga qazantar sashen tadan ragu, cikin ransa yana fatan koyi takeyi da ruqayya tana rage wasu abubuwan. Ya danyi mintuna dasu yana basu alawoyin daya riqo kafin ya miqe "Inajin basusan na shigo ba,bari na qarasa ciki na huta" kai ta kawar tana jin zafi har cikin ranta yadda ya dawo dinnan a wajenta ya kamata ace ya huce dukka gajiyarsa,idan da hali ma kada ya tuna da wata ruqayya. Har yaran sun bishi ta kirasu,ta danqara musu ashar tace su zauna a nan. Hakanan suka dawo suka zauna gwiwa a salube,shikam baima sani ba tunda already ya fita. Haneefa ce data gaji da mutsu mutsu tace "Wannan zama kaman a birsin" tayi maganar kuwa akan gaba,don tana sauke maganar ta ta kai mata kyakkyawan duka a baki harda fuska,ta tsanyara ihu kuwa yarinyar tana dafe da fuskar "Don ****** ni zan dinga fada kinamin musu?,to zakisha wahala don wallahi mugun duka zan dinga miki daga yanzu" miqewa tayi tana kururuwa hadi da banka kuka har ta shige dakinsu. Kallon takaici zainab ta bita dashi har sai data shige dakin,taja qwafa tana maida hankalinta kan waya. Ci gaba da satar kallonta khalil yayi,don shima sashen nasu sam baya masa dadi,kamar gobe ba sallah ba,amma daxun da ya shiga wajensu alhassan sai yaji lallai da gaske gobe sallah. Gajiya yayi da zama ya miqe shima yabi bayan haneefa yana cewa "Ni wallahi dama momynsu alhassan ce ta haifeni,mu ko kayan sallar namu ma tsofaffi ne inajin" ya fada yana fadawa dakin da sauri don kada ta samu nasarar dukansa. Baki bude tabi qofar da kallo,anya ruqayyan bata fara taba mata yara ba?,anya sharrin nata bai gangaro mata kayan yaranta ba?,koma meye anzo qarshen maganar ai ba zata qyale ba sam. Kallo daya ya yiwa ruqayyan wata qaqqarfar ajiyar zuciya yaji ta subuce masa,tayi masa kyau iya kyau,gold Julius Holland din jikinta kamar saboda ita akayi wannan design din,yaran na lullube da shi amma hankalinsa yana kanta. Koda suka kebe bata gajiyar jikinsa yake ba,so yake kawai ya samu kaiwa ga kyakkyawan jikin da ya samu kyakkyawar kulawa da gayu me cike da nutsuwa da kuma cikakkiyar tsafta. Duk da gajiyar da ya sauke mata amma hakan bai hanata qoqarin ganin komai na abincin idin gobe ya kammala ba,daga qarshe tun farko farkon dare ya tsareta a daki yace tazo ta tayashi baccin gajiya,tana cikin jikinsa yana zuqar daddadan qamshinta har bacci yayi awon gaba dashi,wannan damar ta samu ta zare jikinta ta rufeshi da kyau ta fita suka qarasa komai ita da wasila sauran suka barwa washegari. *_WASHEGARI_* Sunyi fes abinsu shida alhassan da alhussain harda iftee da itama akayi dinkin shaddar da ita. Idan ka ganshi zaka dauka sabon angone,duk da a wajensa ya furta mata haka yake jinsa kamar sabon angon,duk sanda ya kalli kayan jikinsa tun daga sanda ya sanyasu kawo yanzu tun daga harshe har zuciya bai daina saka mata albarka ba. Yasan nawa ne price na shaddar data siya masa har yadi kusan goma,ya kuma san tsadar aikin data bayar akayi masa don kawai ta faranta masa. Duka kan iyalinsa ya hada suka wuce sallar idin saboda falalar dake cikinta,harda ruqayya wdda dama bata fashi duk shekara,indai bataje ba saidai idan bata da lafiya. Kusan sau uku yana aike kan zainab ta fito amma tace bata zuwa,tuni ta hangosu ta labule,kuma shigarsu kadai ta cusa mata tarin takaici da baqinciki. Shin idan tace zataje dinma me zata sanya ita?. Har suka fice idanunta suna kan haneefa da khalil wanda shigarsu ta banbanta data yaran,ta lura da yadda saleem din ya tsaya yana kallonsu hadi da jefa musu tambaya,yayi kaman zai shigo sai kuma taga ya fasa,ta sauke ajiyar zuciya,don ta tabbatar zaibi ba'asin kayan jikinsu ne. Sanda suka fice gidan sai ya zamana saura ita kadai,yau sallah don haka tayi niyyar itama tayi kwalliyar kece raini,saboda gobe tun da safe iwar haka zata matsa kambunta ta karbi miji. A duk sanda ta tuna haka ta Kuma tuna ta shiryawa hakan don wajen da ake abun dominshi nata a matse yake gam sai taji farinciki ya kamata,saidai kuma yadda jinin daketa zuba yaqi daga qafa abun yake sake daure mata kai,amma tana d hope don raliya ta gaya mata yau din bayan idi zata aiko mata da rubuta da.magunguna,kuma an bata tabbacin muddin dai asiri ne akayi mata awa hudu kacal zataga ya dauke. A gurguje tadan gyara falonta da bedroom dinta don tanason kafin su shigo tayi adon da zai cusawa ruqayya haushi don basu da nisa da masallacin idin. Hankali kwance ta soma cire kayanta don yin wanka a gurguje duk da tsummokaran jinin data jiqa wanda bata samu tsaiwa ta wankesu ba. Qunzugun ta zaro wanda ya jiqe sosai da jini,zarowar tasa yayi dai dai da fitar wani mummunan wari da ya sanyata kauda kai. *_ZAFAFAN DAI_* *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_* *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR ... ZAFAFA BIYAR NAKU NE *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 30 *_RUK'AYYAT GRAPHICS_* *_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_* *_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_* *_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_* LOGO INVITATION CARDS BANK STICKERS BUSINESS LOGO SAVE THE DATE P.O.S BANNERS BIRTHDAY CARD BOOK COVER DATA FLAYER BIRTHDAY VIDEOS VIDEO INVITATION AI PICTURES _KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_ *_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_* *RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku _KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_ https://wa.me/+2347084515410 _ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_ Daga ita har saleem babu wanda yake da tabbacin meye ya sameta,illa dai ta taimaka masa ya canza mata zani da riga,sannan yasa qarfi ya ciccibeta yana me dauke numfashinsa saboda abinda yakeji ya isa mota da ita. Zataso taje ta canza kaya ta kuma jefa wani abun a bakinta saboda azabar yadda zuciyarta take tashi,to amma yanayin da Zainab din ke ciki bazai bata dana ba,don haka tana a tsaye a nan tasa alhassan ya amso mata slippers da hijabi ta zura tabi saleem motar. Har suka isa asibitin Zainab matagugu take na matsanancin ciwon mara,dukkansu sannu suke binta da shi,saboda sunyi tambayar duniya bata cewa da kowa komai ba,dama ita ruqayya bata zurfafa a tambayar ba gudun jin abinda zai tayar mata da hankali ko maganar da zata bata mata rai. Duk da cewa ranar sallah ne amma asibitin a cike yake,akwai tarin masu ziyara