Sashe 27
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
fito kai tsaye ta wuce umman tana cewa "Bari na shigo da shi" Wani sanyi ne ya sauka a ranta sanda ta ganshi a tsaye jikin motarsa yana danne danne, exactly irin mijin da takeso. Kallonta yayi yadan saki murmushi ta maida masa "Bismillah,ka qaraso" ta fada tana juyawa ciki ya bita a baya yana qare mata kallo,don sosai straight gown din jikinta ta fitar da shape din mazaunanta,uwa uba kuma a yanzun da tasha supplement na qiba ta sake cika,kai ba zakace itace wasila 'yar ficika da ake tsokana ba,don har nankarwa yanzu gareta(stretch marks). Idanu ta juya masa a shagwabe sannan ta miqe tana fadin "Ina zuwa" sai tayi cikin gida yayin da shi kuma ya bita da kallo. Bayason su rabu amma kuma bai shirya aurenta ba kwata kwata,yanason macen da tafi wanann quality,duk wasu alamu da zasu nuna budewar idanun mace akwaisu a tattare da ita,duk da a iya saninsa bata taba zina ba,amma wasu abubuwan nata suna nuni ne da qarancin tarbiyya. Bata zauna ba sai data jere komai,komai tanayi ne cikin gwalangwaso iyayi da sanabe shi kuwa yana biye mata. Hira suka shiga yi kadan kadan,komai a shagwabe take masa hadi da kashe ido da karyar da murya kamar ba zatayi magana ba,abinda yasa ya dinga jin feelings a kanta kenan. Sama sama yaci abincin,duk da baici da yawa ba amma hakan ya mata dadi,tasan indai ya shiga cikinsa magana ta qare,sai daya nutsa yana goge hannunsa da tissue sannan ya dubeta "Waseela,inaso muyi magana ta fahimtar juna ni dake" "Tun dazu nake jira naji maganar ai" ta fada tana sakin murmushi gami da gyara zamanta "Kome zan fada miki ki dauka muqaddarine daga Allah,kuma shine qaddararmu da ni dake,amma kuma abinda zan fada din bawai yana nufin yankewar mu'amala tsakanina dake ba....." Maganarsa ta qarshe ta sanyaya faduwar gaba,amma ta dake taci gaba da sauraronsa. "Wasila aurenmu ni dake bazaiyiwu ba,saboda yanxu haka kakata ta dage ta tada rigima harda kwanciya ciwo wai sai na auri naana 'yar qanin mahaifi na" wani mummunan faduwa gabanta yayi,qafafunta sukayi sanyi ta kasa cewa komai saici gaba da tayi da kallonsa "Kiyi haquri don girman Allah,naso qwarai ni dake mu kasance miji da mata don nayi miki irin gatan da ban taba yiwa kowacce mace...... Amma yanzu ma bata baci ba,ni dake inaso muci gaba da mu'amala,ko meye kikeso zan kashe miki zan kuma baki". Hawayen da batasan yadda suka samu bane suka balle mata,ta girgiza kai cikin alhini tana dubansa "Amma me yasa duk lokacin nan baka gayamin ba?,ka barni inata bulayi da zaman jiranka?" "Banason ranki ya baci ne,kuma da farko na dauka zanshawo kanta ashe abun yafi qarfina,kiyi haquri don Allah karkiga laifina" kasa ci gaba da zama tayi,hankalinta tashe kawai ta miqe tayi cikin gida,tana iya jiyoshi yana kiranta amma bata ko waiwayeshi ba,kiran da hatta umma ta jishi,don tana shiga dakin tana binta a baya itama tana tambayarta ba'asi,saidai kukan da takeyi ya sanya ta gaza bata amsa. **Da sallama ya shiga sashen bayan barowarsa sashen ruqayya kaman yadda ya saba. Adan zabure Khalil da haneefa suka amsa sallamar tasa. Idanunsa ya sauke a kansu sanda suketa qoqarin daga tv plasma din data fado tayi zaman dabaro a qasan tiles. Ko da bai tambaya ba yasan abinda suka saba ne suka aikata,wato rikito da Tv din wajen fadace fadacensu da basa qarewa,su biyu kacal amma zaka tsammaci sunyi su goma a sashen "Waye yayi wannan aikin?" Ya jefa musu tambayar yana tsaresu da ido "Wallahi shine daddy.......qarya takeyi daddy itace ni ba ruwana,turani tayi kai" dukka sai suka kama masa rantse rantse. Ransa yayi qololuwar baci,ya rasa wanne hukunci zaiyi musu?,yo su idan suna da laifi ma ai kaso mafi yawa laifin na uwarsu ne. Matsawa yayi gaba yasa hannu ua daga tv din,ransa ya sake baci da ganin yadda tayi kwatsa kwatsa "Ina mamar taku take?" Ya tambayesu qasan ransa yana mamakin ya za'a yi abu me girma irin haka ya fado ya fashe amma baka ji ba ballantana ka fito? "Ta fita tun da rana" Khalil ya fada kansa tsaye. Tsaiwa yayi cak yana dubansa "Ta fita kuma?,ina taje?" Ya tambayi yaran "Bamu sani ba,mudau tace mana mu zauna a nan yanzu zataje ta dawo". Wani mugu mugun bacin rai ne ya sauko masa,a duniya cikin manya manyan abinda ya tsana a wajen matarsa satar fita, saboda shike haifar da wasu matsalolin da mai yiwuwa ba zasu taba gyaruwa ba. TV din ya maida duk da shi kansa yasan ta tashi a aiki,bata barnar da sukayi bane bama yanxu a gabansa,inda zainab ta sanya qafa ta fita bada izininsa ba tunda rana gashi ana shirye shiryen kiran sallar magariba. Cikin bacin ran yayi alwala ya wuce sallar magariba yana sanya ran kafin ya dawo ta dawo,saidai ko sanda ya dawo din ba ita ba dalilinta,dole ya tasa qeyar yaran suka wuce sassan ruqayya,don kuwa har sun fara jin yunwa,sunce rabonsu da abinci tun da rana,abind aya sake dugunzumashi kenan. Mutum ne shi da yaqi jinin yunwa ko kadan,wannan ya sanya baya bari a hora kowa da ita,koda baisan mutum ba bare cikin gidansa kuma 'ya'yansa. Tana zaune tana lazumi,alhassan da alhussain harma da iftee na zaune suna cin indomie da sukace sunan sha'awa ta kunna musu qaramin electric da ta ajjiye dama don saboda su,don wani lokacin qananun dafe dafe sukan iyayi,yaran badai qoqari ba,dafa taliya haka,shinkafa fara,ruwan zafi ruwan tea,tun uban yana fada da qorafi har ya barsu. *_KURMAN BA I_* *HUGUMA* PAGE 23 https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,akwai bonanza time to time da nakeyi,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*