← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 40

Sashe 18

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

muke jira" Da ya daga kai ya kalleta murmushi ne saman fuskarta kaman ba itace ta fita da fushi ba. Daya daga cikin abinda yake burgeshi da ita kenan,kuma guda cikin failure na zainab. Ita muddin ya bata mata rai sai ta bata masa,muddin tayi fushi ko ranta ya baci saita nuna ta kuma furta maka "Ko sai nazo na qarasa shiryaka ranka ya dade?" Ta fada tana rungume hannunta a qirji idanunta a kansa "Me yasa na damu na kasa juriya da qaddara,na shiga neman aure ido rufe?,don kawai ruqayya bata haihu ba?,yanzu ita ke da twins har da tsarabar diya mace guda,lallai rashin haquri da juriya na gaggauto mana da wasu abubuwa da lokacin riskarsu zuwa garemu.ma baiyi ba" yana gama wannan tunanin tana isowa,kaman jiranta yakeyi yasa hannu ya fusgota zuwa jikinsa,wanann sassanyan qamshin nata yayi ma hancinsa kyakkyawan maraba "Kiyi haquri da bata miki rai da nayi" "Nasan bakayi don kana sani ba,kayine saboda relief kakeson samu a sannan daga abinda kakeji,kayi haquri nima, wani yanayi ne da bana iya controlling kaina" "Laifi nane,amma bazan sake ba in sha Allah,zan fuskanci consequences din ni kadai" "Ya wuce fa,tashi ka shirya,yara har sunci nasu sun wuce". Ita ta taimaka masa ya shirya din,duk bayan sakanni sai ya jawota ya shaqi qamshinta. Har fargaba yakeyi daren qarshe a ranakun girkinta su fita,don gobe warhaka yasan makomarsa. K'arin abun mamakin koda da kudinsa ya siya turaren yace a saka masa iya dakinsa idan ma ita bata da buqata to fa bazai samu hakan ba,ya rasa dalili kamar me aljannun da suke gaba da turare. Da suka zauna alhassan ta aika kiran Zainab din "Jeka kira ummanku,kace tazo muyi dinner" amsa mata yaron yayi ya juya ya fice,ita kuma ta maida hankali wajen fara serving saleem. Tana zuba masan suna hira qasa qasa,yana bin hannuwanta dake jujjuyawa wajen zuba masa abincin da kallo saboda jan lallen da tasha tun shekaran jiya,an mata ratsin baqi a farcenta. Sau da yawa akan ruqayya ne baya yarda da cewar lalle baya kyau a hannun baqaqen mata,bai sani ba ko don yakan manta da kalar lalle idan ba hannunta ba?,don idan kaga Zainab din da lalle to kan tabbatar lallai akwai biki a dangi. *HUGUMA* *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 14 *_RUK'AYYAT GRAPHICS_* *_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_* *_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_* *_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_* LOGO INVITATION CARDS BANK STICKERS BUSINESS LOGO SAVE THE DATE P.O.S BANNERS BIRTHDAY CARD BOOK COVER DATA FLAYER BIRTHDAY VIDEOS VIDEO INVITATION AI PICTURES _KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_ *_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_* *RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku _KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_ https://wa.me/+2347084515410 _ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_ ________________________________ "akwai maganar da nakeson muyi,saidai bansan yadda zaku fahimceta ba" saleem din ya fada a tausashe yana jan plate din data ajjiye masa a gabansa don ya qagu ya fara cin abincin,iya qamshin abincin kadai ya isa ya sa ka zaqu kakai bakinka,kada ma ayi maganar farfesun kayan cikin da yaji spices. Zama tayi sosai a gabansa kaman zata koma cikinsa ko kuma an bata gadinsa tana dubansa da wani tattausan kallo. Idonsa ya lumshe ya sake budewa duka lokaci guda yana dubanta qamshinta yana kai masa ko ina "Uwargida sarautar mata" ya samu bakinsa da fadi. Wani shagalallen murmushi mai qaramin sauti ta saki tana watsa idanunta "Itace maganar da kace zakayi din?" Kai ya girgiza "Bansan ya akayi bakina ya subuce ba" "To ka gyara bakinka tun kafin umman haneefa ta iso,don nidai ba ruwana" "Laifinki ne hajjaju,irin wanann kallon na rantse tsaf zai hanani cin abincin nan,bari kiga tun baki cikamin cikina da soyayya ba" rausayar da kai tayi tana sake sakin siririyar dariyar. Itakam har abada koyon kyawawan dabi'un da zasuja hankalin miji ba shakka sun biyata,don ko yaushe suna wanketa ne a idanun saleem,koda bata sanyawa jikinta komai da zaija hankalinsa din ba,iya kallonta kawai ya wadatar. "Umara nakeson muje gaba daya,ni dake da hajiya sai zainab,to amma kudin hannuna basu cika ba,kudin tafiyar mutum uku ne ba kadan,kinga mutum daya bai samu ba" "Kai,kai ma sha Allah" ruqayyan ta fadi tana langwashe qafafunta "Amma naji dadi qwarai da gaske,Allah ya qara budi,inda duk allura ta fita Allah ya naidata dutse" "Ameen ameen,duka wannan addu'ar haka bayan baki da tabacin kina cikin masu zuwan?" Murmushi tayi masa me kama da harara "Zakaje,hajiya zata je,to meye ya ragemin?,kamar nayi rabin zuwa kenan,rabin kuma sai ranar da ubangiji yayi kirana" zamansa ya gyara yana jinjina kai,ko da yaushe maslaharta itace tasa,koda yaushe buqatunsa take sakawa a gaban nata(maza nason irin wadan nan matan),to shikam me yayi masa saura game da matar kirki?. "Amma sai hajiya tace ko ita z ata haqura naje daku,ita wata shekarar idan da yawan rai tunda alhaji me rasuwa ya taba kaita hajji" Kai ruqayya ke girgizawa da sauri tana dubansa "Kai yanzun koda tace hakan sai kayi hakan?,da yake mu muka haifa mata kai?,sam ba za'a yi haka ba,mu ya kamata mu haqura din,mune qasa da ita,yanzun ni ko Zainab wani a cikinmu zaiso idan su alhassan da khalil sun girma hakan ta faru tsakaninmu da matansu?". Kai ya girgiza yana jin wani sanyi a cikin ransa,lallai ya samu mace ta garin da annabi ya suffanta,yana cikin mazan da suka shigo duniya a sa'a. "Wai da ina ganin zanyi mata gyaran gida ne kafin mu tafin shi yasa" "Dukka ta cancanta daddy,ta cancanci abinda yafi haka ma,hasalima inda zata buqaci ranka ka ciro ka bata baka saka mata da komai ba" ta fadu tana dubansa. Wata ajiyar zuciya ya saki yana jinjina kai cike da gamsuwa,wata irin daraja da kimarta suna linkuwa a ransa,ruqayya macace daya tamkar da dubu lallai ya shaida wannan. Takun Zainab taf taf shine yana hankulansu,suka waiwaya gaba daya suna dubanta. Idanunta akan ruqayya suke,ji takeyi kaman ta shaqota,taji komai a labewar da tayi,banda baqin hali da baqar zuciya da ya cakuda da baqinciki ai ita taso yiwa mugunta. Saudiyyan nan daga ruqayya din har hajiyan ai sunje,shine don tsabar hassada da qyashi me makon ita da tunda tazo duniya ba'a taba zuwa da ita ba tace a dauketa sai tace a barsu?. "Amma dai wannan shawarar ba komai a cikinta sai zallar rashin adalci da qyashi da hassada" Zainab ta fada fuskarta na nuna tsantsar bacin rai. Daga zaunen saleem ya daga kai ya bita da kallo. Tsaiwarta a gurin kawai ya canza atmosphere na wajen. Daurin qirjin nan ne dai na gado sai armless shirt daga ciki,qafafunta tsage tsage a waje kamar sunyi d'ai d'ai "Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar. Cikinta ne ya juya abinda ya Sanya yawu taruwa a bakinta kenan,sai ta juya gefan hagunta ta fesar da yawun tasa bayan hannunta ta goge ragowar da ya bata mata baki. Da sauri ruqayya ta kawar da kanta gefe tana a'uziyya zuciyarta na tashi saboda tsantsami. Juyowa Zainab din tayi tana duban saleem "Ta yaya zakayi shawara da ita ita kadai,bayan ba ita kadaice matarka ba?,ba ita kadaice take da haqqi a kanka ba,sai nayi magana kuma aga na cika qorafi bayan adalcinne sam ba'a yishi ba?" "Ni kika tsayawa akai kina gayan ban miki adalci ba?" Yadda yayi mata tambayar ta bugar mata da gwiwa,amma rashin son gaskiya da jin tafi qarfin ayi mata fada sunyi mata katutu saita kauda kanta gefe ta fara halin nata wato gunaguni "Eh ai azzaluma ka tambaya gashi tana batun ni da ita duka mu rasa ku tafi kai da hajiya saboda tsabar muguntar kowama ya rasa,bayan ko hajiyarma ta taba zuwa ai,nice ba inda na taba leqawa a qa'ida......" Ta fada hannunta a qugunta ba tare data dubeshi ba. "Idan baki matsamin akai ba sai ranki yayi mummunan baci,sakara mara wayo" maganar ta girmi kunnenta don bai taba gwada fadin hakan ba "Um um daddynsu,ya isa don Allah" ruqayya ta fadi qasa qasa tana tausarsa saboda ta hangi fushin da ya fara tasiri a idanunsa "Ki qyaleni na fadi mata,naji ta fara sako batun hajiya ne,ta dauka yanzun daa ne da zan dauki iskancinta akan uwata,wanda kikayi a baya ma na kasa tsawatar miki istigfari nakeyi har yanzu" can qasan zuciyar ruqayya cewa kawai tayi uhmmmm. Zuwan Zainab gidan tana amarya ba ita ba,hatta hajiyan ta shuka mata iskanci kala kala,ba zaka taba zaton akwai wata alaqa ta jini tsakaninta da hajiyan ba,a lokacin bai cewa komai,shi yasa ruqayyan tayi qoqari ta kama mutunci sosai a lokacin (kira ga uwayen gidaje,ina qara gaya muku sau tari ku kike siyawa kanku daraja da mutunci a farkon zuwan abokan zamanku,kuma kuke basu fuska da qofar rainaku tun farko,ki watsar da ita da me gidan gaba daya ki basu space ki maida kanki busy a lokacin da suke ganiyar cin amarcinsu,hakan shine zaifi zame miki alkhairi akan sanya idanu akan duk wani motsi nasu,ranki zaiyita baci ne kina ganin abubuwan da babu lallai suyi miki dadi,ke kuma babu tabbas din zuciyarki zata iya jurewa). Wannan kame kan shine abinda ya jawo har yau duk iya iskancin Zainab da ganin ruqayyan ta tare mata gaba ta tare mata baya ba komai take iya tunkararta da shi ba. "To ai saika dauki mataki yanzu ma bata baci ba" ta fadi a zafafe,saidai gama fadin keda wuya wani zazzafan amai ya biyo baya. Dan janye jiki ruqayya tayi cikin mamaki,zubewar da taga zainab din tayi a wajen ya sanyata miqewa tana fadin "Subhanallahi lafiya?" Qarasowa tayi dab da ita tana qoqarin riqota,saidai wani yanayi dake tashi a jikinta ya sanyata matsawa gefe ta tsugunna tana mata sannu. Mugun galabaita ta fara yi,ita da saleem din suna tsaye a kanta. Wannan abun ya sake bawa zainab dama ta sake ragwabewa sosai ta narke kamar matacciya "Dauko mata hijabi mu tafi asibiti" tsam ta miqe tana juya yadda Zainab din ta sake gaba daga yin amai?. Eh tayi wani irin amai mai yawa a gurin amma baici ace ta sassake haka ba. Sau biyu tana sallama yaran basuji ba saboda sun qure qarar tv sunata kuma damben fada
Chapter 18 · 0% Book details