← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 40

Sashe 24

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dinta ke a gyare ne take juya gidanta, don da ganin kura taci mutum,yadda jimmy din keta wayoyi cikin isa da qasaita y tabbatar mata isassar macace ita a gidanta,kuma komai tace tanaso zataji nurse tayi sallama ta miqo tace inji wane,hakan kadai ya isheta amsa. Murmushi ya kubce mata,Allah ya nuna mata wannan ranar,ranar da saleem zai dawo tafin hannunta,dole ruqayya ta dandana kudarta yadda ya kamata. Tare suka jero shi da ita cikin asibitin,yana riqe da kwandon kayan abincin tana a gefansa. Kallonta yayi kadan ta gefan ido "Yane?,tunda muka shigo naga kinata faman toshe hanci?" Fuska ta yamutsa tana sake jan gyalenta zuwa hancinta "Warin asibitinne baiyimin ba,sai shigarmin hanci yakeyi yana damuna" ta fada tana jin har cikinta yadda yake hautsina mata 'yan hanji. "Sannu,ai ba jimawa zamuyi ba,nasan sallama likitan zaiyi" "Ba komai" ta amsa masa tana sake toshe hancinta da kyau. Sallamarsu ita ta farkar da ita daga saqar da takeyi cikin mugun zare. Tare suka daga kai da jimmy kowa ya amsa sallamar gwargwadon muryarsa. Fuska zainab din ta tsuke ganinsu tare,ranta ya raya mata ita ta riqeshi basu fito ba sai yanzu har qarfe goma. Qarasawa ruqayyan tayi ta jawo kujerar da hajiyayye ta tashi dazu a kai zuwa gaban gadon tana cewa da saleem "Bismillah" kwandon ya ajjiye "Kai haba,nifa namiji ne,zauna kedai" "Muna gaisawa zan baku guri ai,ka zauna kafijin dadin dubata" "Dubiyar kukazo ko wasan kwaikwayo?,ko baqincikin daka saba cusan na jiya da ba'a cusan ba aka biyoni asibiti a cusamin" zainab ta fada tana hade fuska kaman zataci babu. Bai dubeta ba yaja kujerar ya zauna,ruqayya ta matsa gaba kadan tana cewa "Sannu maman haneefa,ya jikin?,Allah ya mayar kaffara" "Gani me tulin zunubi ba,dole ki kiramin kaffara ga bijirarriyar musulma" ta maida mata cikin zafi. Kullum sai taga wata sabuwar suturar a jikin ruqayya,kullum walau a cikin gida ko a waje ruqayyan cikin ado da sauya suttura take. Tayi ado duk da baby kwalliya ko kadan saman fuskarta amma adon dake jikinta zaka tsammaci bawai asibiti zataje ba "Zunubi kam aikowanne bawa yana tattare dashi,saidai ka zama me neman yafiya wajen Allah" ruqayya ta maida mata tana takawa a hankali tana barin wajen don ji takeyi kamar amai zai taso mata "Idan baka zalunci bayinsa bafa" zainab din ta fada cikin son maida raddi "Ya isa haka,likita ya shigo?" "Eh ai bazai zauna jiran zuwanku ba,yace qarfe sha biyu zai sallameni idan likitan rana yazo" ta fada tana hade fuska. "Sannu" ruqayya tace d jimmy sanda ta isa daura da ita zata zauna a kujerar da take a wajen. "Yauwa sannu" jimmy ta amsa da fara'a sassanyan qamshin dake tashi jikin ruqayya na burgeta(qamshi fa yana jawo maka farinjini a wajen mutane tabbas,ku zama masu qamshi don Allah yan uwa mata ). Haka kawai taji ruqayya ta burgeta,tuni kuma ta fahimci itace kishiyar da zainab ke qorafi akai "Kayyasa,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa ai" ta fada can qasan ranta. Tazarace mabayyaniya me dimbin yawa tsakaninta da ruqayya. Ko a yanzun taga dabbanci da hauka a wajenta. Sun iso ruqayya na tattalinsa duk da tare suka kwana,ke anzo dubaki ba wani feleqe ba komai,jiya baki wanka ba me makon yau kafin su iso ko fece jikinki ko yaji dadin kallonki amma kin zauna kamar tsumammiyar jaka,sun iso da kayan abincin ba gaisuwa ba ya ka kwana ba sannu ba godiya kin buge da qorafi ke 'yar sakin zuciya,kamar ke kikafi kowa zuciya,BA KISSA BA SIYASAR ZAMA DA MIJI BA TSAFTA BA MAGANA ME DADI amma tsohuwar ballagazar dinki take buqata ayi mata, tabdijan!,Allah yasa ranar farko ya balle matsiyaci!. Jimmy ta raya a ranta dariya na balle mata har sai data toshe fuskarta da pillow. Tunda ruqayyan ta fidda wayarta take danne danne abinta,ko sashen da suke bata sake kalla ba bare taga abinda ranta zai baci. Yanayin basarwarta da kawaicinta ya sake burge jimmy qwarai,ta tabbatar da wata ballagazar ce itama da tuni tana gabansu ta kafa ta tsare,zainab zata yita yin abu da gayya ita kuma nata ran yana baci. A hankali ta dafe qirjinta saboda taso mata da amai yayi. Jimmy daketa aikin jarida tsakaninsu ta kula da haka,saita aje wayar hannunta "Lafiya?" Dan murmushi ta sakar mata "Lafiya ba komai,na gode" "Kaman yunqurin amai naga kinayi,ga leda don kada yazo bagatatan ya bata jikinki" jimmy ta fada tana cire wata leda da aka siyo mata gasashen nama a ciki ta bata. Qamshin Naman da ya daki hancinta ya sanya tasowar amai din gaba daya,tasoma kwarashi cikin ledar. Qarar aman ya jawo hanakalin saleem da Zainab,saleem din ya miqe da wani irin gaggawa ya isota yana tallafeta. Zainab na zaune ko motsawa batayi ba,wani abu ne kadai ke yawo mata cikin kai "Ruqayya da amai?,tabbas amai na daya daga cikin manya manyan sign na samun cikinta,cikine da ita?,ciki fa!!" Ta fada cikin zuciyarta wani tashin hankali yana zarto mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa yanzun qafafunta. https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 20 _Wai Allah ,da qyar na qwaci kaina nayi wannan,ayimin afuwa don Allah,zainabu na gaisuwa ga jama'arta Gaba daya sai ta koma kamar mutum mutumi,ta dinga binsu da idanu harta gama aman,jimmy da tafi kusa da ita ta bata ruwa ta kuskure bakinta,saleem ya karba ledar ya qulle ya yar. "Danqari!!,ana dara......." Zainab ta fada cikin zuciyarta wadda keyi mata suya "Inaga kamar akwai likita ko?,muje ya dubaki karmu wuce gida abun yafi haka" saleem ya fada cikin kulawa ganin yadda jikinta ya saki. "Allah ya sawwaqe" jimmy ta fada tana komawa gadonta "Ameen na gode" ruqayyan ta amsa mata tana fita a dakin. Batasan ya suka qare ba,ya kusa mintuna uku sannan ya fito suka wuce karban file. "Kinga irin zallar rashin adalcin da ake gwadamin ko?" Zainab da idanunta suka cika da hawaye tace da jimmy "Ummmm,na gani" ta amsa mata tana bata haushi saboda yadda ta karanceta,sam bata iya mu'amala da miji ba,maganganun data gaggasawa saleem kafin ya fita ta tabbatar inda wani namijin ne me saurin daukan mataki daga nan saidai tayi gidansu,kai koda a dadiro ko dandi ne tabbas ba abinda zahana ya lakada mata na jaki har dai an qwaceta. Amma maganganun da ya dasa mata a rai da me hankali ce ita ya kamata taji zafinsu ne ta kuma dauki haske. "Banda aikin asiri.....kazo dubaninamma idanunka ya rufe ba tani kake ba?,don kawai tayi amai?" "Ai aman kawai ne?,bashi kikeyi ba ke sanda aka kawoki asibitin nan?" "Eh amma ni harda gudawa" "Baiwar Allah ai ciwo ciwo ne ko?,sannan nifa a nan banga aikin asiri ba,kawai dai ta fiki sanin kanta ne da alama" kamar cakewar mashi haka maganganun jimmy suka tsaye mata a rai,ta zuba mata fusatattun idanunta tana kallonta. Banda tana tsoron kada ta yiwa kanta sanadin dinkin da za'a yi mata wallahi da sai ta gaggasa mata maganganu "Ban gane nufinki ba" "Maganata a bayyane take ai,baki iya kula da mijin ba,baki da lafazi baki da mu'amala,sannan ki kalli jikinki da nata daya ne?" Jimmy ta fada kai tsaye tana kallon cikin idanunta. Dif sukayi su duka, abinda ya kawo katsewar maganar tasu shigowar hajiyayye, jimmy ta dauke kai taci gaba da harkokinta. Bayan duka tambayoyi sai aka bata gwajin PT don alamu sun nuna hakan. Gwajin kuwa ya fito da sakamakon da ake zargi na juna biyu. A take akayi mata scanning don duba baby. Scanning din ko ya bada sakamako me ban mamaki. "Cikinki ai yayi wata biyu harda rabi ma,kuma dukkan wasu alamu sun nuna twince ne,matso ku gani" likitan ya fada yana zooming scanning din. Wani mugun sanyi jikin saleem din yayi,ya dinga jin tsoron Allah yana ratsashi,anya ruqayyan ba wani matsayi gareta wajen Allah ba da yakeson nuna masa ishara?. Duk wani gwaji anyi ance ruqayyan sam bata taba haihuwa,amma cikin hikimar buwayi gagara misali sai gashi yanata nuna ayoyinsa. Ita kanta a karan kanta sai ta dinga jin girman Allah da girman al'amarinsa yana sake shigarta,ta dinga tasbihi a gareshi tana jin zuciyarta tana tsinkewa "Ki yafemin don girman Allah,saboda bansan me ubangiji yake nufi da hakan ba" saleem ya fada yana tsugunnawa a gabanta harda hade hannayensa biyu "Na yafe maka fa,na yafe maka tuni,komai da ka gani muqaddarine daga Allah" ta amsa masa tana jin nauyin duqa matan da yayi. Kafin su dawo hajiyayye tayi parking kayansu gaba daya saboda anyi sallama,wanda inda ta biyewa zainab motar haya zasu tara su wuce gida ba tare da sun jirashi ba. Tanata kumbura tana wani babbankewa ta wuce gaban mota. Itakam ruqayya ma dariya ta bata,yanzun ita kuma me ya rage mata?,Allah ya mata komai na rayuwa da mace keda burin samun bakin gwargwado,saidai ci gaba da neman qari. A gidan duniya rashin zuriya ne damuwarta,sai gashi Allah ya wanke mata hakan y bata ya bata ya sake bata wasu. Koda suka wuce gida bangarenta ta wuce kai tsaye abinta saboda sam batajin qwarin jikinta,gaba daya tunda ta yi aman kamar laulayin aka zuba mata,zainab kuwa suka wuce da hajiyayye nata sashen,wadda ta matsa ta biyota din,tunda daima tasan nan da dan kwanaki saleem din zai wuce umra shi da hajiya. Tace dai iya yau zata zauna din,idan ya tafin ta dawo. Tunda ta zube a kujerar falon nata take saqawa take kwancewa,gaba daya komai yana neman qwace mata,wannan cikin na jikin ruqayya ya zame mata qadangaren bakin tulu,ya akayi har ruqayya ta rigata samun cikin ita tana zauna?,bayan ta shigo ne don ta haihu?,don ta cika gida da 'ya'ya ta yadda gida zai zama nata sai yadda tace?. Duk yadda hajiyayye takai ga aiki sai data sare,da farko ta dauka lalurarta yasa sashen nata yake kaca kaca haka,saita zage ta fara gyarawa. Saidai sai data fara gyaran ta fahimci lallai shayi ruwa ne,don kuwa tsohuwa kuma tsumammiyar dauda ce danqare a sashen. Iya dakinta da kitchen ta gyara ta dawo ta zauna tana maida numfashi,ta dubi Zainab dake a jabe "Gaskiya magana ta Allah muddin ba zaki gyara wannan annamimiyar qazantartaki ba to kin shiga uku wallahi,aiki tun kana na marmari har ya koma maka na jaraba?,yanzu don manzan Allah uban panties da kika tara a bandakinki cikin bathtub na meye?, harda me jini a jiki fa?" "Don Allah kada ki qaramin tension akan wanda nake
Chapter 24 · 0% Book details