← Book details Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 40

Sashe 38

Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kuma tarin marasa lafiyar da Allah ys jarabta da ciwuwwuka. Sashen emergency na asibitin ne suka amsheta da gaggawa,saboda duk da kasancewarsa private amma babba ne,suna da tarin kayan aiki qwarai da qwararrun ma'aikata. Koda suka shiga da ita dakin marasa lafiya ita da saleem din zaune sukayi suna dako. Tana ankare da saleem din da ya kasa zama,sai dan tattaki da yakeyi kadan kadan daga hauni zuwa dama. Ba jimawa ya qaraso inda take ya zauna dab da ita,ta daga kai ta kalleshi suka hada idanu "Kina da masaniyar wani abu akan ciwon nan na zainab?" Ya yiwa ruqayyan tambaya muryarsa a raunane. Yau din sai taji ba zata iya bagarar dashi ba kaman yadda ta saba a duk sanda ya sako mata zancan zainab "Bansani ba,bansan komai ba,yadda ka ganta yanzun haka na ganta" shuru ya danyi,sannan yaja iska ya fesar "Jikina yana bani koma meye yana da alaqa da ta'ammali da gurbatattun magungunan matan da batasan ingancinsu ba anyhow" dubansa ruqayya tayi da sauri sai kuma ta sauke kai batace komai ba. "Ina wadanda suka kawo Zainab!,kuna ina!,bawan Allah kune?,ku taso maza maza!" Nurse din data leqo cikin daga murya da alamu na kiran gaggawa ta daga musu hannu tana fada. Ruqayya bata motsa ba saboda tana ganin ba huruminta bane ta shiga din,amma sai saleem ya kalleta "Taso muje" zata musanta ya saka hannunsa ya jawota sukayi ciki. Kukan Zainab suka fara cin karo dashi wadda ke maqure saman gado tana gunza kuka,sai nurses guda biyu a gefe da suketa magana cikin bacin rai da metron daya. Hankalinta yayi mugun tashi da taga tare suka shigo da ruqayya,sai taji kamar ta bankawa wajen wuta a tashi ba tare da anyi maganar komai ba "Malam ya akayi kabar matarka ta rube don girman Allah?,a haka kuma kake iya mu'amalar aure da ita?" Daya daga cikin nurses din ta fada bacin rai yana bayyana qarara saman fuskarta. Wani kallo ya watsawa matar saboda rainin hankalin da yaji qarara cikin tambayarta,shi zai riqa yawo ne da zainab duk inda zashi yana kula da gabanta?. Metron din data fuskanci kamar ranshi ya tabu da maganar saita dagawa nurse din hannu sannan ta dubi su saleem "Bismillah ku zauna" "Harda kishiyar tawa?" Ta zabura tana fadi.duk da radadin da take ciki. Dukkansu suka zuba mata ido,nurse din nan dai wadda da alama zafi gareta tace "Bakison kishiyar taki tasan me kike ciki kikayi wasa da gabanki?" "Ya isa hadiza" metron din ta sake fada. Zama sukayi gaba dayansu,metron ta kallesu "Alhaji a gaskiya duk da mu ma'aikatan lafiya ne,muna kuma ganin abubuwa kala kala amma case din matarka ya tashi hankalinmu,al'aurar matarka idan bai rube ba to yayi lalacewar da bashi da maraba da rubewa,akwai dinki a jikinta wanda bai samu kulawa ba,an barshi sasakai har ya gama farkewa gaba daya" "Na shiga uku dinkina!" Zainab ta fada tana dora hannu saman kai kaman ma ta manta a inda take. Idanun saleem da ya juyo ya watsa mata su wanda zuwa yanzu sun sauya launi sune suka ankarar da ita,ta kuma tuna ta yiwa kanta barna zata tonawa kanta da kanta asiri. Wannan abun kawai da tayi ya tabbatarwa da saleem ta aikata din,ta kuma yi komai ne tana sane,don haka ya maida dubansa ga metron "Bayan ya farke kuma da alamu infection sunbi sun shiga ciki yadda sukaga dama saboda rashin tsaftar gurin,sannan da alamu akwai abubuwan da ake yabawa wajen da basu cancanci zama a wajen ba,jinin kuma dake zuba a jikinta wannan gaskiya zan turaku zuwa ga doctor nur,tana nan a hawa na farko,amma dai ina addu'a abinda nake hasashe Allah yasa ba shine ya sameta ba" "idan ma shine ticket din data yankawa kanta kenan" ya fada qasa qasa muryarsa dauke da maqurar bacin rai. "Idan kun gama ganin Dr nur din zatayi magana damu tabbas,amma dai yanzun na tabbatar ba wanda zai iya ganinta a haka sai an fara maganin d'iwa da jinin dake fita a jikinta,idan sun tsaya ma sannan a fuskanci ainihin ciwon da yake jikinta da farkakken HQ din da ya riga ya bude sosai tunda an sake yagashi an dinke kuma ba'a dinke dai dai ba" kaman ta sake dora hannu a kai ta zunduma ihu dajin bayanan nurse din,yanzu ita daje beman tsukewa saboda lalacewa saita bude budewar da tafi ta baya yawa da muni?. Bai sake cewa komai ba kaman yadda ruqayya ta buga tagumi jikinta a mugun sanyaye,tamkar itace cikin matsalar, zallar mamakin zainab ne yake sake mamayeta,yanzun ita saboda kishiya da miji harta aminta ta cutar da kanta har haka?,yanzun gashi cikin su uku waye a ciki?. Duk zaman bin layi zuwa shiga wajen dr nur da sukayi saleem baice ta tafas ba,duk da irin ciwo da radadin da zuciyarsa ke masa wannan wanne irin tonon silili ne Zainab din ta jawo masa,har dinki taje akayi mata?,ta bankada al'aurarta ba tare da saninsa ba?,macece namiji ne waye yayi mata oho?. Tun daga shigarsu tsantsami ya kama dr nur kasancewarta me tsananin tsafta,saidai salon iya aiki yasa ta jure illa facemask data saka. Kai kawai take jinjinawa bayan ta gama gwaje gwajen da suka dauki lokuta sunayinsu "Kin samu cutar CANCER ciwon daji na bakin mahaifa wato CERVICAL CANCER" "CANCER kums likita?!" Zainab din ta fada a mugun gigice,gigicewar da ba ita kadai tayita ba hatta da ruqayya sakamakon ya girgizata,bare saleem da ya dasu a gurin bakinsa ya gaza furta komai. Kuka da tumami Zainab din ta farayi cikin matuqar razani da firgita, duk yadda dr nur taso tasha kanta tayi shuru amma ta qiya,har saida bakin saleem ya budu ya daka mata tsawa. "Ki tashi ki mata bayanin dame dame kika cusawa gurin ya zama haka?" "Tana inserting wani abune?" Dr nur ta tambaya tana duban saleem cikin ranta tana hango banbanci qarara tsakaninsa da zainab din qasan ranta tana fadin "Aure me hade hade" don ko kusa ko alama babu daidaituwar aji tsakaninsa da ita. "Zakiji a bakinta,inajin har fitsarin jaki sawa takeyi" ya fada yana miqewa don ya tabbatar Allah ne kadai yasan me dame Zainab din tayi. Yasha ganinta yasha kuma hanata tare da gargadinta sau babu adadi amma bataji ba. "Yallabai haquri zakayi ka zauna mu fuskanci matsalar nan a tare" Dr nur da itama ta fuskanci asalin fusata daga wajensa ta fada "Na gama da matsalarta ni,na gama fuskantar matsalarta,yanzun matsalarta tatace,Allah ya bada mafita" galala zainab din tayi tana jin asalin tashin hankali yanzu yana ratsata. Kadadai ace iqirarin da yasha yi mata wanda ita bata daukeshi a bakin komai ba a sannan a yanzu ne wa'adinsa zai cika?. "Don girman manzan Allah kayi haquri ka dawo ka zauna", ruqayya da tayi tsaye a bayansa ta fada a tausashe. Ta hadashi da babban bango kuma dan gatan Allah wanda bazai iya tsallakewa ya qetara sunansa ba,don haka ya dawo yana shirin zama,ita kuma tayi qofa zata fice don ta gaji da jin wannan tashin hankalin "Ke kika dawo dani dole ki zauna kema" saleem din ya fada a kausashe. Juyowa tayi tana kallonsa "Ita meye nata a ciki dama?,banda ma son a tozartaka ya za'a yi kishiya ta dinga jin sirrin ciwonka?" Zainab ta fada cikin muryar kuka. Wani kallon banza saleem ya watsa mata "Ke kikaso,ita aji nata mana" . Kasa dawowa ta zauna ruqayya tayi,tana daga tsaye jingine a bango kanta a qasa cikin tashin hankali. Tiryan tiryan zainab ta rattabo bayani da bakinta,abinda ya tashi hankalin kowa a wajen,ruqayya tsigar jikinta ta dinga tashi sai ta bude qofar kawai ta qarasa ficewa ba tare data jira umarnin saleem ba. Motarsa ta koma ta zauna tana maida numfashi,abu goma da ashirin,ga tashin hankali ga tashin zuciya,saita kwantar da kujera tayi kwance kawai tana maida numfashi. Kusan awanni biyu cur sannan taji shigowar saleem din motar,har tayi bacci ta farka,ta miqe ta zauna tana duban fuskarsa da babu alamun walwala a tattare dashi. Kiran waya yakeyi don haka batace dashi komai ba har aka daga,sai a sannan ta fahimci yayan zainab yakewa magana yana shaida musu tana asibiti an bata gado,a taho dame kula da ita "Subhanallahi me ya sameta" "Zatayi muku bayani idan kukazo" abinda yace dashi kenan. Baice komai da ita ba bayan ya gama ya tashi motar ne kawai suka wuce gida. Itama sai taja bakinta tayi shuru. Ranar gaba daya sukuku ya yita,damuwa ce fal ransa da bacin rai zallah,da akazo diban kayan zaman asibiti na zainab din ya sanya haneefa ta debo kayansu ita da khalil. Yarinyar nata murna ta debo din,saidai duk cikin kayan babu wani na arziqi,sai baya ruqayya tasa aka kaisu aka sake wankewasu fes. Bata sake masa magana ba sai washegari da safe da zata shiga kitchen hada musu breakfast "Yaushe zaka fita asibitin zan hada musu da abinci" "Ba yanzu ba,idan kina da me zuwa ki bayar yakai" ta danyi mamaki don ba haka yakeyi ba duk sanda wata ta kwanta asibiti ita ko zainab din "Ba damuwa,zan samu na kammala da wuri sai na fita nakai" "Ban aikeki ba" ya fada, koda ta dakata tana neman ba'asi blanket yaja ya lullube kansa abinsa ya juya mata baya. Kwana uku tayi tana aike musu da abinci,a rana ta ukun sai bayan qarfe goma na dare ya shigo gida. Tana zaune batayi bacci ba don ta kasa,saboda ba sabonsa bane yin dare a waje,ta kuma kikkirashi amma bata sameshi ba. Tunda tayi masa sannu da zuwa ta tabbatar akwai matsala babba tattare dashi. Har zuwa sanda sukazo kwanciya ta dubeshi "Gobe inaso naje na gano jikin zainab in sha Allah " "Ba zaki ba" ya fada a taqaice yana gyara pillow dinsa. Ranta tadan bata kadan "Me yasa kake haka ne?,ko yaran aika bari su ganta ko?" "Ce miki akayi ana ganinta?,ko salon idan kinje kin dawo ki ishi mutane da koke koke?" Ya fada yana tuna yadda likitan dake kan dubata a yanzun yayi masa bayanin irin illar da ciwon yayiwa jikinta da sassan mahaifarta,ransa yana baci kuma idan ya tuna yadda sam bata rusuna ba saima zagin ruqayya da takeyi duk da alkhairinta gareta da yadda ta hana kanta zaune kullum cikin girkin safe rana da dare. "Karki sakemin wannan maganar,hasalima mamanta ta nema mata saki tace sakacina
Chapter 38 · 0% Book details