Sashe 8
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haqura da nufin aika zafafan saqonnin ya koma kan hanyar da itama zainab din ta baje take jira ya isa ga gurin,a wajenta duk wadan nan abubuwan da yakeyi din bata lokaci ne kawai,tafi ganewa kai tsaye a shiga karatun. A yadda komai ke tafiya ya saka farinciki a zuciyarta ya kuma tabbatar mata da lallai yau din taci kudinta. Saidai a gefen saleem tun yana fahimtar abubuwan suna masa yadda yakeso har ya fara shiga wani yanayi na mamaki. Buqatuwarsa ta yau ta wuce ta kullum,abinda bai taba tsintar kansa a ciki ba muddin yana tare da Zainab dinne. Lokaci da qa'ida daya kamata ace komai ya lafa yazo qarshe sai ya kasa dakatawa. A hankali jikinsa ya fara weakening bugun zuciyarsa yayi mugun linkuwa,abinda ya haifar masa da haki da wani mahaukacin gumi. Bazai iya cewa ga yadda akayi ba,shi dai ya samu kansa da yin wani dummmm,kafin daga bisani yaji kamar jijiyoyin jikinsa basa aiki,ya sulale a hankali yayi kwance a gefe yana fidda numfashi. A qalla ya kusa mintuna goma a haka,sam bata lura ba tana daga kwance ta sheme tana sakin murmushi hadi da kada idanu,lallai yau akwai babbar kyauta da zata samu daga wajen saleem. Komai ya gudanar cikin wani irin zafi da kalar buqatuwar da takeso kullum ta ganshi a ciki. A hankali numfashinsa ya fara dai daita saidai yanzu kansa bai sauka daga nauyin da yayi masa ba,hakanan gangar jikinsa babu wata gaba dake da qarfi ko kadan. Miqewa yayi ya zauna yaja jikinsa da qyar ya wuce bandaki,da kallo ta bishi tana gyara kwanciyarta murmushi yana sake fita a fuskarta. Har ya fito tana kwance,ya goge jikinsa da towel ya sanya baqin gajeran wando da singlet ya dawo gefen gadon yana takawa a hankali ya zauna yana bata baya. "Tashi" yace da ita. Wannan ba sabon abu bane,duk sanda mu'amala ta shiga tsakaninsu shike fama da ita akan ta tashi ta tsaftace jikinta,har yau har kwanan gobe kuma bata canza ba,koda alwala kadai sai yayi yaqi takeyi bare wanka da sai da safe ma wani zubin sannan ta rattaba sallarta ta kuma hau shirya yara zuwa makaranta,wannan ya zama silar da duk sanda wani abu ya shiga tsakaninsu sai yara sun makara a makaranta,koda su alhassan sun shirya da wuri kuwa,tunda tare driver yake kaisu. Wannan ya sanya tun hankalin ruqayya baikai ba har ta fahimci abinda ke jawo hakan,saidai koda wasa koda saleem din bata taba nuna masa tasan dalili ba har yau har gobe. "Ni gaskiya bazan iya tashi ba,haba kaman ba kaga rashin imanin daka yimin ba yau,alwalar ma idan Allah ya kaimu asuba nayi" ta fada tana wani narkewa. "Me kika bani na sha zainab?" Ya jefa mata tambayar ba tare da ya waiwayo ba. Ido ta fidda waje hadi da tashi ta zauna ba tare data shirya ba "Me kuwa zan baka daddyn haneefa,me ya faru?" Waiwayowa yayi yana dubanta da idanunsa da suka sauya launi saboda kansa da yakeji ya masa nauyi "Yan ayina ya canza,ba haka nake ba" "Okay,inda a tattare da ruqayya ka samu hakan ba zakace komai ba,saini saboda ban cika macen da za'a ji haka tare da ita ba?" Sai ta fashe masa da kuka. Can qasan ranta tasan tabbas ta kusa jawowa kanta matsala ne kawai,dose din maganin qwaya daya ne amma ta saka uku,kuma taji suna shaqiyanci a group din tare da gargadin masu wuce gona da iri din irinta ko ita a yanzun bawai ta gama sauka bane,amm bataga ta bakin cewa komai ba gudun tabbatar masa da zarginsa. Zazzabi yakeji a jikinsa baya kuma buqatar wata doguwar hayaniya ko qorafi,don haka ya dauke kansa yaja jikinsa ya koma saman gadon yana rufa da blanket idanunsa a rufe yana ambatar ALLAH qasa qasa. *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 06 *****Kamar kowacce rana da zata karba girki,duk sanda ka ganta tana gyare gyare zaka tsammaci wata tafiya me nisa saleem din yayi yake shirin dawowa. Kusan komai na dakin sai ta tabashi,wani ta canza masa guri wani ta gogeshi wani ta sauyashi gaba daya. Kafin azahar sai ta tabbata komai na dakin ya sauya daga ainihin yadda saleem ya fita ya barshi. Sha daya na rana ta fito daga dakin bayan ta gama kintsashi. Qofar ta murda ta bude ta fito parlor dinta hannunta riqe da qaramin towel da tayi goge goge dashi. Alhassan da alhussain ne zaune sun sanya tv a gaba,sun wani nutsu har abun yaso nata dariya. Ta jima bataga yatan dake masifar son kallon cartoon ba irinsu "Yadda kuka nutsu kuna wannan kallon,kada ku yarda anjima nazo karban hadda naci gyaranku". Yare suka dago kai suka kalleta suna dariya,alhussain ne ya fara cewa "Ni ko yanzu ma mommy ki karba Allah na shirya" "Nima din ai na shirya yaro" alhassan ya fada. Take 'yar musu ta barke a tsakaninsu. Gaba tayi ta barsu a gurin,don irin wanann qananun rigingimun nasu a rana har bata iya riga adadin sau nawa sukeyi,saidai fadan baya nisa ake watsewa,shi yasa ba kasafai ta fiya damun kanta da rabo ba. Gaban fridge dinta ta qarasa,ta saka hannu ta bude tana ciro wata doguwar gora me kyau,sai ta azata saman Fridge tana kallon agogo da dan mamaki a fuskarta. Tun dazun take mamakin rashin jin motsin saleem,duk da bata son zurafafawa kanta da tunanin abinda ya hanashi shigowa dubasu tunda hakan ba sabonsa bane,tanata son kiransa ko tabi ba'asin jinsa shurun amma zuciyarta tana kwabarta. Batason abun rigima da fitina,ko kuma taje ta gano ko ta jiyo abinda zai motsa kishin da taketa qoqarin ganin ta mallaki zuciyarta a kansa. Sai da yadan huce sannan ta bude gorar,take qamshin kanunfari da sauran kayan qamshi suka cika gurin. Tun kafin takai bakinta yawunta ya tsinke,ingantaccen tsumi ne data zauna ta dafashi da kanta jiya da sanannun saqe saqi da danginsu rake mazarqwaila harma da zuma a ciki. Cup daya ta cikashi dashi ta fara sha a hankali. Idonta ta lumshe tana jin dadinsa har saman harshenta,sai data shanye a nutse sannan ta kife cup din wanda yayi dai dai da kwada sallamar Zainab,sannan kai tsaye ta danno cikin parlor din. Hannu ruqayya ta sanya ta dauke gorar tsumin nata tana qoqarin maidawa fridge,duk da ba wani abu bane don Zainab din ta gani ba,koda ta gani tasan ba lallai ta fahimci meye ba,to amma ita din mutum ce da ba komai take bari idanun kishiyarta yakai kai ba (hakan ba laifi bane,yana da kyau ki iya takunki wajen kishiya,ba komai kike bari tana sani naki ba,koda kuwa me kyau ne,akwai abubuwan da sukan zama tamkar wani sirri ne naki,kuma makaminki da kike naki yaqin cikin gidan tsakaninki da mijinki,barin kishiya tasan da wannan sirrin ko makamin tamkar wargazawa kanki da kanki shiri ne). Tuni idanunta suka kai din,tunda itan tana cikin jerin sahun matan da komai kayi suna da buqatar sani ko gani,amma tunaninta sai ya tafi ga wani abun daban "Ana nan ana fama da coca-cola" ta fadi qasa qasa. Bata damu da kallon da ta bita dashi ba,ta gyara zaman tsumin ta maida fridge dinta ta rufe tana amsa sallamar tata "Aron mopper zaki ban yara sun karya min tawa" ta fada tana riqe hannu a qugu. Sau tari tana mamakin Zainab har ba iyaka,duka yara biyu amma idan kaga barnar da ake a sashen nata zaka dauka wasu gayyar yara gareta. Duk tsananin baqin kishinta kuma bata kunyar aron abu daga hannun kishiya?,wani abu guda daya tal da ruqayya zata iya bugar qirji tace bata taba yi ba(zubda kaine aron abu a wajen kishiya,muddin ba wai ta kama bane ko ba yadda zakiyi,komai da kikasan zaku buqata keda yara siya ki ajjiye,gwara ke a ara a hannunki). Waiwayowa tayi ga alhassan ta sanyashi shiga store ya dauko mata,saidai sanda ta maido dubanta ga zainab din sai ta sameta tana sana'ar tata wato sanya ido. A duk sanda wani uzuri ya kaita ga shigowa sassan nata to ba zata taba fita ba sai ta yiwa parlor din nata kallon tsaf!,in sha Allah duk abinda ta gani sabo ko baqo sai tayi qoqarin siyan makamancinsa. Abun tun yana bawa ruqayya mamaki har ma sai ya koma bata dariya. "Nikam daddynsu lafiya na jishi shuru bai leqo ba?" Tambayar da tayiwa Zainab mugun dadi,sai ta waiwayo tana sakin murmushi "Angoncinne ya motsa,don da qyar na lallabashi ya fita sallar asuba saboda jiya bamu samu isashen bacci ba ni dashi duka,saboda tsabar duniya ta masa dadi harda wani guntun zazzabin shagwaba" Girma sosai maganar ta yiwa ruqayya,takai idanunta da sauri kan alhassan da alhussain iftee dama baccinta takeyi saman kujera. Allah ya taimaketa hankulansu gaba daya ya tafi kan cartoon din sosai,da alama kunnuwansu basuyi wannan baqin jin ba,sai ta daga ido ta maida dubanta ga zainab. Idanun zainab din fes kan fuskar ruqayyan tanason ganin bacin ran da ta qiyasta zata gani din,saidai ga mamakinta murmushi ruqayyan ta saki bayan ta tako zuwa sashen da take don ta kaucewa kunnuwan yaran jin abinda bai shafesu ba "Ayyah,kayya kiyi masa sannu,ai ban sani ba,bai kamata ace har wannan lokacin ba'a shiga an dubashi ba,amma ina nan shigowa na duba angon naki,irin wannan dattijon amarci ga shekaru ga kuma bar muku sudi?,da kin sani ai aikomin kikayi dasu haneefan,kinga ni lokacin nawa amarcin duk girman gidan nan daga shi sai ni,baccin shekara ma sai muyi babu me tashinmu". Baki Zainab din ta tabe,maimakon ran ruqayyan ya baci sai tata zuciyar ta soma motsawa "Ah ai kunsha bacci,shi yasa tsabar bacci aka dauka juya ya auro" "Sai kuma ga mazaje har guda biyu sun wanke sunan ummansu daga juya zuwa uwar maza ba" ta maida mata amsar tana tsuntsira dariya abinta hankali kwance. Baki yasan abinda zai furta saidai kuma bashi da masaniyar amsar da za'a bashi. Maganar ta sake tunzura Zainab din,sai ta juya tana ficewa a gurin "Ki bar mopper din a wajenki idan kin gama" ruqayyan ta sake fadi,saidai ko waiwayowa zainab batayi ba ta qara gaba. K'aramar dariya ruqayya ta saki,kwata kwata wautar zainab take gani,idan tasan halittar ta saurin fushi,tunzura da rashin iya cinye bacin rai,to ya kamata ta kiyaye shiga ko faro maganganun da amsarsu ba zasu mata dadi ba,ta dinga kame kanta da hana kanta da kanta shiga hurumin