Sashe 30
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
"Kinga fa umma sai kallonki akeyi" ta fada tana kyabe baki cikin tabara. Tana waiwayowa batayi wata wata ba ta tsinketa da mari hadi da ingizata cikin motar "Kece sila da kika raina uwarki sai uwar wasu,sai nayi maganinki wallahi zakisan da waye kike magana" itadai yarinyar bata amsa ba sai kuka da take gurzawa cikin motar kamar wadda aka tsinkewa rai. "B kowanne lokaci bane ba kuma ko yaushe ne idan kishiya tayi miki abu kike tanka mata ba,ba kishiya ba hatta dashi mijin da kike zaman domin shi,yawaita tankawa kishiya akan ko meye tayi miki yana sanyawa ta rainaki,ta gane lagonki,ta kuma fahimci abinda bakiso da abinda yafi qona miki rai,wanda wadannan kuma sune makaminta da zata yita yaqarki dasu tana hanaki sukuni. Sa'insa ko tankiya yawan maimaitasu ba abinda yake haifarwa face jawo raini da zubewa girman babba. Duk mace idan taso tana iya siyawa kanta kwarjini da martaba a idanun kishiya,ita zainab da kike gani,har yanzu batasan mene yake mugun bata raina ba,har yanzu babbankiya takeyi saboda naqi bata wannan damar,har yanzu duk sanda zatayi iskancinta bata isa ta shigo sashe na ba iyakarta farfajiya,kuma har yanzu bata isa ta saka hannu a kaina ba,har kwanan gobe kuma akwai fadan da bata iya tsaiwa mu yishi,har yau har gobe kuma akwai abinda yake hurumina ne cikin gidan,ita ko shi ba wanda ya isa ya taka,idan na zartar saidai kawai su gani a qasa,koshi bazaice komai ba bazaice kuma don me ba,itama tun tana damuwa har ya zamar mata jiki. Ko zage zagen da takeyi yanzu ai sai dana bada baya bawai cikin idanuna ba. Idan kinso kina iya saiwa kanki wannan martabar,wanda tun farkon kawo kishiya zaki siyeta,ki girmanki da mutuncinki,kada ta sameki kina haukan kishi,ki nutsu ta sameki me cikakkiyar nutsuwa,ki yawaita addu'a da roqar Allah ya haskaka fuskarki a idanunsu ita da mijin,sannan kiyi fatan Allah ya baki mijin da yasan darajarki,don gwargwadon yadda ta shigo taga miji yana qimantaki gwargwadon yadda zata fahimci muhimmancinki,koda baya baki martaba shi da ita ajesu a gefe ki kama kanki,ki ki aikata musu a aikace ba ta hanyar magana ba cewa kefa kinsan kima da mutuncin kanki,ko baya qaunar Allah dole yayi biyayya koda bai shirya ba,musamman idan ke din ma'abociyar addu'a ce,me tsarkakkiyar zuciya,wadda baki zaluntar kowa kina qoqarin fita haqqin kowa" shuru wasila tayi jikinta ya sake,zuciyarta kuma na juya kalaman ruqayya. Tabbas tun suna qananuntasan ta fita hikima,ba komai bala'i da masufa yake baka shi ba. Hirarsu ta duniya sukaci gaba da yi wadda cikinta a yau wasila taji tana qaruwa. A nutse take musu tuqi har suka isa gida. Taso ta saka motarta ciki amma saita lura da motar zainab wadda aka yiwa wani banzan parking,so babu hanyar da zata shiga din,don haka ta tsaida motar ta fito tana cewa wasila "Bari naga me ya faru,idan ta matsar da motar ki shigo min da ita ciki,fitsari nakeji sosai" "Yauwa nima yau na dan dana kafin Allah ya kawo mana me siya mana muma" wasila ta fada cikin zumudi tana komawa seat din da ruqayya ta tashi a kai. Tana shiga farfajiyar gidan ta tambayi yaron gidan nasu ya aka ajjiye mota a haka?. Cikin dan rusunawa yace "Ummansu haneefa ce,nima nayi mata magana da nufin ta gyara ko bata lura bane ta zageni tace yau a haka taga daman ajjiyeta" dan jim ruqayya tayi tana gyada kai,sai ta koma da baya ta yiwa wasila magana "Ki ajjiyeta nan qofar gida ku fito ku qaraso ciki" "Me yasa?" "Haka dai nace" ta amsawa wasila tana dawowa ciki idanunta akan motar zainab har ta wuce sashenta.