Sashe 6
Kurman Baki Book 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
taba ce mata ta daina kwalliya ba idan ma wannan shine burinki,kema idan zakiyi babu wanda zai hanaki,hasalima ina maraba da hakan kuma sai nafi kowa farinciki,haka siddan kinason zama qadangaren bakin tulu "sai ya wuce toilet ya barta kawai. "Kadangaren bakin tulu" tayita maimaita kalma,kasancewarta macace me bala'in tsarguwa da sawa rai abu. Wayarta ta dauko saboda ta kasa nutsuwa da abinda yace. Ta bude data ta shiga group dinsu ta kuma antaya tambayar bayan taqaitaccen bayanin abinda ya farun. Cikin qasa da minti biyar kalolin amsoshi suka dinga fitowa,kasancewar group din group ne da baya rabo da jama'a,amsoshin da kai tsaye suka fito mata da ma'anar abinda saleem din ke nufi. Wayar ta ajiye ta koma gaban madubi ta zauna tana duban kanta. Har rana wayau ta kasa gane me tayi wai da ya saka mata da tsanani yake mata kallon qazama,dame ruqayyan ta fita banda baqar fata?. *_KURMAN BA *HUGUMA* PAGE 05