← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 57

Sashe 7

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

'Karfe hu'du na yamma Ra'uf ya sake wani wankan ya shirya cikin kananun kaya ya sauko 'kasa masallaci ya wuce ganin bakowa a falon a masallaci ya ha'du da Dady suka shigo gida tare yana tanbayarsa yanayin aikinsa,a falo suka yada zango inda Dady yake sanarmasa company yabiya da shine dalilin rashin dawowarsa gida da wuri wanda Dady yake da hannun jari a ciki Ra',uf yace "To Dady Allah yayi jagora" yace Amin Babban mutum sunan da Dady yafi kiransa dashi Murmushin sunan da Dady yakirashi dashi yayi yana tuno mai kiransa da sunan da yake tuno rabuwarsu ta 'karshe da ita ya'dan dubi Dady yace" Dady dama maganar kayan da za'a turawa Kawu Mukhtar shine nakeso muyi inasan taimakon kasata yakamata ina bada taimako asibitoci ko yaya ne"Murmushi Dady yayi yace "hakan yana da kyau Ra'uf,Dukda kasartamu akwai arzi'ki amma babu taimako kowa da yasa kansa kawai ya sani rayuwar wani bata damesa ba ,shiyasa har yau 'kasartamu babu cigaba duk mai arzi'ki burinsa sa 'ya'yensa makaranta mai tsada koma subar kasar da karatun gaba 'daya maimakon muyi 'ko'karin bun'kasa 'kananan gurabe zuwa manya manya saboda ko 'kasashen nan damuke ciki ta haka sukayi arzi'ki ,amma saikaga mai arxiki a garinsuma bayason zama da wata 'yar dama tasamesa wani ko gini bazai iyayi a garinsuba, saboda yana tunanin 'kauye ne baya tunanin raya kauyen nasu,wani kuma koda yayi ginin sai yace bazai zauna ba koda aikin gwamnati yayi yayi retire ,ko kuma 'dan kasuwa ne da zai iya zuwa yadawo garinsu,ko kuma wani 'yan mola acewarsa su suka koresa daga garinsu abinda babu mai raba bawa da arziki sai mutuwa,amma sai dai yaje ya raya mahaifar wasu, kuma wasu da yawa idan wata dama tasamesa bazai iya turo ta garinnasu ba ko 'kasarsaba a'a sai dai yabarsu garin wasu kasar wasu Suma marasa 'karfin cikinmu basa baws masu son taimakon cikinmu kwarin gwiwa kuma suma tunaninsu su samu damar suyi fiye da abinda wasu sukeyi shiyasa bama cigaba saboda yadda kowa a yanzu haka kansa ya sani da 'ya'yansa, Nagode wa Allah da 'dana yayi tunanin abu mai kyau Allah ya kara dafamana "Maganar Dady ta shigi Ra'uf sosai yana tunanin rayuwa yadda tazama yanzu ya amsa da cewa" Amin Dady nagode da nasiharka gareni"da wannan zancen Safiyya ta iso falon takatse musu firar ta hanyar sallamarta suka amsa mata ,Inda tana kokarin zama tace Dady shine aka ki kirana muyi fira bakomai zamu rama nida Ammi ,Dady yayi murmushi yace yawwa ai dama munfisan haka gwara kowa ya za'bi gwaninsa" dariya tayi Ra'uf yayi Murmushi yace"ke ina shirin naki "Murmushi tayi tace Yaya nifa nagama shirina dama kainake jira kace nafito" harararta Ra'uf yayi yace"wato nine ma zan je nace miki na shirya?kajitafa Dady",Dady yace"babu ruwa na dashiga zancenku"Ammi ta fito daga kitchen da ruwa na gora a hannunta ta iso da sallama ta zauna kujerar kusa dasu tana kokarin bude gorar take cewa "yanake jiyo hayaniyarku Abban Safiyya ince dai yaran nan ne da basa gajiya da kan kara" wato Ra'uf da Safiyya,Dady yace "kamarko kinsani Asma'u" labari ya bata tace ai saika gaji Indai wa'dannan ne gidan Shureim zasu shine suketa wannan lugyigyita maganar"murmushi Dady yayi yace",ai shine nace bamai shiga fa'dansu"Ammi ta kalli Ra'uf tana canza maganar da cewa "kai wai ina sa'kona" Ra'uf yace "Ammi Safiyya natarar a falo na ajewa"ya kalli Safiyya yace" Baki kaiwa Ammi sakon dana aje ba kuma kinsan na tane"Safiyya tace" Ammi na ajemiki saman madubi danaje 'dakin naga kina barci"Ammi tace" to shikenan jeki ki shirya Ku tafi da haka Safiyya ta mi'ke koda Safiyyan ta iso falon har Ra'uf ya mike tabi bayansa suna yima su Dady sai sundawo.

Basu jima suna tafiya ba suka isa gidan Shureim tarba ta musamman aka musu koda cewar su ba baki bane a gidan Irfan Ra'uf ya dauka ya fice shida Shureim daga falon bayan sungama gaisawa suka bar Safiyya da Inteesar. A jikin motar Shureim su Ra'uf da Shureim suka tsaya Shureim da ya 'dan kalli Ra'uf yace"Abokina kai yaushe zakayi aure kadubafa ni gani harda 'da 'daya,Ahmad kuma 'ya'ya biyu haba Ra'uf ka'din baka tunanin kaima kayi aure kobazakayi dan komaiba ai kariqa duba damu abokanka duk munyi amma kaida kurinka bare kace shiya hanaka yi haba Ra'uf har yanzu tunanin wancen mikin nasan shike dawainiya dakai dukda maganar Ahmad bana tunanin a yanzu abin maiyiyuwane dukda kai din banama sha'awar hakan a karo na biyu domin babu tabbacin zama kasamu abin "kalaman Shureim sunkara tasiri garesa bayan na Ammi data masa Saidai shifa har wayau babu wani tunani a ransa na wata budurwa tun bayan abin da yafaru da yake ganinsu kamar yau batare da an shawarceshi ba aka yanke waccen kyakkyawar ala'kar gani yake da yanzune dasai ya yi fito na fito daduk mai gudunsa da wancen ran da yake gani alkhairine a dunbin rayuwarsa da to zan duba yabi Shureim kawai suka kara ta'ba hira daganan suka karasa masallaci said wajen takwas na dare suka yi musu sallama suka koma gida Inda Ra'uf ko a mota bai kula Safiyya ba ita keta zuba surutunta iyakacinsa da ita ey ko a'a har suka isa gida bai tsaya kula kowa a falon ba Ammi tace ga abincin kazo muci yace yaci a gidan Shureim daganan ya haye bene Ammi da Safiyya damai aikinsu basu damu da maganarsaba dan sunsan baida tsawaita magana wani lokacin Safiyya ko zama tayi ta zuba abinci ta fara shiko Ra'uf kai tsaye dakinsa ya sake ya wuce watsa ruwa yayi sallahr isha',i yayi Azkar kawai ya kashe wayoyinsa ya haye gadonsa da yaketa juyi ya kasa barci sai tunani tunanin da kowanne dare saiyayi rabuwa ce ta nuna iko aka yi gurin wanzuwar rabuwar saidai yaci ace yamanta da wannan abun amma Sam yakasa mantawa yakasa manta waccen fuskokin da fuskar da a cikin fiskokin yafi tunawa dama muryar waccen fuskar ya Allah ya furta ya rasa yadda zaiyi ya manta da waccen rayuwar ta baya da abinda yafaru garesa a waccen rayuwar.

SADIYA KHALI✍🏽

comment#
Share#
Vote#*JININMU 'DAYA*

By Sadiya Ibrahim Khali

7
Kwanci tashi ba wuya gurin Allah yau AbdulAhad kwanansa Hamsin da rasuwa anyi addu'ar Arba'in da Abba bukar ya hutar dakowa sukayi a masallaci,Rufaida da taji karar wayarta ta duba ganin maikiran yasata 'dagawa karon farko Samiha macen da bazata iya mantata a rayuwarta ba tare sukayi rayuwa mai cike da farin ciki da kaunar juna inda lokaci guda wannan rayuwar tazama tarihi ita 'din Samiha jintatake a zuciyarta fiye da tunani,Da sallama Rufaida ta 'daga wayar da Samiha ta amsa takuma kara da cewa "habawa Rufaida ace sai na kiraki zaki tunani"murmushi Rufaida tayi da ita kadai tasan fassarar abinta tace"a'a Samiha ku'din wayar ne babu na kira bama nida caji sai yau nasamu" cikin firgici Samiha tace" Rufaida meke faruwane kiyimin bayani"hawaye shar sune suka biyo kuncin Rufaida batareda tace komaiba kawai ta katse wayar tana tuno cin fuska da cin zarafin da akemata a gidan kuma bata fuskar kowa ba sai Hajiya Jamila da Ruqayya AbdulMalik da Abba basa zama basusan komaiba cajin waya ma basa bari tayi duk dakin datasa caji sai yara sunbita suna kokawar game kwanakin baya jefarmata ita sukayi ta kara tsagewa,idanko tace wani abu saitaga kamar bata kyautaba tunda 'ya'yan Hajiya Kubra da Aunty Amina ke hakan itako a yadda take daukarsu tamkar umminta Hajiya Jamila da Ruqayya ke mata suke uwa da makarbiya,Dakin Hajiya Jamila da take tunanin sawa don samun sauki to tasan ko giyar wake tasha bazata je da zunmar sa caji ba hakananma idan taje kyara ke hadasu bare kuma taje da zunmar wani abu,dukda itama dakinta akwai komai saidai matsalar dayace babu caza tata tana abuja ,tsangwama gori datake sha ga mutane biyun dukshi yafi damunta mutanan datake samun farinciki a gunsu suma hotone idan mai gidan bayannan dan Hajiya Kubra da Aunty Amina basuda hayaniya shiyasa basa shiga abinda za'ayi wata hayaniyar dasu sai daifa idan sunga abin nanema ya tuke suke uwa makarbiya
Chapter 7 · 0% Book details