Sashe 38
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A bakin kofar zaure Rufaida tayi kicibus Hajiya Jamila da take kokarin shiga ciki hartayi kokarin bangaje Rufaida Rufaida tayi saurin matsamata hanya ta kalli Hajiya Jamilar da kallon daya tayi mata taji gabanta ya fadi ganin yanayin annurin fuskarta babu shi anbaton Allah tayi kafin tayi saurin cewa
" Umma sannu da zuwa"
Hajiya Jamilar ta kalli mai mata sallamar tayi ido biyu da Rufaida da da idonta ya rufe bata san da mutum a zauren ba dan tunaninta yayi cikin gidan gaba 'daya wata irin fisga Hajiya Jamilar tayi mata zuwa cikin tsakar gidan tana cewa
"Wallahi yau sai na kashe ki,dan muddin ina raye dana bazai hada iri da kuba"
Jin maganar Hajiya Jamilar ya ankarar da Gwaggo inda a lokacin take kokarin wanke Rufaida da mari gurin Gwaggo ta karaso da niyyar kwace Rufaida Hajiya Jamilar tayi kukan kura ta angije Gwaggo tana cewa cikin 'daga murya" matsanan Munafuka angungunma ca kike yadda kika munafunci 'yan uwanki nima zaki munafunce nine,wallahi sai dai yau na kashe ta inyaso nima akashe ni dan bazan hada zuriya da wannan mazinaciyar uwarta taba ,",ta karasa maganar tana sake kwada wa Rufaida mari daga visa ni ta shake wuyan Rufaida"
Ganin haka yasa Gwaggo saka kuru ruwa tana ihu makwabta neman taimako
Lokacin yayi dai-dai da karasowar Abba Bukar kofar gidan ganin motar Hajiya Jamilar kofar gidan yasashi saurin kashe motarsa ya rufe ya isa cikin gidan harda gudunsa dan yasan,tunda yaga motar Hajiya Jamilar yasan akwai matsala
A lokacin da ya iso Gwaggo ta sake kukan kura ta nufesu tana kokarin cire hannnun Hajiya Jamilar daga wuyan Rufaida amma ta kasa Rufaidan sai zaro ido take
"Jamila wallahi idan biki saki wuyan 'yar mutane ba to wallahi a bakin aurenki"
Abba Bukar yayi maganar yana karasa shigowa ciki,da babu wanda yaji shigowarsa
Badan Hajiya Jamilar taso ba ta saketa
Ta kuma cigaba da dukanta,da alokacin makwabta sun fara shigowa jin kururuwar Gwaggon da suke,da kowacce take tsaye tana kallon ikon Allah,mai kuma Rufaidan tayi wake dukanta dan busu shaida fuskar Hajiya Jamila ba saboda ta juya bayanta
Gurin da suke Abba Bukar ya karaso ya kwace Rufaida daga hannun Hajiya Jamila da Harira da har da ita a masu shigowar tayi kokarin karasowa gurin Rufaida ta janyeta gefe
shiko Abba Bukar Hajiya Jamilar ya nufa da zafin zuciya ya kwashe fuskar da wani gigitaccen mari yayi ball da ita,ya fara dukanta yana cewa
"Ke dabba ce 'yar mutanan zaki kashe"
ganin yana kokarin cigaba da dukanta yasa Gwaggo rikesa tana basa baki
"Kan wannan 'diyar mazinaciyar ka dokeni ko,wadda danginta suka juya mata baya,to wallahi indai kukai kokarin aura mata 'dana saina kashe ta inyaso nima a kasheni"
"Da ubanki tayi zinar ko,kuma dangin ubanki ne suka juya mata bayan ko,kuma wallahi aure sai anyi shi ,kuma karki sake ki koma min gida ,na tsaneki da zama dake ,fitinanniya babu abinda auranki ya tsinanamin face asara"Abba Bukar yayi maganar cikin zafin zuciya
" Saina koma ,koda saki na zakayi saina zauna nayi zaman 'ya'yana"
Cewar Hajiya Jamila tayi maganar tana kokarin tashi tsaye
"Abba Bukar yace
" Bismillah ki koma wallahi da sai kin yi danasanin da tunda uwarki ta kawoki duniya baki taba yi ba"
Rufaida Hajiya Jamila ta nuna da Harira ke bata ruwa tace
"Kan wannan,Yarinyar da ko acikin dabbobi tafi su iya dabbaci saboda 'yar mungada ce, ka wulakantani gaban jama'a ko,bismillah Ku daura auran wallahi saikunyi danasani fiye da tunaninku" tayi maganar tana dukawa ta dauki makullin motarta ta soma tafiya
"Duk barazanarki ba zata hanani aurawa Wahid Rufaida koda ace vayasonta idan harni inasan ya aureta sai ya aureta,saboda bake kadai keda iko da 'danba" cewar Abba Bukar
Kofa Hajiya Jamila tayi ta fice
Sai bayan ta fita Abba Bukar ya jiyo ya bawa Gwaggo hakuri shima ya fice yana sanar dasu zai dawo gidan idan ya tashi daga gurin aiki
Makwabtanma hakuri suka bawa su Gwaggo suka firfito suna jinjina lamarin masu tsinewa Hajiya Jamila nayi masu zaginta nayi,da kwashe mata albarka,dama mutane jiran suke ayi,dan danki zai auri 'yar uwarsa saitazo tana hauka maiye laifin Rufaidan yarinya mai hankali.*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil❤️
40.
Hajiya Jamila da tunda ta fito gidan Gwaggo take kuka a cikin motarta bawai kukan danasani ba akan abinda tayi kokarin aikatawa da kuma furucin mijinta akanta ba illa tunaninta 'daya ina zata da wannan abin.kunyar ace dan ta zaiyi aure bata sani ba sai ana saura kwana uku kuma aure ma ya rasa wadda zai jajubo sai 'yar Hauwa'u da kowa yasan kiyayyar da take ma Hauwa'un,ganin tunanin ba shine mafita ba yasata yiwa motarta key tayi gidan Gwaggo Lariya
Abba Bukar yana fitowa gidan yatarar da kurar motarta kai ya girgiza ya shiga motarsa da tunanin abinda ya yanke aransa kai tsaye gidan wan mahaifinsa ya wuce Baba Ashiru,Abinda ya faru kaf ya fadamasa da kuma hukuncin da ya yanke a daura auren Wahid da Rufaida saboda baiga alamun Hajiya Jamila zata hakura ayi auren ba
Baba Ashiru dubesa
"Gaskiya Bukar kayi tunani me kyau,abinda ya kamata ayi kenan,tunda ita Jamila har yau bazata yi hankali ba kamar wadda ake zugawa"
"Wallahi Baba babu wata zuga danni sai yanzu nake danasanin aurenta ma....
Baba Ashiru yayi saurin dakatar da Abba Bukar maganar da yake yace
"Kul Bukar koba komai ai uwar 'ya'yankace ba kuda wata makankara sai dai muyita yi mata addu'a"
Abba Bukar ya mike ya na cewa
"Haka ne Baba ni bari zan koma wajen aiki dan Allah ka kira Baba Amadu kasanar masa dan Gwaggo da mukai waya tace gaban kaina na fara yanzu tun busu mutu ba"
Baba Ashiru yace
"Ina ruwan Zainabu ,to zan sanar masa da dukkan abinda ya faru zan fadamasa hukuncin da ka yanke amma bazan ce kai yanke hukuncin ba karmu sake yin laifi"
Abba Bukar ya fito daga dakin Baba Ashirun yana dariya
*******
Gwaggo ce tayi kokarin karaso wa inda Rufaida take ganin kowa ya watse daga gidan da ga Rufaida sai Harira da Gwaggon dafata tayi ta soma maganar ba tare da ta damu da Harira dake gurin ba dan abu ne akayi sa ba a boye ba
"Haba Rufaida kukan ya isa haka kinemi sakayya gurin Allah kawai"
Rufaida ta dan goge hawayenta ta dubi Gwaggo tace
"Gwaggo nidai dan Allah a fasa auren nan"
Gwaggo ta zaro ido tace
"Baki da hankali Rufaida auren za'a fasa saboda wannan shashashar yarinyar tazo tayi haukanta,kenan a fasa taci galaba akanmu,to koda Wahid baya sanki sai anyi auren nan dan akuntata mata"
Kuka ta kuma rushewa da shi tare da cewa
"Ni dai dan Allah Gwaggo a fasa ,kina gani fa kashe ni Umma taso yi,ga maganganun da take fada akan Umminmu,Gwaggo dan Allah mai muka yi mata"
"Kinga bafa za'a fasa ba, ita bata isa ta kashe ki ba haukan banza take,maganganu kuma taje tayi tayi ita ce mara aikin yi,kuma sharrin ta saidai ya bita"
Da haka dai Gwaggo ta lalla'beta ta daina kukan suka koma inda suke aikinsu suka cigaba dayi
***
Sallamarsu Ummi Hauwa'u ta katse firarrakin da suke jefi jefi suna aiyukansu da gudu Rufaida ta karasa gunsu ta rungume Aunty Samina dukda ba wani kuzari jikinta
Gwaggo da Harira suka amsa musu sallamar
Ciki suka karaso da fara'arsu suka zauna a babbar tabarmar da aka shinfida
Saida suka gaggaisa ,Aunty Samira ta dubi Rufaida tace
"Yanaga ba kuzari jikinki kamar kinyi kuka ga idonki duk ya kumbura"
Gwaggo tayi saurin cewa
"A'a ba wani kuka sauro ne ya ciccijeta jiya bata sa net ba"
Aunty samira shiru tayi vadan ta yarda ba
Rufaida ta ja hannun su Kalim da Khalil yaransu Aunty Samina dakinsu dan surutun ma batasan shi ko daya
Ummi Hauwa'u ta bita da kallo aranta tana tunanin tabbas da abinda ke damun Rufaida zuwa dare zata sameta suyi magana
Su Rumaisa ne suke shishshigo da kayan da suka taho dasu da sauran yaran Abdul kuwa da shiya kawosu baima shigo gidanba ya tafi gidan Gwaggo Hajiya gurin abokansa
A'a marhavin lale da kanawa,Malam yake maganar da murmushi fuskarsa da shigowarsa gidan kenan ya cikaro dasu Aunty Samina suna aikin doghnut bayan sun huta sunci abinci
Da murmushi a kan fuskarsu suka gaishesa ya amsa yana cewa ina su Gwaggon suka ce masa suna daki
Dakin ya nufa ya tarar dasu a zazzaune suna nunawa Gwaggo kayayyankin da sukai wa Rufaida
Gaishe da Malam sukayi ya amsa yana musu sannu da zuwa
Zuwa can ya nisa yace
"Yau ne daurin auren fa yanzu Ashiru yake sanarmin ina kokarin shigowa nan gidan ya kirani a waya,shine nazo nasanar muku zance na shirya yanzu ,bayan daura auren zasu kawo lefe" da haka ya mike ya bar dakin dan baya san jin wani zancen su yanzu haka