← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 57

Sashe 19

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bazan amsa ba" ta fa'da tana cire hijabin kanta gami da zama gefenta tun 'dazu na ke tamiki sallama kika'ki amsawa," tace"yaya ban jiki ba," Dama baza ki jiba ai waya ta dauke miki hankali ta fada fa'da tana mi'kewa

"Ummi sannu da aiki"Rufaida ta ambata, Datake 'ko'karin shigewa cikin kitchen 'din, Ummi ce tajuyo tareda cewa badai har kun dawo ba?

"Eh ummi su momy 'din duk basa gida"

Murmushi ummi tayi kafin tace wani abu

Rafi'a tashigo kitchen 'din ummi ta mi'kawa wayar ta tana cewa "ummi ga wayarki momy tana kira.

Sai da suka kammala wayar, ummi ta dubi Rufaida "tana cewa momy tace zakuje 'kunshi, Samir zai zo 'daukanki"gobe da safe

_________________________
Abdurra'uf yaushe zaka shirya ne? yanzu fa tara ta yi, Bana son tafiya ace baza'a tsireta da wuri ba", Momy ta fa'dawa, Ra'uf da yake kokarin zura takalmi ya fito daga dakinsa yana cewa momy " yanzu zan fito muje gidansu yarinyar nida Ahmad dana dawo sai na zo natafi", To shikkenan inji momy, Naga Ahmad 'din yafita kasamesa Ku wuce, Da "to "ya amsa ya fice

"Amarya samiha bata laifi kota kashe 'Dan masu gida", Ra'uf kewa kyakkyawar budurwar kirari dariya kawai tayi tasamu kujera ta zauna dake cikin falon tana fa'din "yaya Ra'uf ai sai dai idan banyi ba" ta 'karasa maganar tana mai gaishesu

"Yanzu yaron nan har goma tayi bazai taho su tafi ba yafison sai rana tayi ace za' a tafi guri vaza'a tashi tafiya da wuri ba",dady ne keta sababin fa'dan da ya shigo falon yanzu, momy tace "nima sai da na masa maganar ko da zasu fita", waya dady ya ciro a aljihunsa ya dan na yasa a kunne

Jin karar wayar tasa ne yasashi 'dauka cikin gaggawa "dady ganinan zuwa" inji Ra'uf ya katse wayan, yana mai kallon Ahmad yace "dady yana kira na nazo mu tafi",zan biya gidan Ummi daganan zan kira Mukhtar yazo ya daukeni ,"Ga ku'din kunshi nan "ya zaro ku'di masu yawa ya ajiyewa Rufaida a centre table 'din falon godiya Samiha tayi da addu'ar Allah yakaisu lafiya Ahmad ya fito rakasa

Dady ne ya kalli momy bayan ya cire wayar daga kunnensa, yana cewa "yanzu da banyi masa waya ba bai da niyyar tahowa, Amma yacemin yanzu gashi nan zuwa".

Ahmad da yaraka Ra'uf gate din gidan yace dashi"Sai munyi waya idan kun isa kaje kasha fa'dan Hajiya, Ra'uf yace "ni so nake ma naje naji fa'dan da zan sha gurin Hajiyar da kake fada".

"Gaskiya Rufaida kin 'batamin lokaci sosai, Gashi kin barni da Abdur- Rafi sai fa'da ya kemin kamar wanda nama laifi", matashin saurayin dake tu'ka mota ya anbata,

"Haba yaya Samir kasan ba laifi na bane, Kasan yau Abbi zai dawo gida shine dalilin da yasa sai da na taya ummi aiki ta 'karasa maganar dacewa fa'danka da yaya Abdur-Rafi babu mai shiga ta fa'd tana murmushi"

"Au haka ma za kice to nagode " samir ya fa'da yana cigaba da tu'kinsa

Motar Ra'uf da tafito daga layin gidan nasu Samir ya 'dagawa Mukhtar hannu.

Ibrahim Khalil Family🖊️🖊️️*🔗JININMU DAYA*🔗
By Sadiya Ibrahim Khalil
Hikima writers assoc....
19
Jin sallamar tasu Rufaida ne yasa su Samima da yaran su Aunty Samira biyu dake cikin falon rugowa gurin Rufaida suka rungumeta, "oyoyo yaya Rufaida", Momy dake daya daga kujerun falon tace, samima kar fa yarda yayar taku,ku kuma Auntynku"

Hannunsu takama ta shiga cikin falon da murmushi fuskarta ta mikamusu Biscuit guda uku suka amsa suna godiya suka shige cikin gidan

Momy ta kalli Rufaida tana cewa "maraba da zuwa Umminku da nasake kiranta harda cewa da wuri zaki zo"

Momyn tace "sai yanzu zaki taho kunshin rana tafara yi da bansa Samir ya 'dauko ki ba zaki zo ba "

Murmushi Rufaida tayi tace" haba Momy zanzo Yaya Samir ne baizo da wuri ba dan har nace da baizo ba a napep zantaho ma ,kuma na taya Ummi girki yau Abba zai dawo gida"tace"Bansaniba da nabari sai yammar sai a daukoki tunda naji suna sai yamma karfe hudu za'aje kunshin saboda yanzu mai gyaran jiki tazo,kinsan halin Yayannaku shiriritarsa ya tsaya yi "murmushi Rufaida tayi ta gaida Momy Momyn tace"Samihan tana falon baki Ahmad yazo", kije Ku gaisa

"Lallai Rufaida dama kina nan" Ahmad yace bayan ta shigo suna gaisawa,

"A'a yaya Ahmad bama ha'duwa ne"

Samiha, Ahmad ya kalla "yace haka ne"?

Kai ta 'daga masa Samihan dan itama fushi take da Rufaida take ranar Laraba da sukayi bikinsu guduwa tayi tabi su ABDUL-RAFI gida

Ahmad yace " kin fitar da ita"

Sun 'dan ta'ba hira kafin , Rufaida ta fice daga falon bakin ta koma ciki dakinsu Rufaida ta shiga tasamu Yaya Saudat a ciki da ake mata gyaran jikin amare da ita suka cigaba da hirarsu sai mai gyara da take sa baki a wata hirar ,Shigowar Samiha yasa mai gyara fara yiwa Samihan ta aje musu rafar kudin da Ra'uf ya bata tace"Yaya Saudat gashinan ayi lissafin abinda ba'asiya ba ko sunyi kadan sai aba Driver ko Yaya Musa ya karo"Saudat takalli kudin tace"yanzu duk Ahmad ne yabada wa'dannan kuda'den masu yawa ,ke Samiha ba kya tausayin Ahmad ko "tace" A'a yayan sane ya bayar ,amma shima idan ya bayar ai dolene tunda shi ya tattago yin auren,komai sai kice a riqa tausayawa haka ma kike cewa Yaya Mujahid kenan,bakisan maza ba anuna ana tausayinsuba kusan duk basu da halarci"Murmushi Saudat tayi kawai tace"ke matsalarki kenan a fadamiki goma ki fadi dubu"Rufaida tace"wallahi Yaya Saudat haka take"Samiha ta harari Rufaida tace to aiku gaskiya ne bakwaso a fada"abunda yakamata a siyo ba asiyo ba suka fara rubutawa da yamma suka tafi gurin kunshi da suke saran tafiya Sakoto da asuba saboda daurin auren da za'ayi a can ranar Lahadi da zasuje ana i gobe biki da ranar Laraba sukayi hidimar bikinsu da kawayensu abokan karatunsu maza da mata da angwayen babu wanda yaje dan sai bayan bikin da sai ankai amaren angwayen zasu hada Dinner kowa da shi da Family dinsa banda ma ahalin matan nasu sai tsinta tsinta Saudat cema za'ayi dana ta 'yan uwan kasancewar ita auren zumunci auren gida za'ayi musu ita da Mujahid din nata

ABDURRA'UF ya 'dan duba gefen titi da suke tafiya ganin mota a tsaye gefen hanya yace"
Mukhtar dan duba Kaga kamar mota na gani a tsaye?ya kamata ka fita kaji lafiya,ni a gajiye nake na dade rabona da tafiya a mota mai nisa"Murmushi Mukhtar yayi ya maida dubensa wajen da Ra'uf yanzu na masa yace "eh nima naganta, Sai dai kuma kana ganin ba matsala Idan mukayi haka, Duba da yadda rayuwar ta zama a yanzu"

"Eh babu komai insha Allah sai Alkhairi tunda niyyar taimako mukayi,Allah zai dubi zuciyarmu"

Abba Aliyu wato mahaifin Rufaida ne a motar yana kokarin kiran wayarsu Abdul-Ahad da Abba Bukar ya sanarmusu fashewar da tayar motarsa tayi yanzu ko za'asamu mai gyara daga Zaria suzo a tafi da motar da yake ta kiran wayar baya samu Network ya hana ta shiga ,gefensa da ABDUR-RASHID ne da ya biyo ta Kaduna ya dauko ABDUL-RASHID daga gidan ZAINAB Inda mukhtar ya karasa da sallama a bakin sa , Da murmushi ya amsa masa sai da suka gaisa ya kuma mi'kawa ABDUL-RASHID hannu sukayi musabiha, inda mukhtar ke tanbayar ABDUL-RASHID sunansa,ABDUL-RASHID ke shaidamasa sunansa Abdul-Rashid.

Kafin mukhtar yace ma Abba Aliyu "yalla'bai mai ke faruwa ne naga kun tsaya a gefen titi ko wani kuke jira

yace masa" a'a ko 'daya tayar mota tace ta fashe muna baro cikin garin kaduna yanzu gashi banida wanda na sani mai gyara a cikin Kadunan,kuma banida safayar taya nakira Number din wanda nasani taki shiga "

Mukhtar ne yace"Allah ya kara kiyayewa bara nazo"
"ya amsa da amin, to nagode"

"Mai ya faru ne mukhtar" inji Ra'uf

Mukhtar yace"tayarsu suce ta fashe"

"Subhanallah ka kira mai gyara bai kamata a barsu a tafi ba, ga abinci ka mikamusu" Abdur-Ra'uf ya fa'di haka tare da mi'kawa Mukhtar abincin dake leda mai 'dan girma

Sai da mai gyaran yazo yayi gyaran suka 'karasa kaduna inda Abba ALIYU ke ta Sanya Albarka a garesu tare da addu'oi ma banbanta

"Maraba da zuwa mutanan kasar waje" Hajiya take fa'da da murmushi da ya nuna har a saman fuskarta

Mama ce da Yakumbo suka 'karaso falon suna nuna murnar ganinsa

Inda shi ko Ra'uf yayi 'dai 'dai a kujerar falon yana maida gajiya dan agajiye yake tibis yasha wahalar tafiyar

Yakumbo ta ce "wato Hannatu ta ri'ke ka sai yau kataho ko?" ta fa'da tare da 'kara sakin murmushi fuskarta

Hajiya tayi saurin karfe zancen da cewa "ahaf ai nasan za'a rina taya zan yarda da maganar ki suwaiba ace har yaron nan yayi sati biyu kice baije gurin hansatu ba, Ai nasan da cewa nice bakwa 'kaunata"

Mama ce mai cewa haba "maman jabiru ai kinsan da yaje gurin hafsatu ba ta yadda za'ayi ki'ki sani tun jiya da su Lamido suka fara isowa"

"Suwaiba babu ruwanki tun da kinfi kowa sanin abunda yaran nan nawa suke yi min duk akan 'ya'yen Hassatu yanzu zaki zomin da wata gulma"

Kafin ta 'kara cewa wani abu gaba 'dayansu suka bar falon

Suwaiba ta dubi Yakumbo tana bata ha'kuri "Hansatu kiya hakuri kema kinsan halin yayarki muyi ta yimata addu'a Allah ya shiryeta"

"Insha Allah ,amma Halayyar Yaya Hanne, Maman Hamidu badai zance komaiba tunda kince Allah amma abu tunda jajayen sahu ake har zuwa yanzu bata canza ba" inji Yakumbo wadda ita gani take abinda 'ya'yen nata ke ma yayarta ta basa yimata sai dai ita bata gani, Kullum gani take ita ake yiwa batun yanzu ba tuntuni yayarta ta ke ganin haka , kuma ita ina taga Ra'uf 'din da idanunta banda zuwan da tayi ranar da zaizo 'kasar da guntun hawaye ta 'karasa shigewa wani 'daki

Shiko Ra'uf kai tsaye 'dakinsa ya shige yanajin shigowar wasu mata falon da suka tarar da banbamin da Hajiyar keyi da cewa "Ai ni dai na kwari kaina da na ha'da zuriya da Hansatu duk an mallakemin 'ya'ya ba jabirun ba ba usman 'din ba Zuga Hajiyar suka shiga yi 'daya a ciki nacewa "Hajiya ai tunda kika bari 'ya'yanki suka auri 'ya'yan Hansatu ai sai dai kiyi ta addu'a
Dan kuwa----"
Chapter 19 · 0% Book details