← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 57

Sashe 26

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jin karar wayar Ummin nasu yasa su gaba dayansu maida dubensu ga wayar da take kusada Rufaida ganin me kiran Yaya Abdul-Ahad be yasata rigasu dauka Yaya Abdul ya dubeta yace mata
Wai waye ne mai kiran"
Tace masa
"Yaya Ahad ne"
Ko kallan wayar bai sake yi ba ya cigaba da abinda take
Da haka ta daga wayar da Sallamarta shima daya bangaren Ahad jin muryar Rufaida a wayar yasashi amsamata sallamar da murmushi kamar tana ganinsa ta dora da gaishesa ya amsa ya dora da cewa Rufaida 'yan Candy kunyi Candy bamuzo walima ba bai karasa maganar ba Rufaida taji muryar Hajiya Jamila har kunnenta kasancewar yana zaune cikin 'yan uwansa a babban falo suna fira kamar ko yaushe
" Cikin fada Hajiya Jamila tace masa
"Ahad tanbayar Candy zakayi ko cewa tabawa Hauwa'u wayar kayimata maganar zuwanku gobe, kar a sake kwatanta waccen zuwan fa"
Ahad aje wayar yayi saurin yi Wanda atunaninsa ya katse kiran ya aje yace"Umma ki bari mana anajinki fa"
Hajiya Jamila tace "ni rufemin baki sakarai ajini mana karyanayi inba tsabar iskanci tasan da zuwanku tasakai tabar gidan itada mijinta,ni mutane naban mamaki da sun samu wata dama saisu fara manta Alkhairi duk abinda mahaifinku yayi musu sun manta shi"
Murmushi Rufaida tayi mai ciwo ta kuma kasa cire wayar a kunnents ita ta rasa menene laifinsu me suka aikatawa dangin su suke musu horon aibanta Umminsu tuni batun yau ba bayan itama mahaifiyar tasu 'yar dangi ce ita iya saninta Gwaggo kakarsu data haifi Ummnsu zaune take da kowa lafiya hakama Ummintasu amma haryau takasa fahimtar maiyasa ake cin fuskarsu ake aibatasu ake waresu kowa musamman cin fuskar da zarafin da akewa mahaifiyarsu dasu kansu Hajiya Jamila tafi yin hakan sai a lokacin tayi danasanin 'daga wayar
Jin muryar Ahad ta cikin wayar yadawo da ita daga tunaninta
"Umma sau nawa zan fadamiki fitarce ta dole har yasa muka je gidan basanan,kuma ai sun dawo kafin mutaho"
"Dallah rufemin baki mai kake nufi karesu zakayi took ubanka baka isa ka karesu gurinsa ba akan wannan maganar bare kuma ni da bana kalar dangi ka...." bata karasa jin maganarba ta katse wayar ta ajeta a gefe ta zuba ta gumi hannu biyu ta kuma kife kanta jikin hannuwan nata ita gani take babu wanda yakaisu matsala da 'yan uwansu a ranta tausayin mahaifiyar ta takeji ita kadai ce gurin iyayenta ita kadai tasa ba rayuwa batada abokan shawara sai iyayenta batada yayye ko kanne 'yan uwa kaikace mujiya CE a cikinsu idan ta shiga ko ina Hajiya Jamila ta zauna bata take cikin yan uwa suma da take basanta suke ba saisu yarda tarasa mai Ummintasu ta tserewa Hajiya Jamila gashi tunda mahaifinta ya daina jiran abashi ya daina ci da sha da sutura karkashin wani shikenan tsana da tsangwama garesu ta karu kukane ya kwacewa Rufaida
Ummi Hauwa'u data karaso falon ta karasa gurin da Rufaidan ke zaune ta dafata
"Ke Rufaida lafiya maike damunki ne"
Gaba daya 'yan uwanta suka tsaida abinda suke suka dawo gareta
Abdul yace
"Ummi daina wahalar da kanki gurin tanbayarta Yaya Ahad ne yakira waya to kila mamarsu yabawa wayar ta fadawa Rufaidan maganganu marasa dadi shine take kukan,har yau takasa dauriya akan abinda banga ranar daina shi ba kishin facala matar wa da kani to ita na mamar Yaya Ahad mai zafi ne Gwaggo tasha fadamana haka"
Murmushi Ummi Hauwa'u ta ta dago fuskarta tana goge mata hawaye
"Haba Rufaida komai fa lokaci ne wataran zai wuce gaba 'daya yanzu ina waccen rayuwartamu ta baya take da mukayi ba gata ta zama labari ba"
Gyada kai Rufaida tayi ta mike tabar falon Ummi Hauwa'u da ido tabi Rufaida ta dau wayar tabi kiran Ahad
Ahad dayake zaune kan gadonsa ya zuba tagumi yana tunanin halayyar mahaifiyarsa da baisan randa zata sauya ba yanzu yasamu ya baro mata falon ganin batada niyyar daina maganar karar wayarsa da yaji ya maida kallonsa ga wayar
Ringing biyu ana uku ya dauka cikin zullumi maizai faru a idan ya daga dan ya fahimci Rufaida taji duk irin cin mutuncin da mahaifiyarsu ta musu dukda yasan su wacece Ummi Hauwa'u ba tada maida kai ga al'amuran mutane kome zaka mata bata ko nunawa a fuskama bare kaji a furucinta suma kuma 'ya'yan nata irin halin nata gare su yadda ya zata ko hakan yaji gun Ummi Hauwa'u yaji tace
"Assalamu Alaikum Babban Yaya"
Murmushi yayi a nashi bangaren ya amsa Sallamarta ya gaisheta cikin girmamawa
Sun dan taba hira daga bisani tabawa yaran waya duk suka gaisa
Ahad bai gigin cewa Ummi ina Rufaida ba ganin cewa dama sun gaisa da haka ya katse wayar bayan Ummi Hauwa'u ta amsa wayar ya sanarmata zuwansa a washe garin da haka sukayi sallama tana cewa ya gaida mutan gidan nasu.

SADIYA KHALIL🖊️*JININMU 'DAYA*
*NA SADIYA IBRAHIM KHALIL*

*SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI 27*

*MASU GANIN BANA TYPING KUYI HAKURI KUNSAN TYPING AKWAI CIN RAI WANI SA'ILIN MUSAMMAN KUMA TYPING NA LITTAFI MASOYA LITTAFIN JININMU 'DAYA RUFAIDA NAGAIDAKU ITADA DANTA YASIR DAFATAN BAKU MANTA SHIBA*😊🤔
*******
Yaya Abdul Abdul-Rashid ya kalla da suke Dining suna karin safe su duka yace mass"Yaya ban haka wani kyakkyawan labari ba munje wani boutique nida su Uncle Haris da Aunty naga wani kamarkai"
Abdul yace"nine ma mantawa kayi"yayi maganar yana hararar Abdul-Rashid
"Allah Yaya nima nida Rafi'a munga wani a mota a flyover kamar kai har Rafi'a ta masa magana"Rufaida tayi maganar da fara'arta
"Wallahi kuwa nima Yaya Rufaida har magana mukayi" Abdul-Rashid ya karasa maganar yana tari maganar da yake yanacin abinci ya kawo masa tarin
Kallonsu Abba Aliyu yayi ya soma magana
"Gashinan kaika shaqe ,bakwa tashi yin magana sai kuna cin abinci,duk fadan da ake muku bakwaji"
"Hakuri suka basa suka cigaba da cin abincinsu.
Ummi Hauwa'u kuwa ko magana batayi ba saboda sun bata haushi
Karar wayar Abba Aliyu yasa Abba Aliyu daukarta da take saman Dining ya duba mai kiran da murmushi ya dauki kiran da Alhaji Hashim ne mai kiran sai da suke gama wayar Abba Aliyu ya dubi Ummi Hauwa'u yace
" Alhaji Hashim ne maganar yaron nan saurayin Rufaida ya kira yanzu yana kofar gida
Abdul ne ya cire hannunsa a abincin ya kalli agogon hannunsa 11 saura Abba Aliyu ya kalli Abdul "din ya soma magana
" yanaga ka cire hannunka a abinci badai harka koshi ba"
Yatsina fuska Abdul yayi
"Abba na koshi ,lokacin cin abincina ya wuce indai Rufaida ce zatayi batason gamawa da wuri"
Ummi Hauwa'u tayi murmushi kana tace
"To za'adawo da duty hardakai"
"Haba Ummi 23 shekaru nake dasuba yanzu ai na girmi girki da sauran aikin gida sai kace wani dan daudu"
"nikaga tashi tunda ka gama kaje ka shigo da bakin nan kakaisu falon baki ke kuma Rufaida kije ki shirya Hauwa ki hadamusu abin tabawa a baki"Abba Aliyu yayi maganar yana mikewa yayi Upstairs
Abdul ya fito falon yin abinda Abbansu ya umarceshi.
****
Ra'uf ya dubi Mukhtar da suke tsaye jikin motarsu a kofar gidan su Rufaida
" Mukhtar kodai Ba kofar gidansu Rufaida tace kasauketa ba jiya daka kawota gida,naga nakira Ahmad run dazu kuma inada yakinin ya kira"
"A'a nan ne mujiradai mugani" Mukhtar yayi maganar yana sake kallon kofar gate din

Abdul da yakarasa fitowa daga gate din gidan Mukhtar da Ra'uf suka maida kallonsa garesa Ra'uf da kallo daya yayiwa Abdul yaga kamar da yake da Rufaida ganin yana kokarin wucesu yasa Mukhtar saurin yi masa Sallama
"Assalamu Alaikum Bawan Allah"
Abdul ya juyo da tunda ya fito ya hangosu yadai wuce ne saboda shi kwata kwata busy kwantamasa rai ba dukda yadda ya gansu tsaye jikin mota mai tsada karasowa yayi inda suke da idonsa kyar ya sauka ga Ra'uf da gabansa yaji ya fadi daganin Ra'uf din addu'a yayi ya daure yace musu
"Wa'alaikumus salam"
Hannu Mukhtar ya mika ma Abdul shima ya mika masa cikin murmushin yake sukayi musabihar Ra"uf shima cikin murmushi ya mika masa hannun suka gaisa
"Kune bakin da Abba yace na shugo daku ko"
Abdul yayi maganar
"Eh mune"
Cewar Mukhtar
"OK to bari na bude muku gate din ku shigo daga cikin"
Abdul yayi maganar yana kokarin barin wajen
Suma motar suka shiga Mukhtar ya tayar suka dannan hancin motarsu cikin gidan da Abdul ya wangame musu gate din gidan ya birge Ra'uf sosai duk da bawani mai girma bane amma ginin gidan anyi sa cikin tsari maganar Abdul ta katsewa Ra'uf tunaninsa inda yace musu
"Bissimillah ku karaso mana"
Bayansa sukabi ya karasar dasu falon baki suka shiga falon
"Bissimillah Ku zauna,bari nakarasa ciki nakira muku ita"
Abdul yayi maganar yana kokarin barin falon
Zama sukayi suna mai ce masa "to"
Chapter 26 · 0% Book details